Sashe 134
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Inteesar da Munari suna baje a Falo a kan Cafet din Daya yi ma Falon kwanya Littafansu suka baje suna karatu Saboda test din da zasu fara Ranar Monday da farko Hirar su suke sha Da Anty Safiya bama su fara karatun ba sai da Imran yace mata Taje tayi karatu kana ta mtsama Munari ta Dauko musu Littafan suka Fara Hankalinsu ya tafi kan abunda ke gabansu bama su ji kiran Wayar Inteesar da Daddy ke yi ba sai da ta katse ya sake kira kana Munari taji ta Dauko Wayar tana Fadin"Besty kinga Daddy nata kira bamu ji ba..! Inteesar na Duke da Biro a Hannunta Tana Rubutu cikin wani karamin Littafi kai Tsaye tace"Dauka Sakata a Speaker! Ba musu munari ta Daga Kiran ta sakata a amsa kuwwa ta ijiyeta anan Tsakiyarsu dukkansu suka Hada baki Wajen gaida Daddy bayan yayi Sallama. Daddy ya amsa cikin Sauri yana kallon Daada Data kafesa da ido Cikin Gyara Zama da mgana mai muhimmanci Daddy yace"Intee kina jina Dakyau..? Cikin Mirmishi tace"Yes My Hero Dad !Tafada cikin barkwancin da suka Saba Daddy bai biye mata ba yace"Tambayarki zan yi kuma ina so ki Fadamin gaskiya kin ji Intee..! Daga ita Har Munari sai da suka Dakata da Abunda suke yi suna sauraran Daddy Intee cikin Wani yanayi Lokaci Daya gabanta na Faduwa tace"Insha Allahu Daddy..! Kai Tsaye yace mata"Daada ce ta Umarceni da bama Dan"uwanki Imran auranki..Ammh na Tambayeki ko kin Amince da hakan..? Daga ita Har Munari ido suka Fiddo Waje Cikin mamakin kalaman Daddy Intee Sai taji kamar bataji da kyau ba Tana Kifta ido kamar yana gabanta Tace"Daddy me kace...? Wani Dan"uwan nawa..? Ya imu..? Tafada cikin rawan baki Lokaci Daya Tana kallon Munari Data Washe baki Tsantsan Farinciki ya Cika mata Zuciya na ganin wannan Ranar Intee da Ya Imu as a couple Boyayyiyar Soyayya Zata bayyana kanta don Ubanta ko taki ko ta so. Inteesar kuwa yanayin Datake ciki Allah ne kadai zai iya Fassara yanayin Sai kuma Ma"abota soyayya yayinda sukaji Labarin mallakan Abun da suke so Zuciyarta ta cika da Haske Farincikin da bata Taba Zato ba ko Tsammani Ya Imu fa shi zai zama Mijinta kai Daada ta Biyasheta Mijinta fa Ya imu..? Gabadaya bata son idanuwanta ya cika da kwallah ba sai da suka Zubo Munari ta zungureta alamun Tayi mgana Daddy naji,Domin kowa yayi Shuru Daga chan bangaran ana jiran amaar Inteesar Daada kuwa bata Damu ba Tana da kyakyawan yakinin ba Macen data kai Macen da Zataki Imranu karyanta shi kuwa Imu sai da aka Kirata ya samu Faduwar gaba To yanzu in tace bata son sa fa? Sai Daada ta aura ma Khamis ita Tuni yaji Duhu ya mamayemai ganinsa Wata Zuciyar tace ka manta Sagir yace Tana sonka,Kuma in bata sonka meyasa take Fushi Dakai saboda kace zakaje Wajen Sajida? Daddy ne dayaji Shurun yayi yawa yayi gyaran Murya shima acikin Ransa yana da Full Confident Intee Tana Ra"ayin Imran kodaga yadda Take yawan yin Zencensa Lokaci Bayan Lokaci Umma ma addu"a take acikin Ranta Allah yasa Inteesar ta amsa Domin wannan Hanyar ne kadai Zasu maidama Mami Asma"u martani Sannan ita ai tayi ma Intee sha"awar Yaron Tsayayyen Namiji dazai iya Rike gidansa a kowani Hali Sannan ta Hango Dacewarsu Tun ba yau ba kowa sai addu"an