Sashe 117
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kallo,Kallon juna suke Daga karkashin zuciyarsu suna jin wani Salama da Farinciki Imran Har boyayyiyar ajiyar Zuciya ya sauke saboda ganinta kamar an ce mai an gafartamai Zunubansa sai da yana kallonta yaga ta Ramemai ta idaanuwansa itama Salama take ji da Farincikin ganinsa Idanuwanta suka cika da kwallar ganinsa sai dai itama taga yayi mata Rama acikin Idanuwanta Dukkansu sun Jigata matuka da Rashin ganin juna sai dai Raunin Intee yafi bayyana Imran kuma yana Kokarin Boye Rauninsa ne. Munari da kanta yagaji da Dukewa ta Dago ai sai ta ga an kure juna da kallon Soyayya sai ta Ware ido kawai ta na kallon Ikon Allah Dadi da Farimciki Lokaci Daya da matsanancin Tsausayinsu na Ratsata Har batasan ta shagala da kallonsu ba sai da taji Imran ya Daka mata Tsawa Domin ya ganta sanda ta kafe su da ido Da Sauri ta sadda kanta tana Kokarin Daidaita kanta Hade rai yayi saboda kada taga Fuskar Rainasa cikin bada Umarni da Dakiyarsa yace"Tsayuwar Uban me kike yi..?Bace min dagani kafin na Sauya Miki kammani Nonsess..,! Ai bai ma Rufe baki ba Munari ta bace da Sauri aranta Tana Fadin"basai takai ga Haka ba..! Kamar ta Kifa wajen shigewa Cikin Falon Har Inteesar da ta bita da kallo ta Kusa Dariya yana kallonta Tana Juyowa suka Hada ido Harara ya sakarmata yana wani Kara Dakuna Fuska Tasan Laifinta Narai narai tayi mai da ido kafin ta saka Duka Hannuwanta biyu,ta Rike kunnuwanta Dake Cikin Farin Hijabin Dake jikinta Cikin wata irin Sanyin Murya tace"Am sorry..Sorry..! Tafada Idanuwanta na cika da kwallah Fuskarta yake bi da kallo yanayinta na Ratsashi cikin Dan kauda kai yace"Ashe kinsan kinyi Laifi ko..? Haka kika Raina ni ko..? Saboda kin ga ban taba kwallo Dake ba ko..? Da Sauri ta Shagwabe Fuska Tana Fadin"To bana baka Hakuri ba..! Tafada Tana Turo bakinta gaba Sha"awa ta bashi ya Tsaya yana kallonta ji yayi kamar ya kama Bakinta yayi ta tsotsa Shawaran da zuciyarsa ke basa kenan ammh yayi Saurin kauda wannan Cikin dan Hade rai yace"Ni kike Turama baki..? Shagwaba ko...?shagwaban ki zai Dawo kuka yarinya..! Yafada kai Tsaye yana Tusa Duka Hannayensa Cikin Aljihun wandonsa yana More mata kallonta ji yake yana Cikin Farinciki gsshi ga Inteesar kamar bai taba jin kansa Cikin wannan Halin ba indai suna Tare sai yaji sa kamar yana yawo saman Gajimare saboda Farinciki. Jin Abunda yace yasa ta Rufe bakinta Tana yar Dariya kallonta kawai yake kamar ya kamata ya Rumgumeta haka yake jin wani yanayi yana Shigarsa Tuna abunda ke Cinsa araina neyasa ya Hade ransa kafin yace"Shine na Turo sako kika gani kika ki kulani ko..? Kuma na Kiraki baki Dauka ba Saboda kina chan kina Waya da wannan D'an iskan yaron ko..? Yafada yana bayyana Bacin Ransa Lokaci Daya yana kara Hade Girar sama data kasa Inteesar ta waro ido Lokaci Daya Tana Fadin"Yaushe..!? Hararanta yayi kafin yace"Ok nayi karya kenan ko..? Da Sauri tace"Ni ban ce ba..! Shima Cikin Saurin yace"U mean dat..! Inteesar ta marairai ce kafin tace"Allah ban gani ba Ya Imu da yaushe..? Nima ai ina ta kiraka baka Dauka ba nayi ta Tura maka sako Shiru na Damu har kuka nayi ta yi..! Tafada Cikin Damuwa Idanuwanta sun cika da kwallah Kasake yayi yana kallonta baya so yayi mgana baisan me zai ce mata ba yasa