← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 190

Sashe 16

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Suna gabda da shiga garin Kanon Dabo Wayar Alhaji Mustpha Dukku Dake Hannun Inteesar ta Fara Neman dauki wayar ma ta Zame a hannunta saboda gajiyan Zaman Mota har barci ya kwasheta bata sani ba kiran wayar ya Tada ita Tayi Firgigit ta Farka Daidai Lokacin da Umma ke Fadin"Ke inte miko wayar Daddyn naki ana kiransa..!
Cikin Alamun barci cike a idanuwanta ta Dauki wayar ta Mikama Umma batare data ma kalli mai kiran ba Umma ta karba Tana kallonta tace"Tsiyana Dake Raguwa ce Inte..Daga kaduna zuwa kanon ne Duk kikayi Laushi haka..?.
Baki ta Zumbura wanda ya Zame mata jiki ta koma ta lafe Jikin kujeran Motan Tana Fadin"Allah Umma da Nisa sosai..!
Daddy yana jinsu hankalinshi na wajen Tuki yace"Sahala Daukan min kiran kada ya katse..!
Amsamai kiran Tayi tana Fadin"Barrister ne Mijin Asma"u..Baban Sajida..;
Tafada tana Mirmishi Tunawa da kirarin da Daddy yake ma yayan nashi duk sanda ya kira waya ko suka Hadu.
Gangarawa yayi gefen Titi yayi parking sanin mganar mai tsawo ce yace ya karbi wayar a Hannun Umma ya karata a kunni yana Fadin"Allah ya Taimaki Lauyan lauyoyi..Baban Sajida da Khamis Mijin Asma"u ma"u..!
Dagachan Bangaran Alhaji Kabir ya Murmusa yana Fadin"Mustapha Mijin Sahala..Baban Bashir..Kuma Gatan Mai sunan Daada Inteesar..!
Atare suka saki Dariya Harda Daada Dake zaune gefensa gaisawa sukayi kafin yace"Gani nan na kusa da Daada Tun dazu..Na samu na lallasheta Ammh kaima ka kara gata..!
Yafada yana mikamata ta karba Cikin Fara"a cike da ladabi ya gaisheta ta amsa yayi mata ya jiki tace"Kaifa nifa na warke ba wani abunda ke damuna..Tadin Asabe ne da baya karewa..!
Mirmishi yayi yana Fadin"Haba Daadanmu..Ai nasan ko baki da lafiya haka kike fadi..Don Allah Daaada ki kwantar da Hankali da yardan Allah Damuwarki ta kusa kwarewa Zamu dawo da Yaya Abun ki har gabanki Da yardan Allah..!
Daada tace"masha Allah..Allah ya baku iko..Allah yayi muku albarka..Ina ita Mai Dakin naka..? Ina Babban mijina Basiru..? Ko dayake ko jiya ya kirani mun gaisa harda matarsa ma ina mijin dashi sosai..Banda wannan Sangartattaciyar yar taka mai shigen sangarta da Lalaci..!
Mirmishi yayi ya juya yana kallon Inteesar data koma Barcinta yana Fadin"Kowa Lafiya Bashir yana kaduna shi na barma Harkokin namu yau..Ni da Sahala da Takwarki kuma Daada gamu mun kusa shiga kano Zamu kaita makaranta zata Fara karatun Jami"a da yardan Allah..!
Daada ta kyabe baki kafin tace"Uhm ai yanzu Kabiru ke fadamin nayi ta Fada Mustapha..Bani dai Salahan ita na gayamata kila tafi Fahimtata in kaine kan wannan Diyar taka bajina zakayi ba..
Yana Dariya ya mikama Umma wayar yana Fadin"Daada ce..!
Ko bai fada ba tasani Tunda suna Tare Da asuba sanda Baban Sajida ya kirasa yana Fadamasa Zencen kiran da Baba asabe tayi mai kuma bayan gama wayar tasu sun Dade suna Tattauna damuwar Daadan Dashi.
Karba Tayi Cikin Ladabi Tana gaida Daadan Da Tambayanta Jikinta Daada ta amsa ta Cigaba da Fadin"ke yanzu Salaha da saninki Mustapha zai Dauki Yarinyar nan zuwa wata uwa Duniya da sunan karatu..? Tana gaban ki ma baki iya Tankwarata ba,saboda Ubanta ya Daure mata Gindi Chan din da zaku kaita kusan dasu wa zata fara Mu"amala..? Bafa irin su Maryam ake kaiwa makaranta inda ba kwabar iyaye ba sai ta kara Sangarcewa yarinya ta isa aure ammh Sai wani Sakarci take ko yarinyar yar shekara Biyar albarka..!
Daada ta karishe Fada Cikin Fada Umma dai sai Dariya take kafin tace"Kema kya ce dai Daada..Kila ke yaji mganarki ya Daina Biyema Inte da sangantarta a kusan Koda yaushe ina gayamai aure zatayi watarana ya kamata ya Rage mata wasu abubuwan ammh daga ita har shi ba wanda ke Saurarata Daada..Mganar karatunta a kano kuwa abunda yasa na amince ba Cikin makaranta zata zauna ba Gidan Yaya Amina zata zauna Shiyasa..!
Daada tace"Yayar nan taki ta kano da Mijinta ya rasu Shekarun Baya ko..?
Umma tace"Eh ita Daada..Wajenta Zata zauna in ta samu Hutu sai ta rika dawowa kaduna Dayake ma Dan wajen Yaya Amina Sagir shima makarantar yake karatu zai rika kula da komai..'
Daada tace"To koda naji..Yanzu hankalina yafi kwanciya Allah ya Tsare ya bada sa"a..Ina ita yar Tselen uwar take ne..?
Umma tace"Gata nan tayi barci..Kinsanta Raguwa ce Daada..!
Daada tace"Nasanta kuwa..To ki ce mata nace ayi karatu banda Sakarci da Sangarta.
Umma na Dariya tace"To Daada..Allah ya kara girma..!
Daga haka ta mikama Daddy wayar ya amsa suka cigaba da mgana da Daada yana kara kwantar mata da Hankali kafin abama Kabir din su Cigaba da mgana Cikin Lokaci Sukayi sallama Kana Daddy ya Tada Motar suka cigaba da Tafiya Jefi Jefi suna Taba Hira duk akan Abunda ke Damin Daadan na Batan Dan"uwansu da iyalansa.

