← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 190

Sashe 127

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Imran bai tashi daga wajen aiki ba sai 6pm,Da suka Fita lunch da karfe 1pm Sulaiman Ishaq ya hada karamin Taro inda ya gabatar da sabon Assistan Manger wato mataimakinsa a wannan Reshen bankin ya bada kadan Daga Cikin Tarihin Imran da yarda yazo yayi aiki a Branch din su na Lagos da irin kokarin da yayi Domin duk sanda Banki Zata je Seminar shi ake Turawa kuma zai je yayi kamar yadda ya kamata Cikin Shekaru da yayi yana aiki ya jawo ma Bankin Gt Daukaka da Cigaba sosai jin Dadin haka yake wannam Mtsayin ko ba"a Fada ba Daga ganin Imran bazai yi wasa ba Yanayinsa da Cikar Zatinsa kadai ya Isa Shaida kuma Daga ganinsa He is Ready abunda ake Fada akansa duka ba karya bane,Ya gaggaisa da ma"ikata mazan dake karkashinsa,mata kuma bai yarda yayi hannu da kowata Mace ba bai ma Saki Fuska ba Fuskarnsn dai gatanan ne kadahan kadahan.
Da aka tashi Kowa na shiga Tsararriyar Motarsa ammh Mataimakin Manager ya Hau Mashinsa bai ji Wani kunya ba ya Wuce gida Sulaiman Ishaq ya gansa yayi Wani Tunani acikin Ransa Kafin ya Shiga Motarsa ya Fice Daga Bulding din bank din.
Koda ya koma gida irin Murnan Da Abba da yusuf sukayi bazai misaltu ba,Dukkansu suka Rumgumeshi suna Murna Anty Safiya da Inteesar da Munari da Sagir suna gefe suna Tafi Lokaci Daya suna Fadin Congaratulation Dear.
Mamaki ya kamasa ganin party fa suka Shirya kwarya kwarya wannan kuma Shawaran Intee ne suna makaranta Tunanin ya Fado mata ta Gayama Munari itama tayi na"am Basu Dade a makaranta ba,lecture daya sukayi suka Dawo gida suka Fadama Anty Safiya ita kuma ta shige gaba ita ta Kira Yusuf ta tafadamai yce Tabbas wannan al"amarin ya Chanchanci ayi mai Party,Abba ma Dayaji bai hana ba,Inteesar ita ta Kira Sagir ta gayamai sunyi Girke girke da Lemuka Ya Yusuf kuma bayan ya tashi Daga wajen aiki ya biya Shoprite ya siyo Sweet ba adadi,Safiya kuma da Taimakon su Intee suka Hada Tsararran cake din Dake Dauke da CONGRATULATION IMRAN..!
Basu barsa ya shiga Dakinsa ba suka jasa Saman Dining inda suka Jera komai,Duk da bai saki Fuska sosai ba ammh kana kallonsa Zaka san yaji Dadi matuka Da Hannun Abba dana Yusuf ya hada ya yanka Cake din ya Gutsira ya bama Abba,Abba ya karba bai ci ba ya sakamai a baki Sai ga Taruwar Hawaye Imran yaji Rauninsa ya bayyana ya Rumgume Abba,Abba ya Rikesa cikin Farinciki yana Fadin"Congatulatiom My son..U Deserve everthing..Allah ya bada sa"a Allah yayi maka albarka..!
Su Anty Safiya nata amsawa da Ameen Ameen Yusuf ma ya Debo zai kai bakinsa sai ya rike hannunsa suka Hada Hannu suka kai bakin Yusuf atare kafin su dawo dashi bakin Imran Kafadansa Yusuf yadan Bubbuga yana Fadin"Bravo alaika...Allah yayi jagora dan kanina.!
Dakuna Fuska yayi yama kallon Abba yce"Abba Abeg tell him bafa wani Shekaru ya bani ba..!
Gabadaya Dariya aka saka kafin Sagir ya Yanko katon cake ya Dunfari bakin Imran baya yaja yana dan Fiddo ido waje bai gama mamaki ba Sagir ya Turamai abaki har wajen Hanci Da kumatunsa dama dama da cake Dariya aka sanya gabadaya ganin yadda ya wani Tattare Fuska kamar an yabamai Kashi.
Sagir yace"Congratulation Abokina..Allah ya tayaka riko am so Happy for u..!
Wata uwar Harara ya Wurgamai yana Fadin"Kaifa banza ne tsiyana Dakai kana Girma kana cin kasa..Ya kamata ka Rika gane bambamcin Boy and Man dis abunda kayi is a Childness..!
Yafada yana nuna Bakinsa cikin kyamkyama shifa bai son Abu ya Cika Zak'i shiyasa baya mu"alama da Chaculate sai Dariya su Abba kemai Munari da Safiya suka cemai Congaratilation ya amsa banda Inteeaar da kallo Daya yayi mata ya Kauda kai duk da tayimai kyau a ido Bai Hanashi nuna mata kwanjinsa ba Tayi Shigar bakar abaya ne sai tayi Rolling da karamin Vail fari Fuskarta ba kwalliya sai dai ta shafa ma karamin Bakinta Jan jan baki,Tayi kyau matuka a acikin Idanuwansa ammh bai bayyana mata ba,Dayake ana ta Murna ne ba wanda ya kula da bai amsa mata ba,ya sulale ya shige Dakinsa sukuma suka Cigaba da Shagalinsu Inteesar duk sai taji Gwiwanta yayi sanyi itafa ta Saki wannan Fushin nata Tuni Munari ce ta katse mata Tunani bayan ta Tura mata Cake a baki Har akan Hancinta Sai ta Bita itama ta gutsiro Cake din ta Bita dashi suka Fara guje gujen suna Dariya Abba na gefe yana kallonsu Cikin Jin Dadi da godiyar Allah.
Sagir dai Daki yabi Imran yaga ya shiga wanka sai da ya jirasa ya Fito ya Dinga mai hira yana amsa mai Sama sama Saukakkun kaya ya saka karamin Wando da Riga Fita Falo yayi yaga Inteesar da munari nata Hotuna Harda Anty Safiya baima bi ta kansu ba,ya fada Kitchen ya Dauko Ruwa ya Hado Tea a karamin Mug wajen Abba da Ya yusuf ya nufa suna zaune kan Dining din Sagir ma nan ya Fito ya samesa suka fara Hira ahankali yake bama su Abba Labarin yadda komai ya Fara Sanadin khalil ne Abba nata Godiya yana saka albarka nan yace ma Dr.Ali isa ya kirasa yana mai murna kila khalil ya fadamai..
Sun dade suna ta Hira sai chan Dare suka watse Sagir ranar anan ya kwana Tunda gidan ba kowa mama Tana Kaduna.
Kamar koda yaushe Imran kan kujera ya kwana ya bar ma Sagir gado,Sagir yasha mamakin ganin Imran na Busan Sigari Cikin mamaki yace"Tab kai yanzu daman baka Hakura da shan Taban nan ba..?
Ko kallonsa Imran bai yi ba,Ya cigaba da Busa Hayakinsa,kamar bazai ce komai ba Har Sagir din ya koma ya kwanta yaji Imran yace"Ka Dauka na Daina sha ne saboda na fara aiki..?
Bai ma Sagir damar mgana ba ya cigaba da Fadin"Ma'aikacin banki baya shan Sigari ne..?
Sagir yadan Saki Tsaki yana Fadin"Wlh dai in kaje kana Busawa achan bankin kasan Sauran..!
Dariya Imran yayi har ana jin Sautinta.
Washegari tun Safe ya amsa Kiran wayoyin mutane ba dama Daddy ne Farko har Umma sai da ya bamawa tayimai Murna Kimarsa ta kara Karuwa acikin Idanuwansa,Khalil ya kira sa sun Dade suna mgana Har Mahaifinsa Dr.Ali isa argungun ya Kirasa yayimai Murna Basheer dasu Sadam duk sun kirasa kuma an bada Sanarwan a Group din marigayi Alkali Dukku ammh Baffa Kabiru bai kira Ko Abba ba ballatana Imran wanda Lambarsa ya Zaga ko"ina acikin Dangi kalilan ne ya adana Lambarsu kamar Daddy da Su basheer.
Yaga Sakon Inteesar Daya kunna Wayarsa har da ma da Kiranta ammh bai bi ta kanta in ita Nata wasa ne shi da Gaske yske yi saboda aikinsa yasa baima da Lokacin wani banzan Tunani,da tagaji da kiransa ta Hakura ta Turamai sakon ban Hakuri har tagaji,Bai taba maida kai ba ya shareta ya nuna mata Shi Namiji ne kuma Har yanzu yana nan a Imran dinsa bai sauya ba

