Sashe 47
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
 Yau din Takama Ranar Sati ne Wato Asabar ce Tun Safe Inteesar tatashi da ayyuka,Da wankin kananun Kayanta ta Fara Iners dinta da bata ba dasu Wanki,Daman Tun tana gida ta iya kowani aiki banda wankin kaya sai Dai tana wanke Inners Dinta Sauran kayanta kuma Wanki a ke kai musu Nataa da na Umma sai dai a dawo Dasu a goge tas dasu. Hakama Datazo Gidan Mama Tana Kowani aiki in Tana Gida banda Wanki,Itama Maman bada kanta Take Wankin nata ba kaiwa akeyi Sai da Inteesar din tazo ake Hadawa da kayanta Sagir ke kai musu Suma sai dai adawo dashi agoge. Tana yin girki Duk Ranar Datake Gida kamar asabar da Lahadi,In bata nan Tana makaranta sai Mama tayi. Yau ma hakan ce ta Faru bayan ta gama Wankin Kayan nata ta Share Daki ta gyara tayi mopping ta kuma Wanke Bayin Daki Da kuma na Waje ta Share Tsakar gidan ko"ina Tayi Tsaf, Da Mama tace ta bar Girkin ta Dora sai tace Maman ta barshi Ita Zatayi Shinkafa da Miya da wake ta Dafa musu,Da Salat Bayan ta gama tayi wankanta ta Saka Wata Doguwar Rigar atamfarta Gold mai kalan ja da Brown Anty Hauwa Matar Ya Basheer ta Dinkamata shi,Ta kashe Daurinta na Zara Buhari Fuakarta Tayi kyau Sosai Duk ita ba ma"abociya Kwalliya bace. Sallaya ta Shimfida ta Tada Sallar Azahar Daman Daga Tiolet ta Dauro alwala,Bayan ta Idar da Sallar ne taje Kitchen ta Dibo ma Mama Abinci Ta kawomata Zobon da Tayi Jiya da Daddare Bata Taba gwadawa ba Ko tana gida sai dai Tana ganin Talatuwa mai aikin Umma nayi Shine jiya Dataga Mama nada kayan Hadin Zobon Tace bari ta gwada sai gashi kuma Yayi Dadi,ammh Sai da Munari Tazo ta Taimakamata. Sannu da aiki Mama Tayi mata Tana Daga kan Darduma bayan ta Idar da Sallah Tana Lazimi. Inteesar ta amsa mata Cikin Jin Dadi Domin Tana bala"in jin dadin Zama da Mama Tana ganinta kamar Umma abaya ta Zata tafi Kowa Kewar Gida sai gashi Tana jin Dadin Zaman Gidan Mama,Sai dai kewa ta iyaye kuma gashi Suna mgana ta waya Kusan kullun sai sunyi Waya Daddy Fiye da Sau Uku Rana Umma ce ma sai Bayan an kwana Zata kirata taji ya Karatun ko Bata kirata ba Takan kira Maman su gaisa. Ganin Zata Koma Cikin Uwar Dakin ne yasa Mama ta Daga baki Tana Fadin"Inteesar ina zaki kuma..? Ke banga kin Debo abincin Kinci ba kuma kin gama Dafa Abinci da kanki..! Inteesar ta Juyo Tana Fadin"Mama ba yanzu Zanci ba sai anjuma..Dambun Namam da naci da Safe ya Cikamin Ciki..! Mama tace"Ina Dai Lura Dake baki san cin abinci sai kayan kwalama da Shan Zaki Shiyasa gaki nan Har yau bakya Kiba..! Dariya Inteesar Tayi kafin Tace"Kai Mama Allah ina ci..Rashin kibata kuma wlh ina jin Dadin kaina ahaka Sam bana son kiba..! Mama tace"ai shikenan nayi Shuru..! Yar Dariya Inteesar Tayi kafin Tace"Mama zan Dan kwanta In ya Sagir ya Shigo Abincinsa na Kitchen..!.da kai Mama ta amsa mata Tana cigaba da Laziminta ita kuma Inteesar ta Juya ta koma Ciki kan gadon Datake kwana ta yada kanta Lokaci Daya Ta Dauki Wayarta Ta kira Munari har Sau Biyu bata Dauka ba Lokaci ta Duba taga Har 1:30pm Tayi,Sai tayi mamaki Rashin Zuwan Munari alhalin sun Rabu ajiyan kan cewa yau Zata zo da Wuri suyi Karatu Tare suna Taimakon juna inda Daya bai gane ba in Daya ya gane sai ya Tada