ta amsa yake yi barim ma Yaya Yusuf Sagir dai yasan Komai ma zai tafi kamar yadda yake Fata Inna Bintalo ne kadai Ranta a Hade Tunda yar Fadan Mami Asma"u ce wacce Ke Zaune kawai kamar kankara ya Daskarar da ita Sajida na gefenta Tana Rafzan kuka Khamis kuma kansa na kasa Idanuwansa sun yi jajir ya rasa ma a wata Duniya yake. Munari nata Zungurin Intee tayi mgana Taki yi tama kasa cewa komai kunya da Farimciki sun Lullubeta Dadday yace"Inteesar ke fa muke jira da Abunda kika ce zamu yi amfani..,! Inteesar ta kasa mgana kunya take ji Munari na ganin haka tayi Zaraf tace"Daddy bazata iya mgana ba Wai tana jin kunya gatanan Tana ta Rufe ido Tana Dariya Wlh tana son shi Daddy shima fa Ya Imu yana sonta soyayyar munafunci suke yi ba wanda yasani suna waya kuma su yi ta turama juna Messages na kalaman soyayya I miss u ina son ganinka don Allah Daddy iz not a Love? Daddy da Dariyan Farinciki dana kalaman Munari suka sakasa ya amsa da cewa"Na love Daugther...! Gabadaya su Sadam sai da suka Dara Imu mamaki ya cikashi Lalle yarinyar ta Rainasa wato munari ta na nan Tana Lura da duka Motsinsa Tana Sakamai ido har cewa ma take suna Munafunci ko Lalle jikinta na mata kyaikyayi ne kuma shi kowa sai yace Yana sonta shi yaushe yace yana wani Sonta? Intee Dagachan bangaran ta fizge wayar Daga Hannun Munari ta kashe Tana Hararanta Lokaci Daya Tana Fadin"Munafuka..! Munari na Dariyan Farinciki ta Mike Tana Rawa Lokaci Daya ta na Bude shokki tana Fadin"Intee Amarya oga Imu da kansa kai Ranar akwai shagali! Hararanta Inteesar ta karayi Tana mamakin yadda tasan suna waya da Ya imu Munari tayi Dariya kafin tace"Uhm ai na Dade da gane komai yarinya..Kuna son juna ammh ku kan ku baku sani ba..yanzu ai sai ku bayyana ma juna Tunda zaku zama ma"aurata ni bari naje na Fadama Anty Safiya ta fara shi ZAmu sallama ya Imu kowa ya Huta..! Da gudu ta kwasa zuwa Shashen Anty Safiya Tana kwalamata Kira Daga jin yadda take mgana Zaka hango Tsantsan Farinciki a tare da ita ta bar Intee zaune ta kasa tashi Jikinta yayi mata wani sanyi In ta tuna Imran kadai sai Tsigar jikinta ya tashi Wata Xuciyar tace me ya faru a Dukku da Daada tayi wannan Tunanin? Ko dai Ya Imun ne yace yana sona..?kai Ya Imu bazai ce ba Tunda nima bai Taba Fadamin ba keman gaskiyan Munari ne muna son juna This is a Love bamu sani ba..? Wata zuciyar tace mata to ya aureki ya makomarsa shi da Sajida..!? Tuni taji komai ya Tsaya mata Farincikinta ya gushe Allah na gani Tana matukar Kishin Sajida ko Sunanta ta Tuna amtsayin Matar Imran sai taji kamar ta saka kuka. Achan Dukku kuwa Wayar na katsewa Daddy ya Dago yana kallon Daada kafin ma ya samu Zarafin mgana ta rigasa da cewa"Me muke son ji..? Ta bakinta ai mun ji komai Daga bakin mai sunan Autana..Sannan ita amsar mace Daman Shuru ne Mganar suna son juna Gaskiya ne Domin nima na Dade da ganin Alamun haka.! Tafada Tana kallon Imran daya Dakuna Fuska aransa yana fadin"Lalle nema Daadan nan to Datake kallo na dawa take? Falon yayi shuru Daada ta cigaba da mgana"Mustapha ku fara shiri..Malami baka ce komai ba..?kuma bana son naji kayi ma Imran Fadan abunda yayi duk da ba bamai kyau bane ammh Allah ya Hallata Saki