← Book details Takari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 139

Sashe 29

Takari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A saudiya kuma muna can abin mu munata harkokin gaban mu don ba wani aiki mai yawa da muke yi kamar da
Don tunda muka samu wanan aiki da hajiya laila tai muna hanya aikin gidan sheriff din mu
Agaskiya mun rage wahala so sai bakamar daba don yanzu ko abinci bai muna wuya
yanzu duk yan gidan mu sun,dawo da aikin su nan gidan
saboda aikin da za,ayi na abincin azumi dana lokacin aikin hajji , watau abincin Karama,,
A, yau muke sa ran dawowar sherrif din mu daga dogon tafiyan dayi nakusan wata guda, zuwa gida Nigeria da kuma kasashen larabawa ta tsakiya,,
Munyi aiki sosai saboda dawo wan nashi,,,,,,
, aikin kamar su ,,gyaran gida zuwa yin abinci mai kyau da kula da dabbobin gidan, saboda kada sheriff yace mun barsu da yunwa
Wanda agaskiya da yana nan da bai nan duk gudane muna kula da komai tamkar yana gari,,,
Don shi kuma ,akidar shi da ya iso daga tafiya in yayi, gurin dabbobin shi zai fara zuwa yadan diba lafiyan su sai dan yi wasa da su kadan san nan ya shige gida,,bai kara fitowa indan ya shige,,
Yau ma hakance ta kasance ina wurin da nake kiwon tsuntayen
Jiminan da ake kiwo a,gidan tana miko min wuya ta ina tsokanar ta ina ta dariya dagani sai tsutsayen a wurin,,,
Dariya na nake tayi hankali kwance don ganin tana son ta tsakwace min hannu niko ina cirewa cikin sauri,,,,
Kamshi yan company al,rahab naji duk ya cika min hanci na
Ko ban waigaba nasan Sheriff ne tsaye a wurin,
Don ni Har yanzu nauyin shi nake ji sosai tun lokacin da yasan cewa na fara period, ban son in,ganshi,,,
A,hankali yataka har zuwa inda kejin Akun shi yake,,
Sannu da zuwa nadan yi mashi sama sama lokacin yana magana da Akun na,shi,,,
Saina dan saci kallonshi naga yadan ramay har da baki yadanyi, kadan
Ganin bankalin shi naga tsuntsun yasa nadan juya ahankali don in,tafi,
Zan wuce shi naji muryan shi yana ce min ya jikin hajiyan mu,
saida nai mamakin jin wanan tanbayar daga bakin sheriff din na mu daidai wanan lokacin, dayake tare da gajiyan tafiya,,,
Nace mai taji sauki
Yace min, ,I hope tana ganin likitanta har yanzu nace mai
eh, kawai
Cikin gudu gudu nabar wanjen,
Don kada yakarayi min wani tambaya kuma,,,
Yagane ni sarai kunya shi nake ji
amma dai shi ina ruwan shi tunda yasan cewa mace nake
kuma ai dole inyi wanan abin,,,

Bayan yadawo da kwana biyu mukayi baki daga Nigerian
Sai murna nakeyi da rawar kafa ganin ga mutanen Nigeria sun zo
Don ji nakeyi kamar zasu bani labarin inna na,,,,,
Sunkai su goma maza da matan su
duk da mu bamu fahinci komai ba saidai munga ana ta gyara wuri
kamar irin dakunan dake rufe ba kowa acikin sh, kuma ba ko,,yaushe ake bude su ba,,
Sai gashi Yau ,duk an bude su ana ta gyara ana sa wasu kaya kamar na kwalliyan mata aciki, su,,,
Nidai ban fahinci komai ba
Sai kusan yamma zamu tafi gidane mama may abinci take ce muna wai muzo da wuri gobe saboda munga anyi baki yan kawo amaryan sherrif din mu daga Nigeria,,,,
Amarya na kara maimata maganar na ta,,,,,,,,

