← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 139

Sashe 35

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Barcin da baifi awa biyu ba da,dan wani kai,,,, nayi, nafarka,
Zubur na mike,daga barcin, inda naji marana yai min karfi kamar na hade dutse,,
Ko kari nayi natashi,Wanka nashiga nayi,
nafito bakin mirror naje nadan dubi kaina naga nawani ramay kamar wace tayi wani dogon jinya
Sallah na fara gabatar wa ina zaune ina addu,a abinda yafaru dani dazu yafado min a rai,
Cikin mamaki nadan motsa kadan lalai ba shakka sheriff udeen din, mune yabani magani na,
To a ina yasamay shi sai kuma natuna ai shine ma yakaini asibiti a birnin madina kuma yai min komai,a lokacin har naji saukin jikina
Oho,,, ,, hmmm watau wanan mutumin ,Don tsananin kulawar shi bai manta da lokacin yin period dina ba,ke nan yake nufi ko may
Wa,iyazu billah,, ashe duk wani motsi nawa yana kula dashi kenan,,
Da wanan tuna nen natashi zuwa cikin gida don in gabatar masu da dinner dinsu,
Saboda har yanzu ina dan jin jikina marana ban iya tafiya sosai,
Amma ya zan iya hada ido da sheriff din namu,,
Ko da naje falon kowa na falon zaune cikin dabara nake komai, na hada ma anty nafisa nata, nazo gefen da yake don in hada mai sai yace min yau bazai ci abinci ba in bashi juice kawai sai tea da zai sha anjima, kawai,,,
Tsayin da nadan yi don in saurari bayanin shi, yasa marana ya kara kullewa wuri guda sai wani irin azaba ciwo ke kokarin taso min,
Cikin hikima nadan yi dabaran barin wurin,
Muryan shi naji tun ban wuce ba yana cewa idan nasan cewa banda lafiyane inje inkwanta mana
kada in jawa kaina matsala tunda ba kullun ne mutun zaiyi lafiya ba,
Inkuma har ciwon ya matsa min ne inje inga likita ko za,a san may ke damuna,,,
Wayancewa nayi na,ce mai kainane kemin ciwo kawai, zai fada min zuwa anjima
Dadabara naja kafana zuwa cikin dakina,, yabini da kallon tausayi
Ina shiga dakin na haye gado na ,
Na dunkule wuri guda kamar yar mage duk kafana nashige dashi cikin jikin na nade wuri daya,
Saida nadan samu barci kadan a,hakan bandade ba na farka don ina son in dan fita, in karsa aikina
Ina zuwa Falon shiru yayi bakajin motsin komai sai karar naurorin dake aiki a falon,
Kayan tea da yace zai sha na hado mai acikin wani dan karamin ture,
Nakai bisa tebur din cin abincin su na aje,
Saida na kusa gama abinda nakeyi a bisa tebur din,
Na,hango shi zaune can wani dan corner da aka kebe afalon , bakowa ke zuwa wurin ba ,sai shi,
Don koda nazo gidan nafara aiki saida almustapha, yai warning dina kan zuwa wanan gurin,
Glass ne aka kewaye wurin dashi sai wasu kujerun masu taushi da tulin takardu, akwai alkur,ani mai girma da sauran litatafan addini ciki, sai computers iri iri,
Nikan shiga sau daya a sati don gyara wurin,
Ashe shi tun dazu ya gurin yana tura sako a computer wa mr William,
Koda zai fito saida suka kwashi artabu da nafisa kancewa, gaskiya ita bata yarda duk dare a ce mutun sai ya fita,,,,
Ba wani kulawa tsakann miji da mata hankade ta yayi gefe yafito abin shi yabarta tana mita,,,,,
Ita abinda bata sani ba shine bata cikin rayuwar shi sam don jinta yake yi kamar ba mace ba,
Shi duk da bai taba taraiyya da wata mace ba a,duniya sai ita,
Yansan labarin mata yakaranta komai a cikin wani, littafin
Mai suna, Surar ya mace na wani shahararen balarabe marubucin addini, musulunci, wanda ya, wallafa duk yanayin kowace irin mace,
Ita ko nafisa tadauka bai fahinci komai gamay da ita,ba
Tunda tanaganin tasha gyara wurin mamanta kafin tazo duk wani sadda baru da kayan mata an hada ta dashi,
Shiko anashi ban garen
Biyayya kawai yake wa tsohon shi kanta saboda ya fuskanci cewa baban nashi nason wanan hadin auren,,,,

