← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 139

Sashe 75

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Yau shiru tunda safe banga Aziza ba a waje ganin da nayi cewa anytime tafito sai ta nemay inda nake ,
Yasa da banganta a waje ba na hausama zuwa dakin su,
Kwance take rub da ciki nai sallama a hankali ta ansa min ,
Tajuyo daga rub da cikin da tayi kwancen, sai naga fuskan ta ya kunbura idon ta da almar tayi kuka ma,i,shin ta,
Subbahanallah nace da sauri na isa gurinta ina mai kokarin dafa ta,
Nace cikin rawar murya hjy mai yasa may ki ,ko baki da lafiya ne,
Duk lokaci guda na sako mata wanan tambayar a jere da juna
Girgiza min kai tayi kamar karamar yarinya,
Ta, bude baki da kyat tace min babu ko daya
Fadima
Matsalata tafi karfin fahintar ki kona fada maki bazaki gane ba saboda,
Ke yarinyace, shiru nayi kamar ina na,zari, can nace to amma anty aiko banza gane ba ai zan yi kila taimaka maki ta wani hanya ko,
Saida tadan shere wani hawaye dake shirin fito mata daga cikin idonta, ta hade miyau da karfi sanan ta mike da ga zauna
Hannaye na takama duka biyu ta hada wuri guda tace Fadima inda zaki fahince ni da kin san cewa muna cikin tashin hankali dagani har Ahmad saboda matsalar da ta samay mu,
Sai duk naji na matsu da insan kowata irin matsala ce haka wadda har yasa wanan jarumar matar kuka haka ,
Dan Allah hjy ki daure ki fada min koma maye ko zan san abin yi pls,
Fadima muna cikin matsala rashin haihuwa nida Ahmad munje asibiti likita yace bazan iya daukan ciki ba,
Sai kuma tasa kuka wi,wi,
Sai naji duk hankalina yatashi,, saboda wanan maganar ba karama bace ga duk wani mahulukin da yasan ciwon kanshi,
Tana shere hawaye taci gaba da fadin ,sai wanan test din da mukayi na karshe likita yace muna inda zan samo wata wacce zata taimaka min asa mata cikin ma,ana ai mata dashen cikin
Idan ya fara girma sai amayar min da abina yace yana ganin haka zai sa in samu baby,
Kinga kuma shi Ahmad baya ganin laifin kanshi sai nawa kinji halinda naje ciki fadima, tanayi tana kallon fuskana don taga irin re,action din da zan nuna,
Fuskana fal da tausayin su ban san lokacin da nafara kuka ba ,wi,wi, nima don ba karamar magana bace wanan,
Mutun kamar sheriff ace ba zai haihu ba, treble,,
Muryanta naji tana cewa amma fa kada ki fada ma kowa wanan sirinane da mijina na fada maki,
Saboda yarda da nai miki yasa har na fada maki sirina,
Hmmm hmmm
Wani sabon kuka nasa mai tsuma rai an muka rugumay juna mukai ta kuka har saida muka gaji,
Nakoma dakina fam da tunane da tausayin su,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎✈✈✈ *TAKARI*✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
6⃣7⃣
BY
🐎 ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Almost true life story,,,,,

