Sashe 5
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Yin wannan Tunanin yasa Jikinsa na rawa ya matsa kusa dasu Imran yana Fadin"Kaga ba sai an kai ga Haka ba..ku Turo mgabatanku Shikenan Tunda kun nace itama ta nace sai shi.."Yafada yanawani fiki Fiki da ido na marasa gaskiya Sagir Sai da Dariya ta kusa kamashi Imran kuwa Hannunsa ya Fizge Daga na Sagir ya Tura Hannu a aljihunsa ya Dauki kwalin Tabansa Har ya karar da ita Saura Daya ya Daukota ya Jefar da kwalin ya Jawo makunni ya kunnata ya Zuka ya Fesar da Hayaki kana ya kalli Alhaji Alhassan da Jajayen manyan Idanuwansa yace"Ka kira Yayana ka sanar dashi yanzu..NAN..! Ya karishe Fada Cikin Tsawa da Sauri Alhaji Alhassan yace"Yanzu kuwa..Insha Allahu.."Yafada yana rawan Baki Imran bai Saki Fuska ba ya Taka Hargaban Safiya bai Taba ganinta ba sai sau Daya da Yusuf ya taba nuna masa hotonta duk da bai wani kalleta ba sosai ba,da Jajayen idanuwansa ya kare mata kallo Daga sama Har kasa Tasleem kuwa bayanta ta Labe Tana Toshe Hanci Daya lura da ita tsawa ya Daka mata yana Fadin"Ke....'jiki na rawa ta Dago kanta tana kalleshi cikin Dakiya yace"Ni sa"an ki ne da kike ganina kina Tushe Hanci..? Maza Bude Hancinki kafin ki Tunzurani na Targaki yanzu agaban Iyayenki..!"Da Sauri Tasleem ta saki Hancinta Tana rawan Jiki ta kamkame Bayan Safiya Da kanta ke Duke Tana kuka Hajiya Mero kuwa gum Tayi da bakinta batayi mgana ba Duk da itama warin Tabae ta isheta sai dai ba Halin mgana ganin yanayin Imran din ya Firgitata ta tabbata ko ita ba Shakkarta zai yi ba balle ma Dataga Shi kanshi Alhaji ya Saduda
Safiya ya kallah kafin yace"Bhabi..Stop craying...Kin auri Yayana kin gama..See u sai mun Hadu a GIDANMU.."ya karishe Fada yana wani Mirmishi kafin ya Zuki Tabarsa ya Fesa musu Hayaki kana Lokaci Daya ya Juya yana wani taku Daya Bayan Daya yana wani Rangaji ya Fice Daga gidan Sagir ya maramai Baya Megadi ya Bisu da Allah ya Kiyaye sai da Alhaji Alhassan yaji tashin Mashin din Imran kana ya iya Motsi Juyawa yayi yana kallonsu Kafin ya Fara Bambamin kunya.
"Tsayuwar mu kuke yi kukama..? Ai sai ku shiga Cikin gida...Ke Safiya ki kira shi yaron kicemai ya Turo manyansa Tunda irin Gidan da kika Zaba kiyi Rayuwa kenan ke kika sani.."Daga haka ya Saba Zaman babbar Rigarsa ya nufi Motarsa Direbansa ya Budemai Bayan Bakar prado dinsa ya Shige yana jin Zufa na ketomai Kafin Direba ya Shiga Bangaran Direba yayi Rivers Ya yi Hon megadi ya wangale get suka Fice sai alokacin Safiya ta Juya Cikin gida da Gudu Tana Dariya da kuka Tasleem ta Mara mata Baya kana Hajiya Mero da Jikinta ya gama yin sanyi da al"amarin Data gani.
Imran kuwa Har ya maida Sagir bakin Shagonsa bai ce mai kanzil ba sai da ya ijiyesa kana Sagir ya kallesa yace"Mama Tana ta Cigiyarka.."Imran yayi Mirmishi kafin yace"Kace mata Zan shigo Gobe.."Daga haka ya Bama Mashin Dinsa wuta ya wuce ya bar Sagir da binsa da kallo har ya Bacema ganinsa bai koma Shagon ba ya Nufi Gidansu Dake Jikin Shagon nashi Domin ya Dauko wayarsa da Littafansa ya Shiga makaranta.