🐎ZEEE MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎
[10/4, 14:25] ‪+234 703 602 1388‬: ✈✈✈TAKARI✈✈✈
👣👣👣👣👣
👣👣👣👣👣
4⃣0⃣
BY
🐎ZAINAB IDRIS MAKAWA🐎
🐎HUGUMA GROUP🐎

Murna da annashuwa sun tabbata ga mutunin da tunanen hisabin Allah ya hanashi tara dukiyan ta hanyar haramu,,,,

Yan Huguma groups da Teema luv group maman fati group, mama nawal group Allah ya kara dauka yasa mugama da duniya lfy,,,

Almost true life story,,,,

Ta ce min eh
ai sheriff din mu yayi aure ,itace aka kawo shiyasa muka ga jama,a sun zo daga Nigeria,,,
A gaskiya munyi murna sosai dajin cewa sheriff din mu yayi aure
Farin ciki fal azuciyan mu saboda munyi sabuwar uwan daki,
Duk da ba musan halin taba mun dai yi murna da hakan,,
Ranan cikin farin ciki muka bar gidan muna jin dadi
Muna zuwa gida labarin da mukaje ma hajiya dashi kenan yau
Duk da bamu san ko wace ce, amaryan ba daga cikin bakin da,su kazo,,,,,
Saida muka gama komai muna zaune sai Rugaiyya ke min ita gaskiya bata ga alaman amarya daga cikin bakin da suka zo ba ,,,
Saboda may kikace haka inji yumma
Naga duk kamar ba yara bane kuma babu wace tadan nuna alamar lulubi ko wani dan jin kunya kunya, hakan ga kamar yadda amare ke yi,,
Ina gefe ina gyarawa hajiyan mu kayan wanki da nayi mata tun daren jiya
Yau da safe ban samu gogewa ba,
Hiran su yasa nadan shiga tunane cewa aiko koni din banga alamar wata yar gaye ko amarya wani sign na amarya ba cikin bakin,,,,
Sukaina ce tace ita,ko gani takeyi kamar wanan bakar mai dan rawan kan nan itace amaryan
Don taji lokacin da take cewa don may za,a ajeta dakin kasa
Ita tafi son sama tare da na sheriff,
Sai wata mata daga cikinsu tace ai tunda nan yabaki sai kiyi hakkuri dashi hakana
Taji ana cewa Nafisa don Allah kibi wanan mutumin asan nu kin daifi kowa sanin yadda akai wanan auren ,,,,,
Ki diba fa shekara nawa kina zama agida kuma kiji yadda kaunar mahaifinki tanuna hassadan ta da auren naki
Yanzu duk wani jidakai ko wani girmankai da iya boko irin naku yakare
Indan har kina son wanan daulan yafita hannuki kina ji kina gani to bissimillah ki ga ki ga ,,,,
Bata karasa maganar ba taga ina falon ina hada masu abinci sai tai shiru
Banji karashen maganar tasu ba inji Sukaina,,,,
Cabdijam inji Anty Rugaiyya
inko har wanan din itace matar gaskiya wata killa ba shi yabide ta kamshi ba,,,
Duk hiran da suke yi ina jinsu sai nazarin maganar nakeyi
Karshe na nisa nace koma dai may,ye aishi ya, auro abinshi mukan namu aiki mu bar masu guri,,,
Can cikin dare mun fara barci sai kawai muka dinga jin ihu har na tashin hankali,
Nai zubur zan tashi infita sai hajiyan mu tace min walahi duk nafita dani za,a hada
Tace min Askarawa ne da yanbagaladi suka kawo samamay yau shiyan mu,,
Wata kila watace suka gani suka biyo ta har nan don suka ma
Jin haka duk mukasha jinin jikin mu don tsoro, daidai kofar mu suka tsaya suna ta buga ma wa, yanda suka kama tsawa,
Muna labe munyi shiru kamar ruwa yaci mu ba wanda yayi ko dan guntun motsi cikin mu
Hakan da suka ji tsit yabasu damar wuce don suna zaton ba takari acikin gidan ,,,,,
Don da datakari da masu shi sunji tsoro sun fito dagudu, suna batun tserewa,
Amma jin shirun dasukayi unguwar tamu yayi,
yasa suke zaton sauran gidajen duk na,larabawa ne kawai,ba wani sauran takari wajen,,,,
Munajin tashin motocin su muka firfito, daga inda muka boye,saida wasun mu suka kewaya don tsoro,,
Nice, ta,farkon fitowa wajen gidan mu
don muga kowace ce aka kama daga cikin ,
Duk da gari bai karkare waye ba,
Amma mun,gane cewa lawisa ce aka kama
kuma ita lawisa din nan tanada diya biyu,mace da namiji,,,,,da ta samu dawani balarabe
yaran kuma sun biyo balaraben sosai,,,,,
Ashe koda aka kamata bada yaranta ba saboda ganin da sukayi yaran farare ne,,,
Haka muka karasa wanan daren cikin fargaba da tashin hankali,,
Dasafe kafin in,wuce naje gidan su lawisa na diba yaran nata,,
Aiko nasamay su zaune yaran suyi kuka sun gaji
sun hada kansu wuri guda sunyi tagumi zaban tausayi
Jawo su nayi zuwa wurin hajiyan mu
Aiko hajiya naganin mu tamike tsaye
tana,cewa, fadima kina da hankali kuwa
Kowa baije yadauko ma kanshi wahala ba ke zaki je ki dauko muna
muna fama da kan mu ,muma tamu ta,ishe mu ,,,,
Shiru nayi saida nabari tagama magana nace haba hajiya wa yan nan yaran fa suna bukatar taimako a yanzu,
Sanan kituna wasila fa tana iya kokarinta da mu,
Idan baki da lafiya muna gurin aiki takan zo tana diba muna ke,,,
Sauran yan uwana da basu fita ba sukayo kaina ca,,,,
Kamar zasu cinyeni dan ya,,
Yaran na takure gefe guda sundan rgumay hannun su ,sun wani man,ne majunan su ,zaban tausayi
Jawo su nayi nai masu wanka cikin sauri nadauko abinda zan karya kumallona da shi nabasu,
Har dan abinda zasuci darana saida na hada masu,shi ,sanan nafita zuwa wurin

