← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 190

Sashe 46

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Washegari kamar yadda Inteesar Ta bukata Bayan Munari ta Shirya Gidansu Sagir ta Fara Biyawa Inda Allah ya Taimaketa Imran yana Gida bai Fito ba koda tazo Inteesar ta Shirya ita take jira basu Bata Lokaci ba Sukayi ma Mama sallama Suka Fito Ta bisu da addu"an Allah ya Tsare,Suna Fitowa suka Tsaya Bakin Shagon Sagir ya Fito suka gaisa Shi Kanshi ya godema Allah Imran baizo ba Kila da anyi wani karamin Shirin Film,500h ya basu suka ki karba yace sai dai in sin Raina Shiyasa Munari ta Karba Daganan basu Samu Abun Hawa ba sai da suka Taka da Kafarsu suna Hira Har bakin Titi kana suka Samu suka Hau zuwa Cikin makaranta,Koda sukaje ana Ta Shiga ajin Dole suka bi ayarin yan ajinsu suka Shige suma Domin yin Abunda ya kawosu.
Ranar ma Tare suka wuni,Basu Je Cafteria ba sai da sunje Shago sun Siya Lemo Inteesar tazo musu da Biskit da,Donut sukaci suka Koshi Suka Tsinke da Hira Ranar Munari ta Sha Labarin Daddy da Umma da ya Basheer Har gaisawa sukayi da Daddy Daya kira yaji Inteesar Cikin Fara"a yake Tambayanta tace Besty ta samu Tabana Munari suka gaisa yana ta Saka mata albarka Munari Taji muryan Daddyn Intee kamar na Abbanta Sai dai bata yima Inteesar din mgana ba Shi kuwa Daddy Daga Barayin Yasan Munari ta Musamman ne Tunda Har Daga Haduwa Suka Kulle da Juna yana Fatan Allah yasa kawancensu ya Zama alheri ga juna.
Ranar 4pm suka Tashi Daga makaranta Daganan gida suka Taho,Munari bata Sauka Daga gidan su Sagir ba,Saboda Tana Tsoron Haduwa da Imran illah kamar ta Sani yana Cikin Shagon Sagir,suka Rabu bayan Inteesar ta Karbi Wasu Note Hannun Munari Zata kwafe Tunda Gobe suna Gida bazasu Shiga makarantar ba.
Lokacin Data Sauka Imran da Sagir na Fuskantar Kofar Shagon Sagir kadai ya ganta Shima bai Dade da Dawowa Daga cikim makarantar ba,kanta na kasa ne Tunda Shago ne na Dinki akwai Dandalin Maza awajen Har ta Wuce batama Dago Kanta ba,Imran kansa na gefe yana kallon Wani Atamfa da yaron Sagir ke yankawa Shi bawai yana son koya bane No sai dai yana Kallom komai Dake Gudana a Shagon kuma yana Dauke sa acikin Kwakwalwarsa Batare da ya bama Abun Muhimmanci ba.

