Sashe 52
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Karishe da Fadin"Daddy wai kaji fa Mama..Dan iskan zan aura mai Shan Sigari gashi Daddy Mahaukaci ne Wlh Duka fa wai yake har sai ya Sumar ni Wlh yanzu ma Tsoron Zuwa Gidansu Munari nake Daddy..! Daddy na Dariya yace"Intee Daddynta..Ki daina Cemai Dan iska kin ji ko..?ko bakomai Ai Yayan Kawarki ce kinga ai yayanki ne kuma ba kyau Raina na gaba dakai ki Daina Saboda in ita Munarin taji kina cewa haka bazata ji Dadi kina Zagin Yayanta kamar yadda kema Bazaki ji Dadin azagar miki Yaya Basheer din ki ba..! Inteesar ta Tura baki Kamar Yana ganinta Tace"Allah ya Tsare Ya Basheer dina ba D'an isk..! Umma Dake Tsaye gefen Daddy Tana Hadamai Tea a Saman Dining yake Zaune Tashin su kenan zasu yi Breakfasat ya Kira Yar Lelen tasa Wayar Tana Handfree ne Umma Tana jin komai ita ta Katse Inteesar bata karisa ba Tace"Inteesar meyasa bakya jin mgana ne..? Ana miki Fada kina kara Sakarci..Ki kiyayi kanki fa Kina cemai D'An iska Tsaranki ne..Kince Yayan kawarki ce..Kuma kince Abokin Sagir ne Shine zaki Zauna kina Kiransan Dan iska mara Mutumci..? Haka muka Koya miki kiyi ma na gaba Dake..? Ta Karishe Fada Cikin Bacin rai Daddy bai ce komai ba Sanin gaskiya ne gwara arika Gyarama Inteesar din in Tayi wani abu. Sai dai kallonta yayi yana Fadin"Salaha ki mata a Hankali don Allah..! Ko kallonsa Batayi ba ta Cigaba da Fadin"Ki Daina wannan Sakarcin ke ba yarinya bace yanzu..Ina so ki Sani kada mu rika Zargin mutane in bamu san komai akansu ba kada mu yanke musu Hukunci..! Inteesar da Jikinta yayi sanyi Karo na Farko tace"Bazan Kara ba Umma..Kiyi Hakuri..! Jin haka yasa Umma ta Sasaauta Tana Fadin"Yauwa ko kefa Yar Umma da Mamanta..Daga yau in kika gansa ki Rika gaishesa kin ji ko..? Duk wanda ya Girmeka yayanka ne Balle ma Yayan Kawarkice munari kikace..! Inteesar ta Tura baki Tana Fadin"ni fa Umma tsoro nake ji kada ya Dakeni..kin jifa Munari tace yana Duka Har yana fa Sumar da Mutum..! Ba Umma ba Harda Daddy sai da yayi Dariya Cikin Dariyan ne Daddy ke Fadin"Bazai miki komai ba..Daga gaisheshi sai duka..? Kada ki Damu kin ji Intee Daddy kedai ki Zama mai Ladabi da Natsuwa a Duk inda kika je..! Inteesar tace"Insha Allahu Umma..! Umma Tayi mirmishi Tana kallon Daddy tace"Allah yayi miki albarka ya Karatun..? Ina maman taki..!? Inteesar tace"Alhamdulillah Umma..Mama kuma Tana Lafiya Tana Tsakar gida..! Umma tace"Badai aiki take yi ba kina kwance.? Da Sauri tace"A"a Wlh Nagama Duka ayyukan tana dai Zaune ne Tana Shan Hantsi suna Hira da Ya Sagir..! Umma ta kadai kai Tana Fadin"Naji Dadin haka Allah ya bada Sa"an karatu Sai a kula Sosai kin ji ko..? Inteesar tace"To Umma..Bama Daddyna Wayar..! Daddy Dake gefe yace"Gani nan Inteen Daddynta..! Inteesar Tayi Dariya kafin Tace"Daddy ina ya Basheer ya manta Dani kwana Biyu ko..? Daddy tace"Injiwa..? Aiki ne yayi masa yawa ammh Zaki jisa da kuma Rashin