Nikaina nasan cewa yau,na makara sosai,
Ina fita taxi, Kai tsaye na fito na mika ma mai taxi kudin shi ,
Duk da naga Almustapha a,kofar shiga gidan namu, kauda kaina nayi gefe kamar ban ganshi ba,
Don shima yasan cewa bazan gaishe shi ba,
Fada yafara yi min baiko kai aya biyu bu nadaga mai hannu alamar ya isheni hakana,
Cikin mamaki yake kallo na yana kuma yaba karfin hali irin nawa ,
Har shine zan daga wa hannu,
To yau kowaye min tsaye sai nabar gidan nan ,haka yake fadi azuciyar shi,,,
Na ci gaba da magana ina cewa shike nan don muna aiki bamu da incin kanmu ko wani lokaci na kan mu,
Ai yakamata a,dinga muna uzuri aduk lokacin da aka ga mundanyi wani abu bawai adauki matakin da babu dalili ba
Da in tsaya kana mari na ko zagina duk lokacin da kaga,,,,
Ban samu karasawa ba naga Sheriff's atsaye gaban mu yana muna wani irin kalon mamaki,
Mari mari fa,, Almustapha ,Subahanalla subahanallah ka doki mace macen ma,,,,,
Sai ya kasa karasa wa, naga kawai ya dunkule, hannunshi ya dan daki gudan da shi yana fadin subahanallah,,,
Nikan nasa kai na wuce cikin gidan ina jin yana cewa yaushe kai wanan aikin bansani
Ko kana dukan mace ita wanan din may zaka daka acikin ta,,,
Wuce wa yayi ciki gidan ran,shi bace dagani kasan yayi mugun, hasale ,yabar almustapha a wurin bakin get din, cikin damuwa,,,,,
Don ko yaga fushi yau karara a,idon sheriff din,,nashi wanda rabon shi da yaga wanan fushin yadade,,,,
Chapter 29 · 0% Book details