Daga inda nake tsaye na hage shi, zaune yamaida hankali ga abinda yakeyi,kuma hankalin shi a kwance yake aikin
, bai,man san cewa, ina cikin falon ba alokacin,,,
Hankalin shi duk ya,naga computer shi,
sai yaji a,jikin kin shi cewa bashi kadai ke a falon ba
Da akwai alaman mutun a falon, baigama tune ba,
yaji motsi a bayan shi lokacin yasan cewa na shigo falon,
Daidai lokacin da nake aje cup din da zai sha tean cikin dan karamin tiren da na hada mai kayan tea din ciki,
Naje in juyo haka sainaga mutun gaba na tsaye,
saida nadan firgita, saboda tsoro, nadan waiga inda yake zaune naga tabas shi din ne a gaban nawa,
Kalo guda nai mai na,kauda ido na gare shi, saboda rigar barcin dayasa cotton ce tana nuna mai surar jikin shi waje,
Muryan shi naji yana fadin keda baki da lafiya may yasa kika fito yin aiki idan natashi shan tea din ai zan kira nafisa ta hada min,
Ki koma kawai ki,bar shi koni da kaina zan hada,,, , ba musu na juya don dama daurewa nake duk banjin dadi sam,
Nafara tafiya naji muryan shi yana cewa kin ko ci abinci
kai na kada mai alamar a,a
Batare da yakara magana ba naga yafara hada kayan tea din da na aje mai asaman tebur, din ,,,,,, tea mai kauri ya hada min ya miko min yace inje insha
Ya miko mi magani, yace Kuma in,tabbatar da nasha shi yanzu kafin in kwanta,nasamuace tare da godiya,,,
Nabar falon a duduke zuwa dakina,
Tausayina yakara kamashi, don harga Allah yana tausaya wa wanan yar yarinyar da aka sako ma,duniya ta yi rainon ta,,
Tunda nasha tea din da maganin da aka bani sai naji marana, da ya kulle min tam yadan sake sosai har nadan ji saukin ciwon
wani barci mai karfi ya kwashe ni, a hakan ,,
Bani na farka daga barcin, ba sai daidai lokacin da ake ta kokarin kiran sallah asuba,
Dama daidai wanan lokacin nake tashi, koda agida nake don fara ayukan mu, yau da kullun,,,,
Jina nayi cikin yanayin bako tare dani watau period yazo min, hakan yasani ni kara yin lankwas bisa gadon,
Da kyat nasamu natashi zaune na rarafa zuwa bayi don in,tsab tace jikina,
Bayan nafito sai na tuna cewa aiko nasiyo kadan pad ranan nan da mukafita da anty nafisa
Shinake ta nema cikin dakin tunda nasan cewa ban je dashi gidan hajiya ba,
Turo kofan akayi duk da ina cikin wata duguwar rigan da zura bayan fito wana wanakan,
Saida naji kunyan ganina hakan da yayi ba wani saya jiki,.
Yajikin yace min nace mai da sauki ledar dake hannun shi ya,miko min, yace min ina wanan ne kike bida,
Ledar pad dina dana sayo da muka fita nida NAFISA
Juyawa yayi yana ce min indinga kula da rayuwata tunda ni kadai nasan irin wahalar da nake sha,
Wayyo Allah kamar in shige cikin kasa don kunya kila yafi minti goma da fita ban iya daga ko kai ba balle in cire kafana,
Saida naji alamar bakona zai iya zubowa anytime nai saurin kai ma ledar kalo,
Tabas ledan kadan pad din da na siyo ne, ranan,
Haka nadaure na dan shiya jikina tsab cikin nasa wando da rigar jeans don gudun wahala,
Abokiyar aikina ce ta shigo dakina da ture a hannun ta ,
Kayan tea ne acikin shi sai sauran abin karin kumalo
Nai,mata godiya tace min sheriff ne yace akawo min nan kuma insha magani na,
Daga haka bata kara cewa komai ba ta wuce abinta,
Tundaga wanan ranan ban kara yarda mu hadu da sheriff ba ko a cikin gida
Saima muka fara wasan yar boya da shi yana sane da nufi sarai amma yakamar bai gane ba,,,
Yai tafiya zuwa Riyadh don dama yafi zama can din saboda aikin shi akusan can yafi yawa
Yanzu daine ma da su,ke kokarin bude wanan mai,ai,katar ta Abu Abdallah,
Shiyasa yake dan yawan zama cikin garin makka so sai,
Duk kwanakin da yayi bai gari cikin dadi da walwala nayi su, ban shakar komai,
Daga anty Nafisa kawai nake dan samun takura wani lokaci, don tana da yawan sa aiki,
Amma dai ba laifi ina ina jurewa da takurar ta,

Yau aiki yai muna yawa don saida muka gama abincin dinner sai anty nafisa tace muna wai bata son wanan saidai muyi mata wani mara nau,yi taci,
Don haka dole muka koma girka wani
duk da marance yayi muna, amma bai hana mu yin sauri ba,
Mun,gama komai muna jerawa a table ,ina dan wake ,wake na na larabci ,
Sai kawai hancina ya sanar min da akwai mutum abayana don fitinanen kamshin turaren sa, da ya gauraye falon,
Waigawa nayi kadan don in,tabbatar ko da shi din ne,
Don koda bai nan gidan namu baidaina kamshin sa ba tankar yana gari,
Ina waigowa naganshi tsaye yana kokarin karba waya hannu shi rike da briefcases din shi,
Wayan yake karbawa amma hannkalishi naga reni ,,,, ganin hakan danayi yasa nataka a hankali har zuwa inda yake nakarbi dan briefcase din nashi cikin ladabi ina mai sannu da zuwa,
Koda nabada baya ido yabini da shi yana mamakin yadda yaga nakara girma cikin dan lokaci guda,
Dai lokacin yakare wayan shi yana kokarin sa wayar a aljihu yadaga kai gefe anty Nafisa ce tsaye tana kallon shi,, cikin mamaki,,,,

[10/4, 14:31] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
4⃣5⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost true life story
Chapter 35 · 0% Book details