kuma yayi shi a gabar Daya dace gabar da muka samu Masalaha..! Abba kansa na kasa yace"Shikenan Daada mu masu bin Umarninki ne Da dukkan Abunda kikace..Allah yasa mu Kulla alheri..! Yafada yana kauda kai Daga kallon da Baffa Kabiru ke binsa dashi kunya yake ji Wlh Imran ya basa kunya sosai da abunda ya aikata ammh bashi da ta cewa Daada ta mara mai baya. Daada ta gyara zama Tana Fadin"Yau fa nake son a Daura auran nan ga ya"yanku nan zasu Taya ku shirya komai kuma bana son bata Lokaci nan da Wata Daya nake son ayi Taron Tarewarta Ayi komai a gama cikin Lokaci..! Daddy ne ya karkace Kansa yace"Daada sai naga ko abar Daurin auran zuwa gobe ne..! Kinga yamma Tayi kuma ko Goro da dabino bamu siya ba da zaki mana lamini zuwa gobe da safe karfe Tara na safe sai a Daura auran zuwa 10 ko 11am na safe kowa ya Dauki Hanyar inda ya fito ko ya kukace.? Yafada yana kallon su Abba da Baffa Kabiru wanda yake kallonsu kawai a bai ce ba,Inna Maimunatu tace"Eh hakan yayi Daidai daada..kiyi Hakurin Goben sai a Daura da yau kuma da goben duk Daya ne a wajen Allah..! Daada ta jinjina kai Tana Fadin"Shikenan...Kai Kabiru..? Tajuya bangaransa Dago kansa yayi yana Fadin"Na"am Daada..! Daada tayi Mirmishin su na manya kafin tace"Naji tunda muka fara wannan zaman bakace komai ba..? Kai zaka biya ma Danka Imranu Sadaki ko..? Tafada Tana tsareshi da ido Cikin Rauni da wani Takaichi ma yake kallon Daada Bai samu ma Zarafin mgana ba Mami Asma"u ta Mike da karfi kamar wata mahaukaciya Sabon kamu,Shock din Daya Riketa sai alokacin ya Saketa ta kara Tabbatar ma kanta Daada ta gama Tozarta ta Imran ya gama Tozarta yarta ya gama Wulakantata Saki..?ko Tareewa batayi ba auran da ko wata Daya bai cika ba Shine za"a yi ma yarta wannan Sakin Tozarcin da wulakancin. Daada ta kallah Ido na cikin ido tafara Fadin"Wlh ba"a isa ba..Ba wanda ya isa..Ni Asma"u aka shirya a Tozarta..Asaki ya'ta ko wata batayi da aure ba sakin Tozarci da wulakanci Sannnan agaban idon mu Daada kike cewa Baban Sajida ya sake biyama Wanchan mara Mutumcin yaron Sadaki..? Kai mustapha harda kai Ashe haka zaka ma Dan"uwanka ko Daada tace zata aurama yaron chan Yarka saboda Baban Sajida bazaka hanata ba? Kai kuma Malami Daman au nasani D'anka ai ya gagareka Duk Abunda yaga Dama shi yake yi ba kuma wanda ya isa yace don me to Wlh bazata sabu ba Bazan yarda akan Wannan al"amarin sai na shigar da ku kara akotu Wlh sai an bima ya'ta Hakkinta..! Ta Karishe Fada Rauninta na Bayyana sai kuma ta fashe da kuka Tana kara Fadin"Wlh bazan yarda ba..Wlh bazan yarda ba..! Take Fada Tana kuka har Gilashinta na Fadi kasa bata sani ba. Daddy ya dago yana kallonta Cikin mamaki yace"wazaki kai kotu..Asmaa'u.? Mami Asma"u ido na cikin ido take kallon Daddy da Jajayen idanuwanta Tace"Daada zan kai kara Kotu..Sai kuma wannan Tsagerin yaron.Duk Abunda ya Faru saboda ita ne Tsohuwa mai sonta kanta kawai ai ba Malami da Mustpaha kika Haifa ba Harda Baban Sajida meyasa baki nuna adalaci a kansa..? Kin cika som kai kuma baki da adal.! "ASMA"U.......!! Bata karisa ba Baffa Kabiru ya Dakatar da ita da karfin amon Murya yana Tsaye ne Ransa na Tafasa da abunda ya Faru da kuma kalaman da Ma"u