******

*After 10Days..*
Bayan kwana Goma da Haduwar Inteesar da Munari Sosai kawancensu Yayi nisa wanda yasa Kowa bai iya Boyema Daya Labarinsa,Har takai Abba da ya Yusuf da Safiya sun san Sunan Inteesar Besty Munari a bakinta Abba yaji Dadin jin Diyar kanwar Mama ce Mahaifiyar Sagir Hakama Ya yusuf,Shima bai Hanata ba jin na Gidane Tunda yanzu suna Kokarin Daidaita komai nasu ya Dawo kamar Baya ne.
Haka itama Inteesar din Daddy da Umma da Ya Basheer sun san da Zaman Munari Tunda In suka kira a makaranta indai suna Tare da Munari sai ta basu sun gaisa sun santa da Murya Sosai Harta da Nasara ma ta san Labarin Munari sun ma Taba gaisawa Watarana Datakira Inteesar din suna Tare da Munarin ta bata suka gaisa.
Inteesar ta Taba Zuwa Gidansu Munari sau Biyu bata Hadu da Ya Yusuf ba Imu kuma yana Dakinsa Shi a labarin ma bai sani ba Domin Munari bata yarda ta Furta Indai Labarin Zai kaimai ba.
Sai ta Hadu da Abba ita kanta Inteesar ganin Farko Datayi ma Abba sai da Tayi Shock Ta Dinga kallonsa Tana so Ta Tuna ina ta Taba ganinsa ta kasa Shekarun Dayawa Tana karama ne,Sannan kuma yanayin da Muryansa kamar ta Daddynta,Sai dai itama abun na Ranta bata iyama Furtama kowa ba,Sai ya Yusuf da suka Hadu Rana ta Biyu Data Dawo Shi kanshi Taso ta ganesa Domin da Girmanta Tataba Raka Daddynta Dukku suka Hadu dashi yazo Shida Marigayi Nura alokacin Sai dai kamaninsa ya bace mata Tunda ya Kara Girma aure yasa ya Zama wani Budede Sai kawai ta Watsar da Abun acikin Ranta ko Zencen batayi ma Munari ba.
Tana jin Dadin zuwa gidansu Munari Sabida Abba da Anty Safiya Suna da Matukar kirki Haka Abba zai ta janta da Hira yana musu Fadan su maida Hankali ga Karatu,ita kuma Anty Safiya ta jasu Shashenta suyi ta Hiransu,Ta maida kanta Sa"arsu Ranar ma da Inteesar din tazo Suna Shashen Anty Safiya sai gasu mommy sun zo ita da Anty Saratu da Tasleem Dama Tun jiya Mommy tace Safiya tasa Idonsu Dayake ta Dade ta Tura musu Kwatancen Gidan basu sha Wahalan gane Gidan ba Tunda ba yana Lungu bane.
A falo suka Fara ganin Abba yana Zaune yana kallo Suka Gaisa Dashi,Kafin Safiya ta Fito ganinsu Mommy yasa ta Murna ta Rumgumesu Cikin Farimciki nan take Fadama Abba Mamartace da yayarta da kanwarta suma ta gabatar musu da Uban Mijinta Suka kara gaisawa Sosai Abba ke ta Godiya sai da Mommy da Anty Sarati suka ji wani iri.
Sun zo Da kaya sosai a manya Ledoji Safiya tajasu Zuwa Shashenta sun ga abun mamaki kayan arziki haka,Ba ko sisinsu,Nan inteesar da Munari suka gaishesu Tasleem ma suka gaisa da Munari ta gabatar mata da Inteesar,Nan suka barsu suka Koma Dakin Munari suka Cigaba da Hiransu Daga Baya nan Tasleem din ta Dawo suka Hade su uku suna Shan Hira Tasleem na Fadin itama Buk Zata Cike Taje chan su Hade tare.
Safiya kuwa Ta Dinga ina zata saka da Iyayenta,Daman ta yi girki Dazu ita da Munari,Farar Shinkafa Miyar Kaza Sai Kunun aya da sukayi shi ta Zubo musu sukaci suka saka albarka suka Leka ko"ina suna yabawa Anty Saratu ta Kada baki tace"Ni kam ai banga aibun da Alhassan ke Fada akan wannan Gidan ba..Ga Baban Mijinta Dattijon yasan Karamci ji yadda yake mana Godiya mu da muka kawo musu ya ba komai ....Ji Abun arziki Mero..Ji Safiya tayi kiba kamar ba ita ba ai wannan gida..Tabbas Gidan Aure ne Wlh..Allah ya Zaunar Lariya..!
Hajiya Mero Tana ta Dariyan Farnciki,Sun zo mata da kayan Kitchen,da Turarun ka Daki Dana Jiki sai Speciess na girki da Garin kunu da Zogale Bushashiya,da su Kubewa,kuka Da Sauran abubuwa sai Kayan gyara,Da kayan gara irin su Mangyada da manja da Kwalayen Indome da Taliya da Macaroni suka Gyara Kitchen din suka Jera komai gwanin Sha"awa Basu Tafi ba sai yamma da Yusuf ya Dawo suka gaisa,Lokacin Inteesar tatafi Gida Tasleem da Munari suka Rakata Gida suka Dawo suna Dawowa Suka Tafi su kansu suna ta yima Yusuf Godiya Shi kuwa aransa yana Fadin ai Shi ke da Godiya Safiya ai Kamar Zinare ce a wajensa Bayan sun Tafi ta Nunamai kayan da suka kawo mata ya gani ya saka albarka har Abba ta Fadamawa Shi ma ya saka albarka
Sun Tafi sun barta Cikin Farinciki Suma sun koma Cikin Farinciki suna Yabon Irin Gidan da Safiya tayi aure aciki.

*Shakira.. *
3/22/22, 23:05 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

            *🅿�18*
Chapter 46 · 0% Book details