Lafiyar Matarsa...Su Abiden ma Jiya suka koma suna nan Tare Damu.." Inteesar tace"Wayyo Har yanzu Jikin nata..? Allah ya bata Lafiya Daddy wai Ciki ne da ita..!? Umma Dake Turama Daddy Mug Din Tea gabansa ta Rike baki Daddy na Rike Dariyansa yace"Eh haka akace waya gayamiki..!? Inteesar tace"Ya Basheer ya gayamin..! Umma tayi karaf tace"bana son Shiga mganar manya Intee..! Daddy shima ya karbe yana Fadin"To itadin me kika maida ita..? My Intee is Not a Small Bby kamar yadda kike Tunani..! Umma tace"Yau kuma..? Ka manta kai ke Fadamin Kullum Intee yarinya ce..! Daddy yace"Eh ina nan akan bakana Sai dai ba yarinyar da kike Tunani ba..She know wht she is Doing..! Baki Umma ta tabe tace"Allah ya kyauta..! Lokaci Daya jan Daya Daga Cikin kujerun Dinng din Dake kusa da Daddy ta zauna ,Inteesar Dake Jinsu a Waya aranta ta Murmusa tana Fadin Daddy bazai Saki ba ita kuma Umma bazata Daina Jayayyaba. Cigaba da mgana sukayi da Daddy gabda Zasu yanke kiran Take Taambaysaa Daada ya jikinta..? Daddy yace"Ta samu Sauki Sosai Last Week naje na Kara Dubata..! Inteesar Tace"Allah ya kara Lafiya..Ka gaisheta Daddy..! Yace"Zataji ki kirata Da kanki mana..Tana Tambayanki indai naje Dukku..! Inteesar tace"bani da lambarta a wannan Wayar ka Turomin Daddy..! Cikin jin Dadi yace"Ok zan Turo miki..Bye zamu Breakfast ne sai Zuwa anjuma zan kiraki..! Inteesar ta Shagwabe Tana Fadin"Wait Daddy..Yaushe zaka zo..! ? Tunda kuka kawoni Almost 4 to 5 weeka ba wanda ya kara Zuwa ya Dubani..? Daddy yace"Sorry My Angle..Rashin Lafiyan Daada yasa baki ganni ba..Ammh ki saka Ganina Next week in ban samu Zuwa ba Basheer zai zo in kuma Munzo Tare shikenan..Akwai wasu Karafan da Zamu zo mu siya anan kanon..! Tsalle Intee ta Daka Kafin tace"Plz Come Daddy Don Allah..! Cikin Farinciki yace"Insha Allahu.." Daga haka suka yanke kiran Bayan sunyi Sallama Umma na Jinsu Tana ta Kurban Tea dinta Lokaci Daya tana Hadawa da Soyayyan Dankali da Kwai Kala batace ba Shima suna gama Wayar ya Fara karyawa Cikinsu ba wanda ya kara mgana Har sai da suka Kamallah. Inteesar na gama Wayar ta Fita Tsakar Gida Tana Gayama Mama Mganar zuwan su Daddy Mama na kan kujera yar Tsugunno ta Fadada Fara"arta Tana Fadin"Kai masha Allah..Allah ya kaimu Allah ya kawosu Lafiya..! Intee ta amsa da Ameen Tana Fadin"Mama ya Sagir ya Fita ne..? Mama tace"Eh yanzu ya Fita Kamar an Kirasa a waya ne..! Kai ta kada mata Kafin ta Koma Cikin Dakin. Ba Dadewa sai ga Munari Tazo Dauke da Tarin littafai nan Waje ta Fara Tsaayawa suka Fara gaisawa da Mama kafin ta karisa Ciki,Rumgume juna sukayi da Inteesar suna Murna kafin su Zube kan gado suna Dariya Abun na Ran Inteeaar Cikin Zolaya tace"Besty ya kika kare da wannan yayan naki..?yama sunansa..? Munari tace"Au yau kuma Sunansa kike Tambaya..? Ai da D"aniska mara Mutumci kike kiransa..! Inteesar sai taji kunya Cikin Sanyin Murya tace"am sorry Besty..Nasan ban kyauta ban