Yana Shigowa Falon ya ci karo da Yusuf sai washe baki yake Cikin Murna ya Sarke Hannayensa yana Fadin"Bro..Wai me kayi ne..?Yanzu Safiya ta kirani tace Abbanta yaje na Turo Manya..Am so Suprise Mutumin Daya gama Rantsuwan jiyanan bazai taba bani Auran yarsa ba sai gashi yau da kanshi yace na Turo manyana.."
Mirmishin Jin Dadi Imran ya saki ganin Dariya a Fuskarsa Dan"uwansa Hannunsa ya Zare kafin ya Dafa Kafadarsa yana Fadin"Imran kaifi Daya ne..Yana Cika Duk Abunda yace..So sai ka Fara Shirye Shirye ka kusa Zama ango akalla bayan Wasu Shekaru zamu samu wata mace zata karu acikin GIDANMU..!
Yana gama Fadin haka ya Sauke Hannunshi ya Wuce zuwa Dakinsa ya Shige ya Turo Kofa,Yusuf ya Bishi da kallon Kauna da Tsausayin Dan"uwansa kafin ya Girgiza kai yana Fadin"Kana Matukar Burgeni IMRAN ABUBAKAR MALAMI.."daga haka ya juya zuwa Dakin Abba Cikin Farinciki Domin ya sanar dashi Allah yayi zai yi aure wannan karan.
******
*KADUNA..*
_Area:Anguwan Sarki.._
Acikin anguwan Sarki acikin wani Tangamemen gida na Zamani Da misalin karfe 8pm na Dare wata yar Matashiyar Budurwa nagani wacce bata wuce Shekara 20 ba aduniya Doguwa ce sosai bata da Kiba Kirjinta kadai ne yake Tudu daga kasanta kuma ba wani abun kirki Sai Doguwar Fuskarta Kalar Fatarta baka ce ammh Ta samu Hutu da Jin Dadi,bata da Dogon Hanci Sai dai kana ganinta zaka Fahimci Ta Hada Jinsi da Fulani ko ta Uba ko ta Uwa tun bare ma yanayin Tsawonta da Idanuwanta Masu Dauke da gashin ido da kuma Gashinta Data Tufkeshi Har ya sauko Zuwa ga wuyanta.
Sanye Take da wata karamar Riga kamar Shimi Doguwa kanta ba Dankwali Sai Faman loda kaya take cikin wata Trolley bayan wadanda Tagama Durawa akwatuna Hudu gasunan a jere asaman Dan madaidaicin gadonta.
Har aka Bude Kofar aka Shigo Bata sani ba sai da taji Daga Bayanta ance"Auta wannan Uban kayan Duk na zuwa Kanon ne..?
Muryan wani Namiji ya Fadi hakan da Sauri ta waigo Tana kallonsa Shima kamar ita yake sai dai abun mamaki Shi Fari ne kuma ya Fita Dogon Hanci da Jikin Maza saboda yana da Dam Kiba ammh da tsawon da yanayin komai iri Dayane,Shekarunsa kuwa baza su wuce 30 aduniya ba
Zurawa Tayi da gudu zuwa gareshi ta Rumgumeshi Tana Fadin"Ya Bashir..Yaushe kazo..? Yana Mirmishi ya Shafa kanta yana Fadin"Autan Umma Kenan..Yanzu na Shigo nazo kawo su Abiden ne sun saka Rigiman wajen Umma yau zasu kwana.."Fuska Ta tabe kafin tace"Nifa ban gane musu bane..Suna so su kwacemin mtsayina wajen Umma da Da Daddy.."Yana Dariya yace"Wane su su kwace gwamnatin autan Umma da Daddy..Shalelen Ya Bashir da Anty Hauwa.."Tanajin wannan kirarin ta washe baki Tana Fadin"Shiyasa nake matukar sonka Ya Bashir..Zan yi kewarka in na tafi kano.."