Ranar data Damesa Sai yaTura mata Sakon cewa
"Kin gama Fushin ne..?

Da sauri tace

"Eh nagaji na tuba nabi Allah na bika Ya imu..!

Mirmishi yayi kafin yace mata

"In kin Gama ni yanzi zan fara nawa..!

Aikuwa ya fara nashi Domin Dif ya Dauke mata ya Rataye ta bata ma ganinsa tun 7:30am na safe yake Fita sai 6pm na yamma yake dawowa in kuma ya dawo yana Daki yana aiki Tunda ya siya karamar Laptop Apple Saboda aiknsa kudin nan ne lokacin Bikin Yusuf da Baba Manu ya dawo mai Dasu,Yusuf bai karba ba ya cika ya siya Computer,Sannan Abba yasa Yusuf ya basa kudi ya siya kaya da Takalma tunda har lokacin Akwai kudi a Bankin Nura sannan akwai kudin da suka saida Motocinsu da su ya kara ya siya Suit masu yawa da Takalma da agoguna Saboda yanayin aikinsa.
Mganar aikin Imran har Daada sai da taji Daddy ya Kirata ya Fadamata Tayi ta Saka albarka,Da sukayi ma waya da Abba Tayi ta addu"a Imran din basu samu mgana ba Tunda baya barin Wayarsa a Bude sai ya dawo gida.
Sati Daya da Fara aikinsa Bankin Gt ta mallakamai Gida Mai 2bedroom madaidaicin Falt,da Sabuwar Motar hawa Kirar 4matics kyauta Halak malak,saboda Sadaukarwarsa da da jajircewarsa Sulaiman Ishaq ne ya shigar da Korafin a Chan Sama Board of Directors kuma sanin Waye Imran Abubakar malami yasa akayi approving din mganar aka kuma Tabbatar.

*Shakira*
3/22/22, 23:15 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�14*

*Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488*
Chapter 127 · 0% Book details