← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 190

Sashe 98

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Ta kasa dauke idanuwanta akansa Haka kurum bata san Dalili ba Zuciyarta ta fara Bugawa Fat!Fat!yanayinsa da komai ya tafi da Tunaninta wanda ya Haifarmata da kuramai ido ta kasa Dauke idanunta akansa.
Shi kuwa Tunda ga wannan kallon bai karama kallon Inda take ba ammh yanaji ajikinsa Tana kallonsa Tattare Naman goshinsa yayi waje daya cikin Takaichi ammh yaki yarda ya Kara kallon barayinta Akallon Farko yaji Kwata kwata yarinyar batamai ba Daga yanayinta da komai Tun kafin yasa itadin wacece Tunda shi dai Tunda yazo bai taba ganinta ba sai yau.
Ita kuwa kallonsa take Tana so Tayi Tunanin waye shi..?Domin bata taba ganinsa ba ko yana daga cikin Ya"yan Baffa Malamin ne bata sani ba..?koma waye ajinsa da  yanayinsa sun mata a irin yadda take son ganin cikakken Namiji mai cikar Zati da Haiba.
Basheer ne ya Daga ido ya kalli Imran Daya ke Tsaye kikam aransa yana mamakinsa Shi ko gajiya ma bayayi Gyaran Murya yayi yana Fadin"Imran zo ka zauna mana..Kana ta Tsayuwa..!
Yafada yana kallonsa Shi kuma dan yamutsa Fuska yayi kamar yace A"a sai yaji bazai iya Ture alfarmansa ba Haka kurum Sagir kuwa yana Shirin cema Basheer ya kyalesa bazai zauna ba sai gashi ya bashi kunya ya Fara Takawa Cikin Takunsa na isa da Sassarfa ya isa kusa da Basheer din ya Zauna Lokaci Daya yana Harde Hannayensa saman kirjinsa yana Jingina da Jikin kujera Bai saki Fuskarsa ba sai ma kara wani Hade rai da yayi,su Sadam suna gefe suna kallon komai Mirmishi kawai sukayi akallah dai ya Fara shiga Cikinsu.
Dago idon da Imran zai yi suka kara Hada Ido da Sajida dan Waro manyan Idanuwansa yayi akanta irin Lafiya..?sai lokacim ta sunne kanta A kafadan Mami Asma"u dake gefenta sai alokacin Taji kunya ta kamata Imran kuwa Dama ya Fahimci Sajida ita waye karamin Tsaki yaja Har sai da su Basheer suka Juyo suna kallonsa bai basu daman mgana ba ya Kirne Ran nan ya Kauda kansa Lokaci Daya yana wani Dakuna Fuska.
Khamis ne Dake kusa da Sa"id ya taso yazo ya zauna Kusa da Mami Asma"u suka sakata a Tsakiya kenan Kallonsa Tayi Tana Fadin"My son ya wajen aikin naka..? Hop ba wata mtsala ko..?
Tafada Cikin Kulawa da Annurinta na son ya"yanta.
Kansa ya Dora saman Kafadanta yana Fadin"Komai Normal Mami na..I miss u..,!
Sumar kansa ta shafa tana Fadin"Muma muna kewarka Our Son..!
Sajida dake gefe ta Tura baki Tana Fadin"Wai Mamina..? Sai kace Maminka ne kai kadai..?
Kallonta yayi kafin ya Dago kansa yana Fadin"Yarinyar nan baki da kunya kin Rainani ko..?Shegen son jiko kamar mage ga Umai ce ta Shiga Cikin yan"uwa ke kuma kina nan Wajen Mami kina Sakale da ita Kamar Zaki koma ciki..!
Yafada Cikin jin Haushinta Sajida ta kara Nanikema Mami Asma"u Tana Fadin"Mami kin gansa ko..?
Mami Asma"u tace"Zaka fara ko..? Kaifa babba ne..Namiji kuma Ita kuma Macece ko aure tayi a wajenmu She is a kid..!
Bai ce komai ba Sanin wacece Mami Asma"u kai kawai ya Rausayar Daidai Lokacin da idanuwansa yakai kan Imran wanda shima yake kallonsu Duk da ba suna Kusa bane sosai sai dai Yana jin duk Abunda suke Fada Haushi duk ya kamasa Matar nan yar Renin Hankali ne daga ita Har ya"yanta da Mijinta They are all Selfish.
Bawai fa bai gane Khamis bane ya gane sa Sarai domin ya tuna gabda Rasuwar su Anni da Abba ya matsamai suka zo suka kwana Biyu Khamis din ma yazo Tare da Baffa Kabiru kawai dai Shi bai son mu"amala da Khamis ne,Haka nan yaji yaron bai mai ba yana ganinsa Kamar Mahaifinsa ne,kuma shi baya Doguwar Mu"amala da wanda Ra"ayinsa da Zuciyarsa bai kwanta Dashi ba,Bakinsa ya Mele Lokaci Daya yana wani Yamutsa Fuska kamar yaga Kashi ya wani Dauke kansa Khamis shima ya kallesa a Saukaken kafin shima ya Kauda kansa Mikewa yayi ya koma cikin su Sa"id da Yusuf Sajida kuwa Tana jikin Mami ammh gabadaya Hankalinta da Tunaninta na kan Imran wanda bai ma kara Kallon Barayinta ba Sajida ko Wayar nata bata kara Dannawa ba Saboda Kallon Imran gabadaya ya Dauke mata Hankali.
Waige waige ya farayi acikin Falon ko zai ganta saboda yaga ga su Munari na Taya Baba Asabe jera abinci ammh bai ganta ba sai yaji ya Damu,Falon Dayake isu isu ne kadai su Abba suna Dakin Daada,Kamar ya share sai kuma ya kasa Kuma bayason ya Tambayi Munari ta Rainashi sai kawai ya Fito da karamar Wayarsa Ya Shiga Wajen Tura sako.

"Kina ina..? Ban gan ki ba..?

Haka kawai ya Rubuta mata ya Tura mata Sai dai Har tsawon wani Lokaci yana Duba wayarsa bai ji sakonta ya Shigo ba alhalin yana da Tabbacin Inda Lafiya da Tuni ta bashi amsa sake Turamata yayi.

"Ki amsani mana..!
Chapter 98 · 0% Book details