Ta karishe Fada Kamar tayi kuka irin na Shagwabbun yara bai samu Zarafin mgana ba wata Mata Baka mai Fadin Fuska wacce sai da ta Shigo na Fahimci inda ta Dibo Bakin Fatarta da Hancinta irin nata ne sak,Sai dai ita bata da Tsawo a Shekaru bazata gaza 40 ba Tana Shigowa ta gansu ahaka ta Tabe baki Tana Fadin"Kana nan kana Biye Shiriritar INTEESAR KO.? tun Dazu nake mata mganar ta Rage wadanan kayan taki jin mganata Ta kwashe Rabin kayanta kamar Chaj zata koma Har Abada..!
Umma ta Fada Cikin kara Bayyana mamakinta Wacce aka kira da Intesar ta Fara Buga kafa na Shagwaba Tana Fadin"to ni Umma ba Karatu zan Tafi ba..Kuma ai ance yan Jami"a fa yan gayu ne sosai Dole nima naje da kayan gayuna kada wata ma ta Rainani.."Ya Bashir ya saka Dariya yana Fadin"Hakane fa Intin Umma..Gwara kije da Kayanki Jjc Student.."Ya karishe Fada yana Dariya jin Abunda yace ne yasa ta Nakwa nakwa kamar Zatayi kuka ta Kwashi Gudu Ta Fice Daga Dakin Tana Kukan Shagwabarta Tana Fadin"Sai na gayama Daddy..Kai da Umma kun hademin kai kuna min Dariya..!
Umma ta Tabe baki ta kalle Bashir Dake Dariya tace"Kabiya ta Kitchen ka Karbi Dambun Wajen Talatu katafin ma Hauwa"u dashi.."Cikin Ladabi yace"To Umma..Angode.."Batayi mgana ta Fice Daga Dakin Shima ya Rufa mata Baya Jin Daddy na Kiran sunansa Topa Auta ta kai Sunansa yau shi da Daddy sai Allah Dariya kawai yake kasa kasa Har ya Kariso Falon.
*Shakira...*
3/22/22, 23:02 - Ummi Tandama😇: *GIDANMU..*!
_(Our House)_
*Book1*
*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty*â¤ï¸
*DEDICATED TO:*
*Aisha alto(Sisinah)*
*Chubado muhammad(Uwar dakina)*
*Yahanasu Soupnass(Qawalli1)*
*Kausar salis(My jika)*
*Rahma Ladingo(Dota)*
*🅿�3*
"Da sallama ya Shigo Falon yana Danne Dariyansa ganin Inteesar dare Dare kan cinyar Daddy Tana ta Zubamai Shagwaba shi kuma yana ta Biye mata yana Lallashinta ga Abideen da Abida suna Tsaye gefe suna kallonta Daga duk alamu suna kan Jikin Daddy din ne tazo ta Turesu ta Haye Daman tace wajenta ne suke Neman su kwace mata.
*ALHAJI MUSTAPHA HAMISU DUKKU* ya Dago kyakyawan Farar Fuskarsa Tar da ita kamar ataba Jini ya Fito,Hancinsa Har baka yake kana masa kallon Farko zaka Shaida Tabbas Bafullace ne,Akallah Shekara bazai gaza Shekaru 58 aduniya ba Fararsa ta goge da jin Dadi da Hutu In ka kara kallonsa zaka Fahinci inda suka Dauko Tsawo da Doguwar Fuska Daga Bashir din Har Inteesar din sai dai Bashir Hasken Mahaifinsa ya Debo wanda Gashin kansa da Gemunsa suka Fara Zama Fari bakin gashin kadan ne Daga ganin sa yana da yalwar gargasa ajikinsa.
Cikin Muryansa ta Dattako ya kalli Bashir yana Fadin"Taho nan..Naji Meyasa kuka Tasa Autana agaba kuna mata Dariya kai da Mamarka..? Yafada yana dan Hade ransa ganin yadda Inti din ke kallonsa Bashir na kanne Dariyansa ya Zauna akasa Kusa da Kafar Daddy,Da gudu kuwa su Abiden suka Nufesa ya Daukesu ya aza kan jikinsa,Daga ganinsu yan Biyu ne saboda suna da Tsananin kama da juna Shekarasu bazai Wuce 3 aduniya ba yara ne kanana sai dai sun Debo Tsawon Babansu suna da Tsayi ba Laifi.