← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 139

Sashe 54

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Labarin da naji natafiyan nafisat yatayar min da hankali sosai agigice natafi side dinta,
Da sallama na ,nashiga dakin nata,
Kwance take saman gado ta dunkule waje guda da ka ganta kasan cewa tana cikin damuwa sosai,
Kallo daya nai mata sai naji wani irin tausayin ta yakamani,
Jin datayi alamar anshigo dakin nata shiyasa ta dan gyara kwanciyar ta kadan, tadawo da kallon ta sai tin kofar shigowa dakin,
A hankali nadan karasa har bakin gadon nata,
Kusan wani dan lokaci ba wanda yace kala tsakanin nida ita,
Gefen gadon inda kafarta yake, nai saurin isa gurin,
Maimakon inyi magana sai kawai nadan fara kuka mai tsima rai,
Shiru tayi nadan wani lokaci tana jina,
Saida ta daure sanan ta iya ce mim kin ji cewa zanbar gari ko,
Nadan gyada kaina alamar eh,
Tace min hakika fadima ke yarinya ce karama wacce tasan ya kamata a rayuwa,
Ta dan dago daga kwacen idon ta sun gada sun yi ja jajir, dagani tayi kuka sosai,
Sai jiya nagane cewa kina kauna na fadima, nakuma gane cewa duk abinda kikeyi ba don kowa kikeyi ba sai don Allah,
Nayi nadama da danasanin kuntata makin da naitayi, abaya wanda dana sani in rugumay ki,takar yar uwata saboda irin yadda kika rikeni,
Tsayin wani dan lokaci babj wanda ya,iya cewa kala acikin mu,
Ahankali na dan iya bude bakina nace don Allah idan har na saba maki kiyafe min don Allah
Tashi tayi ta zauna da kyau tace da sauri haba fadima duk iya zaman da nayi daku nice mai yawan saba maki,
Saboda rudin shedan da mugan kawaye,
Duk kokarin da zakiyi kifitar dani kunya kin yishi fadima don gudun kar zamana da mijina ya baci kinyi iya kokarin ki wajen gyara min zama,
Don ko jiya ina sane da cewa kece kika dauke abin da yar lici ta bani
Wanda in badon kin dauke a,yadda nake ji ajiyan wlh da nasha mai isata saidai su Abba su ganewa idon su irin abinda nake yi,
Kinga duk da Ahmad yasan abinda nakeyi da kuma irin plan din da muke shiryawa akanshi baisa ya canza min ba ko ya nuna min cewa, yagane komai,
Duk sai jiya wurin bayanin da salim yayi yass nagane cewa kece kika taimaka ma rayuwa na sosai,
Wanda in badon ke ba da ban san ya zata kasan ce dani ba awanan kasar,
Masu daukan doka a hannu ba sai ta baci ba
Tausayin tane yakara kamani so sai bansan lokacin da na rike taba ina kuka, ajikinta,
Ina fadin kada kitafi don Allah kiyi hakkuri ki zauna tare da mu,
Itama din kuka takeyi na nadama sosai da danasani
Mundan kai wani lokaci a hakan ba mai ba wani hakuri a dakin sai itace ma tai karfin halin cewa don Allah intaya ta rokon Allah akan irin rayuwar da take ciki,
Sai a lokacin nakula da cewa nafisa bata jin dadin jikinta har yanzu karfin haline kawai takeyi,
Abinda tayi yanzu yayi matukar bani mamaki saboda sai nake gani kamar a mafarki nake ba wai nafisan da nasani bace har take cewa in yafe mata ,,
Kai duniya abin tsoro ne gaskiya,
Idan bakabi duniya a sannu ba saidai tagama dakai karaf daya badai kai ka gama da ita, ba,,,,
Muna a haka ban mu fargaba sai jin muryan sheriff mukayi ya bakin kofa, a,storace muka waiga duk kan mu,,
Inda yake tsaye, fuska a daure, Gabana saida yafadi don tsoro,
Takowa yayi zuwa cikin dakin yanawa nafisa wani irin kallon kyama, Nima dai kallon nashi nakeyi da kumburarun idan nu na da su ka sha kuka acikin kwana kin nan,,
Tabayana yayi yana fadin may kukeyi anan dakin , wurin wanan mara,imani,
Kafin in bashi ansar tambayar da yai min sai nima na wurga mai tawa tambayan
Nace mai Sheriff din mu don,Allah kazama mai yafiya da uzuri ga duk wanda Allah ya hada ka zama dashi,
Kayi hakkuri kayafe mata kada ka bari ta wuce a,haka cikin wanan yanayin da take ciki
Dan dariyar yake yayi tukun ya juwa zuwa kofan dakin da ya shigo yana cewa
Da kin fara bani ansar dana tambaye ki kafin ki ce zaki min halin yan adam,
Bayan shi nabi da sauri don naga cewa yana shirin barin dakin,
Amma sai bancin masa ba don ya bi hanyar fita wajen gidan ne,
Daki na koma don in yi nazarin abin yi don gaskiya ban son tafiyar nafisat sam wlh,
Ina shiga dakin Amal ce kwance a saman gado na , tadauki wayana tana dakila,
Tana ganin na shigo dakin tajamin wani irin uban tsaki,
Tadan kalleni ta tabe bakinta idonta na saman wayan dake hannu ta, ta min ,
Wai ke fadima wata irin yarinya ce wai da bata da zuciya haka,
Wanan matar da har kike wani shishigin zata tafi, kinsan komai akanta,
Sanan saboda tsabar kiyayyan da take maki har iki,rari tayi da cewa sai ta halakaki, agaban kowa,
Kuma taso taiwa yayan mu sheri da kazafi duk akanki,,
Wai shine rashin zuciya kalar taki har kina kokarin tayar ma kanki da hankali,
Akan hukuncin da magabata suka yanke, ke ina ruwan ki da maganar manya da har zaki sa kanki aciki,
Jin da nayi tace maganar manya sai jikina yai sanyi lankwas saboda nassn cewa gaskiya Amal ta fada min bawai ba,
Kan gadon nakaraso na zauna jiki ba kwari ajikin gadon nadan jingina, gami da yin tagumi da hannu na guda,
Ido tazuba min da alamar mamaki take kallo na
Cikin tausayawa nake magana, nace haba dai Amal da ba,a yafe ma mutum aida Allah ya shudemu ko kamar mutanen farko,
Saboda irin aiyukan zunubi da sabon Allah da dan Adam ke aikatawa akulun,
Zancen Amal takawar tana fadin ke fadima waiko ma kin shirya kayan tafiyar ki kuwa,
Sai a lokacin nadan yi murmushin karfin hali nace har may zan shirya Amal
Hararana tayi tace min ina kayan da yayanmu yasaya muna badasu zaki ba
Sanan kinsan cewa dasu Aisha da Umar zamu tunda da maman su za,a tafi,
Sai alokacin nadanji wani dan shakat azuciya na jin ance aida su Umar zamu tafi