ya kalleta Cikin Idanuwanta kafin yace"Meyasa kikayi kuka..? kai Tsayen tace"Saboda kaki kulani ni kuma bansan Halin Dake ciki ba Shiyasa na Damu ina ta kuka..! Tsigar Jikinsa Sai da ta tashi Haka yarinyar ta Damu dashi bai sani ba Wayyo Allah shima Data san irin Wahalan Daya sha Saboda ita da batace haka ba. Kai ya Kauda kafin yace"Kada ki Sake kuka Saboda ni..kukan ki zai Hurting dina..! Kallonsa Takeyi kai Tsaye kamar yadda Shima yake Kallonta kamar an ce su Haddace kamannin juna. So yake yaji bada yaron nan take Waya ba yasa yace mata"Dawa kike ta waya Tun dazu..? Inteesar ta Dago wayarta Dake hsnnunta Kafin tace"Daddy ne fa ya Kirani muna ta mgana ya bama Umma mukayi ta mgana dani da Munari Har Umms tace na bama Mama sun Dade suna mgana ni ban ma san ka kira ba..! Tafada sai Lokacin data Bude wayar taga Misssed calls dinsa ido ta Zaro kafin yace"Ai kuwa gashi..Allah ban gani ba ya Imu ka yarda dani..,! Shi dai ya riga ya samu Salama Jin ba da shi take mgana ba Har sai da ya Sauke Numfashin Salama. Kallonsa Tayi lokaci Daya tana kallon Taban Data gani a kasa Cikin mamaki Tace"Miye wannan..? Tafada Tana nuna mai kasan yasan ko miye bai kallah ba ya Dauke kansa kafin yace"Meye..? Nima bansani ba..! Dariya ta kusa kama Inteesar har sai ta Murmusa Tana kallonsa Dakuna Fuska yayi kafin yace"Kina son Duka ne..? Dariyan nata sai da ta Fito da Sauri ta saka Gefen Hijabinta Tana Danne Dariyanta Hannunsa Daya ya Fito dashi Yana shafa kansa yana Mirmishi Cikin Dariyan kansa Inteesar ganin Fararan Hakoransa a waje ya Shagaltarta da ita tana ta kallonsa Tana auna irin kyan Imran He so nice. Ganin Taki Tsayawa da Dariyan ne yasa ya Tallabi kanta ahankali Cikin Nishadi yace"yarinyar nan kin Rainani ko..?kinga gadon barci na..! Yake Fada yana Kokarin Daidaita kansa. Kanta ta sosa tana yar Dariya kallonta yake Cikin Sha"awa kafin yace"Yana kiran ki..? Tsayawa tayi tana kallon cikin mamaki kafin tace"Waye shi din..? Yana Dakuna Fuska yace"Yaron nan mana..Wanda yace yana sonki..A Dukku..! Fara"arta ta Rage kafin tace"Yana kirana bana Dauka ko ya Turomin sako bana Dubawa..Tunda muka Dawo Daga Dukku yake Damuna..! Tafada cikin bayyana Jin Haushinta Ransa yayi fari jin bata kulasa Sai dai bai kamata ya sakankance ba Hannu ya mikamata yana Fadin"Muga lambarsa..! Batayi musu ba ta lalubo ta Daga Sama Saboda ya Kirata ma da Safe,Ta Haddaceta Duk da batayi Sarving ba Mikamai tayi ya karba wayar ya shiga ya Sakata Cikin Blook ya shiga bangaran Sakon nin yayi musu Delete all ya mikamata wayar yana Fadin"Ko kina son shi ne..? Karban Wayar ta tayi kafin tace"Ni bana son shi..! Tafada Tana Tura baki wani sanyi yaji acikin Ransa kafin ya kalleta yana Fadin"Gobe zamu tafi Lagos..! Ido ta sakarmai kafin tace"Lagos..?ku da suwa..? Imran yace"Ni da babanki da Abba da Ya Yusuf..,! Baki ta Washe kafin tace"Daddy zai zo nan..Eyeee..,! Tafada Tana bayyana Murnanta. Kallomta yake yi yana jin Farincikin ganinta haka cikin dan Hade rai yace"Kina Murna saboda zan tafi..! Bata rai tayi kafin tace"Ah"a nifa ina Murnan zan ga Daddy na ne ai kuma ba Dadewa zaku yi ba ko..? Kai ya gyada mata kafin yace"Jibi zamu dawo..,! Kai Tsaye yace"Chan zaka koma da aikin ka..? Yana kallomta yace"Wayace miki aiki zan koma..?Gidanmu dake chan