Cikin dare na kasa yin barci mai nauyi saboda yawan tunanen da ke ta addabata,
Juyi kawai nake yi ina faman ajiyan zuciya da dan guntun tsaki,
A, gaskiya na tausaya ma sheriff din mu so sai yanzu ace duk tausayin shi da mutuncin shi bazai haihu ba,
Ashe haka wasu Allah ke halittan su, batare da haihuwa both miji da mata,,
Saboda ni nadauka cewa mutun guda akan ce baya haihuwa mijin ko matar,
Amma su sai,gashi wai duk kan su case din su gudane,
Babu mai karfin haihu daga cikin su,
Dan sanyin da naji shine cewar da tayi idan an yi dashen cikin za su iya haihuwa insha Allah,
Kwancin bai min hakan yaban damar mike na shiga bathroom na dauro alwala na fara nafila ina fadin bukata na, a wurin Allah,
Nafilan nan da nadan samu na gabatar yasani jin sanyi a zuciyana ,
Har na dan samu barci maidan nauyi yadauke ni zuwa asuba ,
Hakan ne ma yasani makara da sallah asuba,
Saida gari yadan yi haske nafar ka zubur da salatina a baki,
Saidai duk jikina ba karfi hakana naje nadauro alwala,
Ina zaune inda na sallamay sallah asuba ina ta kwarara ma sheriff da iyalin shi addu,a,
Shawar da na yanke tun cikin dare shi na yi niyar aiwatar wa,
Amal na dakinta kwance nafito nace mata zan je masjidul nana Aisha ,,
Da mamaki ta kalleni daga kwancen da take tace min tunda safe haka,
Murmushi nadan yi mata, nasamu gefen gadon ta, na zauna ina gyara belt din takalma na,.
Ido takura min har na kare daura belt din sai tace min may ke damun ki fadima,
Cikin dan basarwa nace mata kamar ya fa,
Hmmm kawai tace min,
Sai kuma tace bana son ki sa kanki acikin fitinar da ba zai amfane kiba, wlh
Saida na mike tsaye da kyau nace mata ba wani fitinar da nasa kaina, aciki Amal kece dai ke hasashen hakan,
Amma for me ba komai ina fadin haka na sa kai nabar dakin
Zuwa masjidul bai dauki wani lokaci saboda sanin hanyoyin da na yi acikin sauki,
Ina isa nai addu,a na dauro niyar umrah nadinga addu,a da larabci, da hausa kai har mada turanci duk na hada ,
Saida na gama dawa,fi, nadawo daidai saitin indararon nan naita zuba addu,a
Saikuma na koma daidai kofar dakin naba mukamin ibrahim baya, nadinga kwararo addu,a agurin,
Dalilin dayasa nai haka gurin hjy Laila nataba ji suna hira da hajiyar mu cewa indan mutum yana neman haihuwa koda dan uwan shi ne keson haihuwa,
Sai yaje yayi dawafi, ga bakwan karshe saika dada addu,a agurin indararo saboda anasa rai cewa guri ne da duk abinda ka roki ubangiji agurin zai ansa ma insha Allah,
Indan ka gama sai ka dawo daidai saitin kofar shiga shi ai,nihin dakin ka,aban ka tsaya tsakiya, inda hali ka dauki ruwan zam,zam kayi wanan dawafin da shi,
Karoki Ubangiji Allah bukatar ka insha Allah Allah zai karba ma mutun,
Wanan ruwan zam,zam din sai kaba wa wace ko wanda ke da lalurar haihuwa ko wani ciwo yasha ya shafa tare da bissimillaj,
Sanin danayi cewa Aziza bazata sha ruwan ba kila ko nakai mata yasa ban dauki ruwan nayi mata dawafin da shi ba,
Saidai addu,an da na tsaya tsakanin mukamin Ibrahima da kofar dakin ka,aba nayi na Allah yataimaka ya bawa sheriff din mu haihuwa mai albarka a rayuwan shi,
Tare da kwararo wa sauran al,umman musulumi a ddu,a,
Daga karshe na tsaya daga can gefen yamma kadan nadibi ruwan zam,zam nasha sai nayi nafila raka,a biyu
Nagode ma ubangijina subbahanahu wata ,ala,
Dana gama nadade gurin zaune na zubawa dakin ido sai naji wasu hawaye masu dumi suna zubowa daga ido na,
Nadade a hakan sannan natashi nasamu guri na zauna a gefe guda,
Ranan anan nai sallolina har i,sha,i ina gurin,
Sai da dare na zo hanya don in tare taxi zuwa gida sai na dinga jin hayaniya,
Ko ban waiga ba nasan cewa yan bagaladine ke kokarin kama wasu daga cikin yan yawon takari,
Hakane ne kuwa don dai daga inda nake inajin muryan su sunacewa Nigeria,
Duk da hayaniyar da akeyi agurin bai hanai jin kuru,ruwar matar da aka kama ba
Azuciya na ,na,ce ya Allah yasa mutanen mu su daina wanan kazamin da bi,ar , tazuwa yawon takaru ba lasisi shiga kasar,
Idan ma mutum na so za,s iya bashi, lasisi idan har yabi ta hanyar daya dace,
Saida na ji cewa ni a halin yanzu zan iya zuwa ko ina saboda ina da kardan zama akasar ,,
Wanda bakowa ne yai min wanan hanyar ba sai sheriff Ahmad Lawal Zanna,
Zuciyata jinta nakeyi tai min shakat kamar an cire min wani nauyi acikin ta,
Haka na dunfari gida cikin wal,wala da sakin fuska ba wani damuwa atataredani,
Chapter 75 · 0% Book details