kara kiransa da wadanan sunayen Gayamin sunansa Allah dashi zan Rika kiransa..! Munari tace"Imran muna kiransa Ya Imu..! Da Sauri Inteesar tace"Yauwa Ya IMRANN..ya kuka yi Dashi..?na dawo gida ina ta Tunanin ko Kila jiyan ya Sumar Dake da duka..!ta Karishe Faada Tana Dariya Duka Munari ta Dakamata Abaya Tana Fadin"Muguwa ba Mutuwa bace kin manta ne ba Suma da kika gudu kika barni SAi yanzu ne zaki Tuna dani..! Inteesar na Dariya tace"To sai na Tsaya..? Wlh ban tsayawa Gudu ya Zama Dole Besty nidai gayamin Allah yasa bai Dake ki ba..? Munari Tace"Baimin komai ba Wlh..Sai yace na Wuce Cikin gida kafin yayi Kwallo Dani..! Atare suka saka Dariya Har da Tafawa nan suka Cigaba da Hiransu Munari na kara bata Wasu Labaran Halin Imran Inteesar taji ai yama Wuce yadda Take Tunaninsa A Tsegaranci Shi lamba Dayane. Ba su Fara karatun ba sai da Inteesar ta Zubo musi Dambun Nama ta Dauko musu Lemo suna Ci suna Korawa da Lemu suna Karatu ganin haka yasa Mama tace suyi Karatunta ita Zat Dafa abincin Ranar. Haka kuwa akayi mama Tayi musu Danwake da mai da yaji da salad,Sukaci sosai Harda Santi Munari tace"Ya Imu nasan Danwake sosai ammh in nayi agida sai yace ban iya ba..Mama tafi ni iyawa..! Mama na gefe tace"Ai yanzu ma Sagir yazo ya Daukan musu suna Shago zasu ci..Ni kaina Saboda shi nake yawnn yin Danwaken..Kuna Cikin Daki Dazu ya Shigo muka gaisa yake Cemin Mama ina Danwake kwana Biyu..? Shine nace yasha Kuruminsa yau Saboda shi Zan yi Danwaken..! Munari ta Zaro ido Tana Fadin"Ammh baisan muna nan ba ko mama..? Mama tace'A"a ina ma ya wani Damu da ku..Bai ma san kuna nan ba inaga..! Ajiyar zuciya Munari ta Sauke Inteesar na mata Dariya Sanda ta Fito Gida Bata gansa ba Abba Kadai Tayi ma Sallama Anty Safiya ma da Ya yusuf suna Shashensu basu Fito ba. Munari na Tare da Inteesar har yammah,Kana Tayi Shirin Tafiya Inteesar ta Sako Dogon Hijabinta Maroon wanda Anty Hauwa ta Dinkamata Mai Hannu sai Fuskarta Tayi kyau sosai. Munari tayi Sallama Da Mama Suka Fito Tare da Inteesar Bayan ta Diban mata Dambun Nama dasu Cake da Donot,Dambun naman ya kare Cake din na Sauran kadan Dayake ba ita Kadai take ci ba,Mama bata cika ci ba ita da Sagir ne sai Munari Da takan Diba su tafi Dashi makaranta. Koda suka Fito basu ga kowa akofar Gidan ba,Suna Daga Chan Cikin Shago su kuma suka yi gaba zuwa Hanyar Gidansu Munarin Har gida Inteesar ta Raka Munari ta Shiga suka gaisa da Abba munari ta Nunamai Abunda Intee ta bata yana ta Godiya da Saka albarka Wanda Inteesar ke jin Dadin hakam Har ga Allah in ta gansa sai Taji kamar Tana Tare da Daddynta ne Tana ganin a mgana da wasu abubuwan suna mata kamanceceniya da Juna sai dai shi Abba yafi kama da Alkali Hamisu ne su kuma su Daddy sun Dauko Fuskar Daada ne. shashen Anty Safiya suka Shiga intee ta gaisheta tadan Zauna a Shashen Antyn Safiya suna Hira kafin ta Fito Munari ta Rakota Har Bakin get Taci Sa'a Imran baya Gida.