← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 139

Sashe 128

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

kai ina mamakin maganar ta , Tadaga min kai tace kwarai da gaske hakane ko ki na ganin baki isa yai maganar ki a gyefe bane, Ta ce har in ki na shakku ki daina don ni gaunau ce ba jiyau ba don a gaba yake fadawa Abba da hjy tsohuwa irin halaiyar ki, da abinda yasa har ya aure ki, Dan haka ki shirya kawai duk lokacin da ya bukaci ku koma ki bishi kawai batare da nuna bacin rain ki ba, Shin idan kin tsaya nan may zaki tsinta mijin anan din idan har kin tsaya, Daga kai nayi ina mamakin ta, kodai don bata san ko shekara nawa nayi can batare da iyayyena ba, Sai naji ansar kuma a bakinta, tana cewa kina yar karama ma ,kin inyi zama batare da iyayyenki ba balle yanzu da kike da aure a kanki, Kenan tasan koni waye tun farko wasu hawaye naji sun sulalo min a fuska na, Dafa ni tayi a kafada tace ki zama ma jajircewa akoda yaushe don ki lashe duk wani lanbar yabo daga mijinki , Ki zama mai mallake mijin ki ,koya mai yin adalci acikin ku, duk da nasan yana kwatantawa, saboda shi haka ya tashi mutum mai tsoron Allah, Kiyi kokari ki tarbiyartan da ya'yan ki cikin hikima da dabara ki hane su ga duk wani abinda zai kaisu ga koyon lalacewa, Hakan bazai kai ga samun nasaran ki ba sai kina kusa da mijin ki uban diyan ki, Dan haka kada ki kara bata ranki ga wanan tafiyan ki je ki zama mai yi nayi bari na bari kamar yadda aka san ki, Daga haka bata kara ce min komai ba sai shirun da yabiyo dakin, ido kawai ta zuba min, Sai can nadan yi ajiyar zuciya, na nisa, nadago kai na kalle ta na ce cikin siririyar murya na gode kwarai anty kuma zan yi kokari in koyi da duk abin da kikace, Kafin mu fito falo nai ma anty falmata godiya sosai acikin ziciya na kuma ina mai gode ma Allah da ya hada ni da ita , Hudu daidai sheriff ya iso inda suka kwashe mu zuwa gidan su Bashir An muna taro na arziki so sai an kuma nuna muna so da kauna na gaskiya, Ba mu wani dade ba saboda dare yayi mukayi sallama da su muka dawo gidan Abba, Washe gari har hjy tsohuwa muka dunguma zuwa garin su can wani local government ne, Ummu ta tare mu cikin jin dadi dakuma murnan ganin yan jikokin ta duk tana kokarin boye wa, Nikan sai ince gida nazo don gidan wan mahaifinane nazo, Aiko zuwa dare nan da nan yan uwan su Shehi dake zaune agari aka diga shigowa gani na ni da mariya, Duk wanda ya gan ni sai ace wai lalai, mun mafi diyan shi kama da shi, Hjy tsohuwa tasa fitina akan dole gidan ta da zamu sauka dan haka kwana guda kawai nayi a gidan Shehi na koma gidan hjy, Duk da Sheriff yafada madu mun fasa yin kwanakin da mukayi niyar yi anan da farko ,saboda wasu dalilai da suka taso daga gurin aikin su, Gyaran jiki sosai akai min dakuma kitso irin nasu na yan maiduguri, Gajikin jego dake samun kyakyawan kula ga kuma adon da aka yarfa min a,jikina Haba ai sai kawai na ko.a kamar wata bakar balaraba can Tunda nazo bamu kebe da Sheriff ba sai yau muka hade a dakin hjy tsohuwa, Ina zaune ina bawa Abbazannah nono yashigo tundaga kofa dakin idon shi na akai na duk daga mutane adakin yau sheriff baiji kunyar kowa ba, Kallo guda nai mai naga irin kallon da yake min sai da gaba na yafadi sai kuma yabani tausayi, Don a gaskiya yana da hakkuri sosai namiji lafiyye kamar sheriff mai mata uku yazauna kwana da kwanaki hakanan, Cikin murya kamar ta mai kasala yake min magana yace fadima maganar su gwago ne da man nazo dashi, Saboda gobe da mun koma ranar jumma,a da asuba zamubar kasar nan, Duk da naso in daure amma sai nakasa nadogo da sauri na kalle shi, Murmushi yai min kawai yaci gaba da zancen shi, Don haka ko can tare da su zamu tafi tunda maigari da kawu sunce sai kunyi arba,in kamar yadda al,adar hausawa take, Don hakane ma tun muna maiduguri na bugawa maigari na sheda mai cewa yayi hakkuri dasu zamu tafi, gabadaya Wani irin murna naji ya sauka min azuciya na, wanda banko iya lissafawa, Yace saboda agaskiya naji dadin zuwan su tare da mu sosai saboda irin kulawar da suke ba ku akai da kai, Azuciya na ko cewa nayi aini nafika jin dadin hakan don ni zama dasu sai jinaje kamar da innata nake zaune, Saboda gwago ta canza sosai saikace ba itace mai hattarata ba da ake zaton cikin shege da shi, Sam banga laifin su don sona yasa sukai min haka yanzu ko da suka gane gaskiya sun fi kowa farin ciki, Muryan shi naji yana cewa ina fatan zaki masu gamsashen bayani ko, Godiya nafara mai sai kawai naga yadaga min hannu, alamar bai so Ina jin lokacin da Sheriff ke shedawa Ummi zan cen airen Amal yace bazai dade zai dawo dan ayi bukin takoma can Naji dadin jin haka don ko ba komai zan samu yar uwata a kusa dani, Don haka nafara mata sherin cewa duk tafiyan mu guda nida ita tunda zama kasar mu yagagareni, Munyi sallama da yan uwa cikin wani yanayi kamar kada mutafi dan dan sabon da mukayi da jama,a, Gwago da mama matar mai gari jin labarin tafitan su sukayi kamar almara, Don basu taba zaton haka ba, Saiga shi cikin ikon Allah tafiyar yazo masu a cikin sauki, Mariya ko ina ga tafi kowa murna dan ina fada mata tai wani ihu ta kankamay ni saboda farin ciki, Da kanta taje yiwa sheriff godiya,, Kamar yadda yace hakan ne yafaru don da Asuba muka bar Abuja zuwa saudiya, Inda muka sauka ta jidda don haka Makkah direct muka nufa,,,,,,
Chapter 128 · 0% Book details