Dan"uwansa haka suke yi Duk Karshen Sati basa yarda su Zauna haka ko suce sai Test yazo ko Jarabawa Zasu Fara karatu a"a su Tuni suke Karatun Duka Course dinsu Saboda Karatun Shi suka sakama gaba ba Shirmen da wasu ke yi ba.. Har Barci ya kwasheta Munari bata Biyo Bayan kiran nata ba,Karfe 2:30pm ta Farka ta sake Duba Wayarta Ganin Ba Missedcall din Munari yasa ta Kara Kiranta Nan ma bata Daga sai Hankalinta ya tashi tasan ba Lafiya ko Bata kusa da wayar in tazo ta gani Zata kirata. Saukowa Tayi Daga kan gado Tana gyara Daurinta Daya Warware gabam Madubin Dake Dakin ta Tsaya taga Fuskarta ganin batayi komai ba yasa ta Bude Akwatinta ta Dauko Jan Mayafinta ta Yafa ajikinta Ta Nufi Wajen da tayi Domin Ma"ajiyar Takalmaanta,Ta Dauko wani Flat Shoe red Colour Shima ta Saka ta Dauki Wayarta ta Fito falo ta Samu Mama na Zaune ta gama cin Abinci Tana gyanyandi Cikin Dariya tace"Mama kina jin Barci basai ki Shiga Ciki ki kwanta ba..? Kina ta gyangyadi a azaune kamar yadda Inno take yi..? Mama ta Farka Cikin Muryan Barci Tace"Kaniyarki Innon Kike cewa Tana gyangyadi a zaune..! Inteesar na Dariya tace"Kai Mama keda Umma bakwa so kuji an Taba Inno..mallam Babba yafi ku ji da wannan yar Tsohuwar matar tasa..! Mama ta yunkura ta mike tana Fadin"Kinga Laifinsa..? Mutum da matarsa kuna sakamai ido..! Inteesar Tace"Tsofai Tsofai dasu Mama..! Mama ta harareta Tana Fadin"Bana son Shakiyanci Iyayen namu ne Tsofai Tsofai Ai Soyayya bata Tsufa sai dai Masoyan su Tsufa Ballatana Irin Soyayyarsu su na Mutan Da..! Inteesar Dariya kadai ta saka Kafin Tayi mgana Mama ta Rigata da cewa"Ina Zaki kuma..? Ni ina nan Zaune bayan na gama cin Abinci gyangyadi ya kwasheni ban sani ba..Asama sama nake jin mganarki..! Inteesar tace"ki shiga ki kwanta Mama ahakan ai sai Kanki ya Sage..! Mama tace"To bari na dan Mike Saman kujeran nan..! Inteesar tace"Yauwa ko kefa Mama..Bari in leka Munari Tace yau Zata zo muyi Karatu kuma najita Shuru,Na kirata bata Dauka ba.! Mama na ZAma kan kujera Tace"Eh Leka Ki gani ko Lafiya..in Lafiya take ai da yanzu ta Shigo Gidan nan..! Inteesar ta Duka Tana Kwashe Filet din da Mama taci Abinci ta Fice dasu Mama ta Bita da adawo Lafiya. Sai da ta Biya Kitchen ta ijiye abun Hannunta Nan taga Sagir bai ma ci Abincin ba kenan bai Shigo ba Shima Ficewa Tayi Daga Gidan Cikin Takun na Natsuwa Zuwa Gidansu Munari. Sun gaisa da Iro Megadi Kamar yaushe In tazo gidan kana ta Nufi Cikin Gidan Cikin Sanyinta Iska na kadata kamar Zata Fadi. Sallama Tayi Daga Kofar Babban Falon Gidan nasu Munari Abba Dake Zaune Shiyajita sai ya Amsa mata Duk da bai san ko wacece ba. Turo Kofar Tayi ta Shigo Lokaci Daya tana kara yin wata Sallamar. Wannan karon Harda Safiya Da Yusuf a masu amsa mata Tana daga gefe Wajen Dining Tana goge goge Abba na Zaune Kan Daya Daga Cikim kujerun Falon Center Table na gabansa Dauke da Ruwa da karamin Kofin Tangaran,Sai karamin Qur"anin Dake Hannunsa,an Dauke wuta Shiyasa yau babu karan Tv. Abba yana Sanye da Shadda mai Ruwan madara Riga da wando kansa ba Hula ammh Yana sanye da Farin glass dinsa. Imran ne agefensa kansa da Idanuwansa na Duke ne yana kallon Zanen cafet din Dake Falo,sanye yake da Vest Fara Wacce ta kama jikinsa