Karfe 11:34pm na Rana suka Shiga garin kano Daman Tun Daran Jiya Umma ta kira Yaya Amina ta sanar da ita gobe suna Tafe,To bayan Shigowarsu garin kano Daddy yayi waya da wani abokinsa Dake Lacture anan Buk din a Shashen Kimiya da Fasaha wato Computer Science Daman shi yayi ma Inteesar din Cuku Cukun samun Addmission din Shiyasa suna waya bayan sun Shigo yace su Fara shigowa cikin makarantar Inteesar din Ta fara Regisration din ganin Lokaci yana Tafiya har sun fara Karatu.
Shiyasa kawai suka Fara wucewa Cikin makarantar sai dai Umma ta kira Yaya Aminan ta Fadamata sai sun gama abubuwan daya kawosu zasu kariso nan ammh kwana zasu yi sai Gobe zasu koma ganin Rana tayi kuma ko gama abunda ya kawosun basu yi ba.

*Shakira..*
3/22/22, 23:03 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*DEDICATED TO:*
*Aisha alto(Sisinah)*
*Chubado muhammad(Uwar dakina)*
*Yahanasu Soupnass(Qawalli1)*
*Kausar salis(My jika)*
*Rahma Ladingo(Dota)*

   
  *🅿�7*
Chapter 16 · 0% Book details