zamu je mu gani..! Ajiyar Zuciya ta sauke kafin tace"Har naji Dadi..Bama so kayi nisa na Daina ganinka in ma zaka fara Aik plz Ya Imu ka yi shi anan garin kaji..! Kamar wani gaula haka ya gyada mata kai Dariya tayi kafin tace"Zamu dinga mgana ta waya in kun je ko..? Dauke kansa yayi kafin yace"A"ah..,! Bata rai tayi kafin tace"A"ah kuma..? Tafada Kamar Zatayi kuka Karo Farko Dataji Sautin Dariyansa yana Fadin"Shikenan zamu rika waya..Kada kimin kuka Shagwabbiya kawai..! Yafada yana kallonta da Dukkan Zuciyarta sai Lokacin ta saki Fuska Tana Buga Kafarta Tana Fadin"Kai Ya imu kaima zaka Biye ma Umma ne..Nice ma Shagwabbiyar..? Kallonta kawai yake yi bai yi mata mgana ba,Yanayinsa ne ke Sauyawa ganinta ahaka yasa ya kauda kai yana Fadin"Shiga gida..! Kai ta gyada mai kafin ta wuce Tana Waigensa,tana Dariya ta zata bai ga abunda tayi ba Sigarin nan Daya Wurgar ta saka kafa tatafi dashi Tana ja ya ganta yayi kamar bai ganta baa ya Kauda kai yana mirmishi Lokaci Daya yana shafa sumar kansa jinsa Cikin Farincikin da suka yi mai kaura Tun bayan Rasuwar su Anni sai da ya Hadu da Inteesar yake jinsa kamar ba shi ba. Koda ta shiga ciki Abba ne kadai afalo nan ta Zauna suka gaisa suka Shiga Hira anan ma shima ya gayamata zasu je kaduna gobezasu tafi Lagos tayi musi Fatan Sauka Lafiya da Dawowa Lafiya,kafin tatashi ta nufi kitchen inda Taji mganar Anty Safiya da Munari Tana Shigowa Munari ta Fara Dariya saboda ta ga Ya Inteesar din Zatayi ta Kalleta Tana Fadin"Allah yasa ba wani Laifi kikayi mai ba..? Ta fada Cikin Damuwa Inteear tace"Fada kawai yayimin..! Munari ta Kwashe da Dariya a Fili ta Furta su Fada manja Inteesar bata gane ba tana Dariya Anty Safiya ma bata gane komai ba sai itama Dariyan take ta Zata Shakiyancin Munari ne. Tare suka kama Girkin sai gabda mangriba suka gama kana suka shiga Domin yin wanka da Sallah. Bayan sun idar ne Inteesae tace Munari tatashi ta Rakata Gidan Mommy ta Dauko mganinta na Ciwom mara Data zo dashi Daga Gida Jin maranta ta dan Fara mata Ciwo kadan kadan,Munari ta sako Hijabi suka Fito a Falo suka bar Abba da Ya Yusuf shima sai da yayi musu Fadan Fita duhu ya Shiga Jin Mgani zasu Dauko yasa yace suyi sauri ko kuma su Tsaya wajen Maman su kwana. Sum sum suka Fice suna zuwa Haraban gidan zasu Fita suka kusa Cin karo da Imu ya dawo Daga masallaci ba Wutan Nepa sai dai Wata ta Raba gari Tar. Lokacin da suka Fahimci shine Sai da jikinsu ya Dau rawa kallonsu yake Cikin mamaki kafin yace"Ina zaku yanzu da Daddaran nan..? Yafada yana kallonsu Cikin Dakiyarsa Cikin In ina Munari tace"Gidan..Ma...ma zamu je..! Inteesar dai batayi mgana ba sai Morema kallonsa take yi yana Lura da ita sai dai bai bata Damar ma ta Fahimci ya ganta ba. Hade rai yayi kafin yace"Yanzu da Daddaran nan..? Yafada yana kara Duba agogon Fatan Dake daure a tsitsiyan Hannunsa. Kafin ya Cigaba da Fadin"Ammh baku da Hankali ko..? In akace ku Fita iyanzu sai ku fita..? Munari kanta na kasa tace"inteesar ce zata Dauko mganinta..! Tafada tana Zungurin Intee datayi mgana ita kuma taki cewa komai. Kallonta yake cikin Mamaki yace"Mgani bata da lafiya ne..? Da Sauri Munari ta gyadamai kai Inteesar din yake kallo ita kuma taki yarda su Hada ido cikin Dakiyarsa yace"Oya ku koma gida in dai kunsan ba Chan zaku