← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 190

Sashe 7

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai da sukaji Tashin Motarsa kana Daddy ya juyo yana kallon Umma yana Fadin"Meyasa koda yaushe kike maimaita mgana Dayane Salaha..? So nawa zan gayamiki ki Daina Ganin abubuwan da Inti ke yi a wani abu kar ki manta fa yarinya ce fa In ta girma Zaki ga Duk ta Daina wadanan abubuwan kuma kada Ki manta Sai da Bashir ya Shekara Goma sha Biyu aduniya muka Sameta alokacin da muka Fidda rai da samunta ita kadai ce Mace awajenmu menene Laifin in mun bata kulawa da gata..? Ai hakan bai Hanata zama mai Tarbiya da ilimi ba ina alfahari da ita da kananun Shekarunta ta Sauke qur'ani yanzu kan Haddatanta take,Kuma kina gani Da kuruciyata gashi Zata shiga Jami"a Alhamdulillah bata Taba Jawo mana mgana ba Salaha ni banga abun Damuwa ba.."
Ya karishe Fada yana kure ta da ido,Umma ta Sauke Numfashi Tana Fadin"Uhm..Alhaji kenan wai kana Bani mamaki in kace Inti yarinyace..? Wacce ta Haura Shekara ashirin ce yarinya Alhaji..?
Cikin Halin ko inkula yace mata"To in ba yarinya bace Babba ce..? Shekara ashirib Duka Duka nawa take..? Don Allah ki Daina wannan mganar..In bamu kula da yayanmu ba..Ai samun mu ya zama na banza sai mu Daina Fita Neman Salaha..!
Sanin bazai Taba Fahimtarta ba yasa ta bar mganar ta Mike Dauke da Abida Tana Fadin"Bari na kai Abida Daki tayi Barci.."Daddy yace"Ga Abidin ma yayi barci ajikina.."Batayi mgana ba ta wuce Ciki Dakinta ta kai Abida ta kwantar kan gadonta kana ta Dawo ta Dauki Abeedin Shi ma takaishi ta kwantar ta Rufa musu bargo ta Rage musu Sanyin Ac ta kuma Rage Hasken Dakin kana ta Rufo musu kofa ta Fito Ta samu Daddy zaune in da Ta barshi ya maida Hankalinsa kan Talabijin yana kallon Labarai Kitchen ta wuce ta samu Talatu na Goge goge Sannu da aiki Tayi mata kai tsaye Fulas din Dake Kan Cabinet din kitchen din ta Nufa ta Dauki karamin mug ta Tsiyayo Ruwan lipton din Dayaji kayan Itatuwa da Ganyen Na"a Na"a ta Fice dashi Zuwa Falo Tana Zuwa Taja Center Table din Dake Tsakiyar falon ta ijiye Tana Fadin"Alhaji ga Ruwan Lipton din nan..!
Dago kansa yayi yana Fadin"Yauwa Nagode..'Daukowa tayi ta mikamai ya karba ya Fara Kurba sau Biyu yayi ya Dauko yana kallonta yace"Wata anguwa Su Yaya Aminan suka koma ne Bayan Tashin su Daga zoo road..?
Umma tace"Gadan kaya suka koma..Gidan Marigayi din da Sagir din yagada Ta koma Ciki suna zaune.."Daddy ya gyada kai yana Kurban Tea din yace"Sai nake ganin kamar Nauyi zamu kara mata Salaha..!
Umma ta kalleshi a kaikace tace"Wani irin Nauyi kuma..? Sai da ya kara Kurban Tea din yana Fadin"Kai mata Inti da zamu yi ta zauna wajenta Tayi karatu..Ga Wahalan Rayuwa ga Kuma Rigiman Diyar taki..! Umma Tayi Mirmishi Tana Fadin"Wlh ko Daya Alhaji..Bakaji da na kirata na gayamata Intisar ta samu addmission anan BUK ba..Kafin na Furta mata ina son Inti ta zauna wajenta sai dai ta rika zuwa Tana Dawo in anyi Hutu sai Tazo mana nan tayi mana Hutu ita ta Fara Cemin ammh wajena Zata zauna ki..? Kasanta da son Diya mace kuma Allah bai Bata ba Danta kenan kwara Daya Sagir..Bayan mutuwar Mahaifinsa kuma tace bata Sha'awar kara aure ba yadda su Baba Bala basu yi da ita ba tace baxata kara aure ba Shiyasa taki Dawowa ta Fara sana"arta achan tana kula da Danta har gashi yana Karatu shima kuma yana Sana"ar dole suka sakamata ido.!.
Daddy ya jinjina kai alamun gamsuwa yana Fadin"Hakan ma yayi. tunda wani Lokacin sai kiga karayin auran ma wani abu ne Dabam..Badai shi yaron Dangin Mahaifin nashi na waiwayansa ba..?
Umma tace"Eh suna iya bakin kokarinsu..Ai kanin Babbansa Daya Wani Manu..Ko Yaya Aminan wh suna mata kokari..Ita Dayake bamai jira bace macece mai neman na kanta Ko Daga nan gida zaka ga ba kasafai take kira Tanemi wani abu ba.."Daddy yace"Allah sarki..Rabona da kano Tun Rasuwar Mahaifin yaron nata.."Umma tace"Sai gashi Dalilin yarka zai kai ka ko.? Yana Dariya yace"Zaki fara ko..! Kin san bana samun Zama ne..Allah ma ya Taimakeni Bashir yanzu yana kula da komai.."Umma tace"Gaskiya fa..!
Daddy ya mika mata Mug din yana Fadin"Naji Dadi da Inti Tana da inda Zata zauna..Dama bana son zaman Hostel sam kinsanta Tana da Tsiwa kuma bata saba Zama cikin mutane ba..Uwa uba da kuma D'an wajen nata ko bakomai zai rika Taimakata awasu abubuwan Tunda Bashir ma yace shima nan yake Karatun nashi.."Umma tace"Eh Haka Yayan tacemin..Ya kusa gamawa tace shi.."Daddy ya Mike yana Mika yace"Shikenan dai..Zuwa gobe ki kamalla mata komai jibi zamu tafi insha Allahu.."Umma ta mike Itama Tana Fadin"Allah ya kaimu..Miya ce zan mata..Dambun namanta na Soya mata..Sai su Snaks Datace Tana so nayi ma kawata Mgana Gobe za"a kawo.."Hanyar Dakinsa ya Nufa yana Fadin"Ina jiranki aciki.."Hanyar Kitchen ta Nufa Dauke da Mug din Tana Fadin"Gani nan Tafe..Baban Inteesar.."Yana jinta yayi Mirmishi ya Shige Cikin Bedroom din Dayake mallakinsa,Umma Data fito Daga kitchen din Kashe Tibin Tayi Kafin ta Rufamasa Baya.

