Sashe 12
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
haka yaron da ba wani saninsa yayi ba yazo har gida saboda ita. Bai gama mamaki ba Yaji Muryan Imran din Ciki Kaushi kai tsaye yana Fadin"Dama kan mganar Auran yayana ne...Gidan Dayake son yarinyar sun nemi Daya Turo mgabantansa Shine nazo na sameka ina so ka Shige masa gaba a Bangaran Neman auran..! Ba wani Roko ko alfarma kai Tsaye ya Fadi mganarsa kuma bai Damu ba. Baba manu mamaki ya kamashi ya kalli Sagir,wanda ya Sunkuyar da kansa domin bai ta cewa Sanin Halin wanda ya kawon. Cikin mamaki yace"In shige masa gaba..? To ina iyayenku ko nace Waliyan ku..Ma"ana kanin Mahaifi ko Kanin Mahaifiya ko wani Daga Cikin Danginku..! Imran kamar bazai ce komai ba sai Chan yace"Bamu dasu..Gidanmu mu kadai ne Dagani sai yaya na sai kanwata sai Abbanmu..Kuma shi din bai da Lafiya ne shiyasa nazo wajenka..! Baba manu ya gyara Zama yana Fadin"To baku da yan"uwa ku din Daga sama kuka Fado..? Sai alokacin Imran ya kara Dago kai yana kallon Baba Manu Cikin wani yanayi kafin yace kai Tsaye"Eh..! Ba Baba Manu ba Harta Sagir sai da ya kalli Imran yana Auna masa Harara da ido Cikin Kufulwa da Rainin wayau Yaron Baba Manu yace"Kuma kace Min Eh..! Imran yace"Eh..Ai kaima kasan ba wanda ya Taba Fadowa Daga sama..Ballatana ka Tambayeni ko mu Daga sama muka Fado..! Hankalinsa kwance yayi mganar Zuwa Lokacin Ran Baba Manu ya Fara Baci Cikin Hargowa ya kalli Sagir yana Fadin"Au daman da saninka ka Kawomin wannan Tsagerin yaron har gidana zai Cimim Mutumci..? Sagir ya kwaso Rantsuwa Baba Manu ya Dakatar dashi da Fadin"Maza tashi ka Tarkatashi ku barmin gida kafin na Saba maka..ko ce maka akayi ni Mutumin banza ne..!? Sagir ya Sadda kai yana Fadin"Don Allah Baba kayi Hakuri..Ba Cin mutumci zai maka Shi haka yake don baka Sanshi bane..Imu ka bama Baba Hakuri don Allah..! Ya karishe Fada yana kallon Imran Din da har ya Mike daga Tsugunnon Cikin mamaki yace"Saboda mene zan bashi Hakuri..? Nayi mai wani Laifi ne..? Mgana na kawo mai ni kuma ya Tambayeni na bashi amsa do i do Something wrong..? Bana bada Hakuri a inda ban aikata komai ba Mganar aure ai Mganar alherice balle yace Mganar Shanshanci na kawomai..! Yafada Hankalinsa kwance yana Laluban Aljihunsa Cikin Takaicin ya manta bai Fito da Tabansa ba sai dai Lether din,Karamin Tsaki yaja ya juya zai Fice Daga gidan Baba Manu ya saka baki ya kira Sunansa Tsayawa yayi kafin ya juyo Da kai ya gyada mai kafin yace"Dawo ka zauna muyi mgana..Na Fahimceka! Yafada da Dan Sakin Fuska Domin a kalaman yaron ya gama Fahimtar sa irin yaran ne kaifi Daya marasa Tsoro,Gaba gadi basu karya ba Munafunci. Inda ya tashi ya koma ya Kara Durkusawa Cikin mamaki Sagir ke kallon Baba Manun sanin Halinsa na Fada ammh sai me sai yaji yace ma Imran din"Wani gida ne shi yayan naka yake neman auran..? Ajiyar Zuciya ya sauke kafin yace"Gidan Alhaji Alhassan Buhari..! Baba Manu yayi jim kafin yace"Kardai kace min gidan Alhassan malami a jami"ar Buk Dake Zaune a Zooroad..! Da Dauri Sagir yace"Shi Baba! Baba Manu yace"Ai ta kwana Gidan Sauki..Ai nasam sa makotan Marigayi yaya nane Mahaifin Sagir kafin Allah yamai Rasuwa a saida gidan suka Dawo nan gadan kaya da Zama..in hakane ba mtsala Zan nemi abokina Alh.sadi sai muje ayi mganar kada kadamu kaji..! Imran yace"Shikenan kamar me dame ake Bukata..? Baba Manu yace"To zuwan Farko dai Kudin gaisuwa ne za"a