Washegari muna kofan gida duk kanmu gaba dayan mu su nafisa da Abba da wani dan uwar su nafisa wanda ya wakilci,, mahaifinta sai hajiya tsohuwa ,
Nafisa tafito cikin shigar kayan indiya wando da riga sai gyalen da ta dan rufe kanta da shi ,
Kallo daya zakai mata tabaka tausayi saboda koba komai taga samu taga rashi,
Saboda samun miji gare ta irin sheriff din mu ba wasane ba gareta, saidai dayake, ,, ba,adai fidda tsanmani kawai,
Ni, a haukana ganin nakeyi, Duk wanda ke wurin ya,na tausayin nafisat,ne,,
Ashe ni ban sani ba kowa dake wurin, murna yakeyi da tafiyan ta don duk ta ishe su agidan basu da yadda za,suyi ne kawai
Kuma shi sheriff ba mai daukar magana bane da yakori kusan kowa na gidan,
Ina hada ido da ita sai naji wasu yan kwalla nabakin ciki na batun sulalo min,
Amal ta kula da hakan sai ta dafa min kafada tace min hjy tsohuwa na magana dani,
Muna kallo suka wuce agaban mu ba mu da yadda zamu yi da ita,

Mumadai gadan gadan shirin tafiya mukeyi zuwa madina inda zamu fara wani sabon rayuwa,
Gaskiya sheriffudeen Ahmad yai muna na mijin kokari sosai
Don ni azatona wanan gidan nashi da nasani,na ma,aikatar su dake madina zamu zauna
Ashe abin ba hakana ba hakana yake ba,,
Don gata ne na sosai akai muna wani dankareren gida mai kyau aka sai muna a tsakiyar gari anan zamu zauna ,
Gidan baida nisa sosai da makarantar mu, da kuma masallacin haram,
Zamu iya yin karatun mu ,zamu ,kuma samu yin ibadar mu a sau,kake ,
A gaban ummi muke ana gobe zamu bar garin tana muna fada kamar yadda duk wata uwa ta kware zata iya yiwa danta fada,
Tai muna nasiha sosai da ja muna hankalin kanmu guji don abin duniya wanda hakan shi yafi yawa ga alumma yanzu ,
daga karshe tai muna nasiha akan kuka da ibadar mu fiye da komai na duniya,
Sai fatan alheri da taimu dakuma muriki junan mu cikin amana da fahintar juna,,,
Shiru mukayi dakin saboda nasihar nata duk ya kashe muna jikin mu, sosai wlh,

A hankali yake saukowa daga matakal jirgin idon shi mane da wani dan farin tabarau wanda yadan kara ma fuskan shi kyau
Fari dogo kyakywa dashi matashi ne maiji da lokaci da ganin shi,
Shigar shi kawai ta isa taba mutun ansan hakan.
Kallon garin yake yi a tsanake yana anyana cewa lalai tsarin garin tayi mai daidai,
Hotel din filin jirgin yadan kama don yadan huta gaji kafin ya kira dan uwan nashi dayai ma tafiyar bazata,
Saida yadan huta sanan ya kira da uwan nashi don ya sanar mai cewa yana kasar tasu pa
Chapter 54 · 0% Book details