← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 139

Sashe 92

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Jirgin da zai sauka birnin madina, ran daren Laraba muka shigo,
Salim ne yazo taron mu shida wasu mutum biyu, cikin farin ciki da kwanciyar hankali muka sauko
Kallo guda zakaiwa sheriff kasan cewa ya samu lafiya fiya da ,da ya wani murje yadan kara kaurin jiki kadan gawa wani haske da yakara,
Muna hada ido da salim naga yai min wani kallon mamaki, yana murmushi,
Mungama clearing na komi ,muka fito cikin air port din ,motoci ukune muka jera zuwa gida,
Katuwar pickup din dake bayan mu an lodo mata kaya saida ta shake fam,
Muna tafe salim nata zolaya na yanata mamakin irin kyaun da nakara cikin dan lokaci guda,
Ina jin duk abinda yake fadin saidai ban iya ansa mai alokacin saboda duk a gajiye nake
Ga wani irin barci da nake duk ya kara saukar min da kasala ajikina,
Maimakon mu tafi gidan mu inda muke sai naga mun yi parking a wani kyakyawan gida mai kyau da kuma girma sosai,
Sai alokacin Sheriff dake gefe na zaune yadan waigo yana kallona
Ya dan duko kadan daidai saitin kunne na yace min welcome to your new house, fatima,
Da sauri na mayar da dibana akan gida cike da tunane iri,iri,
Dan kallon shi nayi da mamaki sai kawai yadan daga min kai kadan alamar eh,
Cak naji nunfashi na kamar ya tsaya min saboda mamakin, jin wai wanan gidan gidan da zan zauna ne,,
A,zuciyana nace ni fadima diyar inna yar kulu ce zata shiga cikin wanan katafaren gidan mai kyau,
Ginan gidan yakai gina a gaskiya kowa yasan yadda gidajen saudiya suke da kyau da tsari kamar ba hannu yai aikin ba,,
A hankali na fito motar sheriff yafito inda nake a ya dan rika min hannu cikin kulawa da so da kauna,
Mukashiga cikin gidan gami da sallaman mu,
Kallon mamaki kawai nake bin gidan da shi, saboda irin tsaruwar da gidan yayi,
Motsi da naji alamar akwai mutum a gidan ya sani daga kai da sauri nakai kallona ta gefen da naji motsin,
Don in ga ko waye, hakan yai dai da lokacin da mama Umar ke kokarin bude falon gidan don mu shiga,
Mukayi ido biyu da sauri na ja hannu daga jikin sheriff na nufe ta da murna na,
Muka rungumay juna cikin murna da son junan mu,
Kafin in mata wani magana saiga salimat rugumay da As,mau tana muna lalai mar ha bbin,
Bansan lokacin da na sake maman Umar ba na nufe ta, na rugumay su,
Gyaran muryan da sheriff yayi ne yasa muka dan waiga ya tsaye inda na barshi hannu shi a cikin aljihun shi
Yana muna kallon cikin nuna alamar in bi a hankali pls,
Sukuma su Salimat cak suka tsaya gaba dayan su suna min wani kallon cikin mamaki,.
Murmushi na sake masu, gami da karasa ga kujerun da ke falon nadan zauna,
Ganin kallon yai yawa yasa na dan kalli kaina ina mamakin ko may sukaga na canza ajikina suke min wanan kallon,
Cikin natsuwa na dan kalle su nace anty Salimat, wai may nayi ne kuke min wanan kallon haka,
Kafin su bani ansa Amal ta fado falin da kusan gudu,gudu,sauri,sauri,
Tana zuwa ta fada min ta rungumoni ajikin ta, muka dan kankame junan mu cikin murna da an nashuwa da jin dadi,
Sai a lokacin naga UMMI tsaye, a bayan Amal, tana muna murmushi,
Tana fadin, a a tafiyan cikin, dare haka, aiko saidai jirgi kam,
Tsam,tsam na isa gareta saboda kunyar ta da nake ji na dan rugumay ta,
Haka aka hau murna da farin cikin dawo war mu lafiya,
Ganin da Ummi tai min na a gajiye nake yasa ta cewa ya kamata mudan huta kafin a kira sallah,
Kowa yace gaskiya kam,
Wata sabuwa wani kato bedroom mai dauke kayan alatu iri, iri Amal ta kai ni,
Mamaki duk ya cika ni jin cewa wai shine daki na,
Cikin mamaki da kuma nuna hankali nake karewa dakin kallo,
Fitar Amal ya bani damar cire kayan da ke a jikina a, hankali don duk a gajiye nake a lokacin,
Sheriff ya shigo dakin a lokacin shima a gajiyen yake saboda dan bata lokacin da jirgin mu yayi a Dubai kafin ya taso,
Ta bayana yadan zo yana kokarin tayani cire rigar,
Saida yaga ya cire saura yar breezeir kawai da dan bujen ciki yasa ya dan kyale ni, rigar barcin da nagani a saman gado nadauka, na sa ajikina,
Sai a lokacin na fahinci cewa ashe wai daki guda zamu zauna da ni da sheriff ,
Tirka shi, ga ummi ga su salim da Amal zan zauna da shi daki guda
Gaskiya da sake bazan iya ba sam
Yagane mai nake nufi sarai, saidai bai nuna min yagane ba, wanka yaje yayi yana fitowa ina zaune bakin gado har yanzu sai ce mun yayi bangaji ba ke nan tun da ban kwanta ba ko,
Nadai san cewa bazan yi wanka ba a cikin daren nan ba, ko,
Saida na dan bata rai nace, ni gaskiya dakin Amal zan koma,
Kafin in wani maga sai kawai naji ya kwantar dani ta baya a hankali,
Bada son raina ba dole na hakkura hakana na kwanta tare da shi daki daya,
Duk da gajiyan da muka kwaso hakan bai hana mu farkawa da wiri ba don yin sallah a suba ,
Sai dai ina idar,wa na kara kwantawa kuma ,sai wani barci mai nauyi yakara daukana,
Yuwa kawai ya sani farkawa, da ga barcin,
Wanka nayi nafito cikin shigar wata doguwar riga irin ta matan Brazil,
Rigar light blue ne, har kasa take saidai hannuwan ta shara shara ne haka bubude, cotton ne sosai sai wani sulbi da yauki takeyi, nasa yar gyalenta na daure kaina,
Saida naci abinci so sai na koshi a lokacin ne, nake tambayar anty falmata,,
Amal ke sheda min cewa ta koma gida tun bayan wucewar mu da kwana uku,
Gaskiya banji dadi da ta wuce bani a gari ba don,
Salimat da ke gefe take ce min fadima waiko kinga yadda kikawani kara girma ga fari dakikayi,
Kinyi wani kyau sai kace irin matan nan da muke gani a TV ko muji rabarin su,
Murshi kawai nai mata nace aike dama kullun haka kike cewa idan kin kwana biyu baki gan ni ba,
Tace gaskiya wanan daban yake, ba kamar na kullunba Allah sai kace an maki wani famfon girma,
Duk muka dara gaba dayan mu dake a cikin falon
Chapter 92 · 0% Book details