kai sai su Minti da goro ko Dabino da Tarbarmu ko Cafet na kayan na gani ina so..In kuma zamu kara komawa bayan mun yi mgana dasu Waliyan yarinyar sun yanke Sadaki sai muje dashi da kayan Saka Rana! Imran yayi shuru kafin yace"in naso aje gabadaya Sau Daya fa...? Baba Manu yace"Shi Alhaji Alhassan don ya Bukaci Haka..?. Kai tsaye Imran yace"Ko bai bukata ba..Ni haka nake so ayi.Kuma hakan za"ayi yanzu Duka da komai da komai har Sdakin ita yarinyar nawa zasu isa..? Abun sai ya bama Baba Manu Dariya Confident din yaron Cikin Dariyan yace"Ni kuwa ina zan san Sadakinta ni ba Ubanta ba..? Sai dai muje da kudin In sun yanke na Hannunmu sun kai mu basu in kuma da kari sai mu Dawo Mu kawo Daga baya..! Imran ya Mike Lokaci Daya yana Fadin"Gobe in Allah ya kaimu zan kawo maka 200k..Zuwa Jibi nake so kuje gidan..! Baba Manu yace"Wannan ba mtsala bace..Sai dai an sanar da megidan muna tafe jibin..? Imran kai tsaye yace"Yarshi zata sanar dashi..Nagode..sai ka ganni.! Daga haka ya juya Cikin Takunsa na Sarssarfa ya Fice Daga Gidan Baba Manu da Sagir suka Rakashi da Ido kafin Sagir shima ya mike yana Fadin"Baba sai da Safe..! Baba manu ya Sauke ajiyar rai yana Fadin"ina ka sami wannan yaron..? Daga yanayinsa da mganarsa na gane akwai abunda yake Faruwa dashi koma ya Faru dashi Daya kara maidashi haka..? Sagir yace"A anguwar mu suke Baba.Sune wadanda suka siya gidan Marigayi Habibu Daya rasu kwanaki fa! Baba Manu yace"Au..Nan suke da Zama..! Sagir yace"Eh Baba..Nima haka na gansa har muka fara abota basu da kowa anan garin koma suna dashi ban taba gani ba basu Hulda da kowa daga su sai su kawai sai ni kuma da Allah ne kadai yasan Daliln Abotanmu..! Baba manu Dayaji Tsausayin su Imran ya kamashi yace"Allah Sarki Shi kuma Baban nasu Dayace bai da lafiya me ya same shi..? Kuma ina Mahaifiyarsu..? Sagir yace"Wlh nima Bansani ba Baba..Abbansu dai kullum yana Daki yana kwance likita ke zuwa gida yana Dubashi kuma agidan banta ba ganin wata mace ba Daga Imran din sai yayansa Yusuf wanda shine komai nasu sai Karamar kanwarsu Maimuna..! Baba manu na jinjina kai yace"Ikon Allah..! Zai sake mgana suka jin Hon din Imran da karfi da Sauri Sagir ya Duka yana Saka Takalminsa Lokaci Daya yana Fadin"bari naje Baba kada ya tafi ya Barni.Labarin yana da Tsawo zan Sake dawowa sai mu Tattauna..! Da toh kawai Baba Manu ya Bishi har ya Fice da gudu,Sai kuma ya Gyara zama yana Tunani da Nazarin Labarin da Sagir ya bashi game da Imran shidai yana ganin akwai wani abu mai Girma wanda yake cikin Zuciyar yaron kuma shike hanashi Sakin jiki Cikin mutane. Koda Sagir ya Fita Ran Imran ya gama Baci yana Hawa Mashin din ya Fizgeta sauran kadan Sagir din ya Fadi sai da ya Rike karfen Mashin din kana ya iya Zama Dakyau Cikin Tashin hankali Sagir yace"Yanzu daman Saboda ka yi sanadiyar da zan mutu ko na jikkata ka je har gidanmu ka Daukoni..? Imran ya saki Tsaki yana Fadin"Kamin shuru mallam..kafin na Sauya Shawara na Tsaya da Mashin din na Cikama baki da jini..! Sagir na jin haka yayi Shuru da bakinsa Domin yafi kowa sanin Zuciya irinta Imran bamai kyau bace Haka sukayi tafiyan ma wannan Karon Shiru har Imran din yakai Sagir din gida ko gama Sauka bai yi ba ya Figi mashin dinsa yayi Gaba Sagir ya Bisa da kallon kafin ya Girgiza kai kawai bai Shiga gida ba Shagonsa ya Shiga yana Duba agogon Hannunsa Tara ya wuce ya kamata su Rufe Shagon sai kuma gobe.