Sosai Har ta bayyana Karfinsa Domin gabadaya Muscles dinsa sun Bayyana sai Wando Baki 3Quaters,Tun Shigar Da yayi da Safe ce yaje jogging,Karan Sigari ce a Hannunsa Tana kunne Hayakinta na Fita sai sai ba Sha yake ba Gabadaya kansa na kasa ne ba wanda ma ya Fahimci wani Hali yake Ciki,Sai yusuf Dake gefen Imran din Sanye da Jallabiya mai Ruwan Madara. Abba ne ke mai Fadan Shan Sigarin Dayake yi ganin,Tun Safe bai ci komai ba bayan ya Dawo Daga Jogging Dinsa suna Breakfast Safiya tayi mai Tayi yace ya koshi Da Rana Tayi Lonching ma bai ci ba ammh Yusuf ya Shiga Dakinsa ya Tarar sai Busa ma Cikinsa Hayaki yake yi Shine ya kawo kararsa Wajen Abba For d First Time ganin yanzu Abba Alhandulillahi ya Dawo Hayyacinsa. Jikinta a sanyaye kanta na kasa ta kariso Falon Tunda taga da Mutane afalon,Gaban Abba ta Zube kanta na kasa Tana gaishesa ya juyo yana Kallonta Cikin Fara"a yace"Daugther Kin Tashi Lafiya..? Inteesar ta amsa kanta na kasa Ta Gefen Idon ta Hango Yusuf Zaune da Sauri Tace"Ina yini ya Yusuf..? Ina Yini Anty Safiya? Tafada bayan ta Daga kanta sun Hada ido da Anty Safiyan Dake goge Saman Dining Din da wani karamin Towel. Shima Cikin Sakin Fuska ya amsa mata da Cewa"Lafiya Lau Inteesar Hala kin ji kawar taki Shuri kika Biyo Sawunta ko..? Kai ta gyada Lokaci Daya Hancinta na Shako mata Warin Sigari Tunda ta Shigo Yayi mata Maraba sai bata kawo hakan ba aranta tace bamai Shan Sigari agidansu Munari sai ta Lakanta hakan da Yadda bata son Warin Sigarin Shiyasa take jin kamar Tana Jin Warinta sai dai zuwa yanzu Data dan jima afalon ta Fara gasgatan Hancinta. Safiya ce Dagachan Tace"Ai kawar taki yau Tatashi Batajin Dadi Shiyasa Baki ganta ba..Ki tashi ki SHiga Tana Cikin Dakinta..! Da Sauri Inteesar ta Mike kamar Tana kan kaya Zuciyarta ce ta Fara Tashi Miyanta ya tsinke,Sai kawai ta Saka Gefen mayafinta ta Toshe Hancinta Daidai Lokacin Data kai Dubanta kan Inda Taga Hayakin Sigarin na Fita Zuwa Saman Fuskar ma mallakin Hannun Dake Rike da Sigari Bata ga Fuskarsa sosai ba ammh ta Cika da Mamakin ganinsa Domin bata Taba ganinsa ba Sai dai tasan Munari na Fadamata Bayan Ya yusuf Tana da Wani yayan kuma yarda ta Lura Tana Matukar Tsoronsa. Abba ne ya Lura da yadda take Toshe Hanci Cikin kulawa ya kalleta yana Fadin"Inteesar Lafiya kuwa..? Da Sauri Inteesar tace"Abba..Warin Sigari bana so..Yana samin Tashin Zuciya da Amai..! Adaidai Lokacin Dayaji Muryanta kamar Saukan aradu acikin kunnuwansa tun Shigowarta bai maida Hankali Wajenta ba Yana Fama da Dacin Ran Fadan da Abba kemai,Sai yanzu yaji mganarta Sai kuma ya gane Muryanta Da Sauri ya Dago Idanuwansa ya Sauke a nata Karaf wannan lokacin a karo na Biyu Suka kara Hada Idanuwansu Lokaci Daya kuma Zuciyoyinsu suka Kara Bugawa atare kamar wanchan Lokacin. Imran kara Girman Idanuwansa yayi yana kallonta Tabbas itace ammh miye kawota Gidansu? Mganar Abba ce ta katse mai Tunaninsa Inda yace"Yi Hakuri..Maza shige Wajen Munari..Yanzu nake mai Fadan yawan Shan Sigarin Dayake tana Illah ga Lafiya Ke gashi ma Warinta amai yake sakaki shi kuma Hayakin itace abincinsa..! Kamar Abba ya Watsamai Gwarwashin Wuta haka yaji mganar Abba aransa ya ayyana Dama Marinsa Abba yayi wlh Daya fiyemai