*******

Yusuf ne ke Tallafe da Abba yana Bashi Tea abaki Munari  na Gefensa Tana mikamai Buredi mai yanka yanka yana Bama Abba Imran na Tsaye Daga Jikin Wardrope din Dake Dakin Abba yana Sanye da Farar Singelet da Wani Bakin wando 3quater,Hannunsa sanye Duka Cikin aljihun wandonsa Allah ya Taimaka yau ba"a Busa abun Ransa ya Hade Tamau kamar bai Taba Dariya ba yanayin yadda yake Tsayen kiris yaje jira atabashi ya Fashe.

Har Yusuf yagama Bama Abba Tea din ya bashi mgangunansa yana kokarin maidashi ya kwanta Imu Dake Tsaye yace"Ka barsa ma Ruwan zafi yabi Jikin nashi.."Yafada Cikin muryansa mai Cike da Amo da zati.
.bai yi gaddama ba Munari ta sakamai Karamin Filo a bayansa suka Jinginshi ya Dago yana kallonsu yana Fadin"Allah yayi muku albarka.."Yusuf yayi Mirmishi ya amsa da Ameen Abba Allah ya baka Lafiya Dukkansu suka amsa da Ameen kafin Yuauf ya Zarce da Fadin"Na Fara Tunanin ko mu Sauya ma Abba Likita ne..?
Imran Dake Duke da kansa yace"Saboda Mene..? Yusuf yace"Bana ganin wani Cigaba..Kullum Abba jiya iyau..Kamar ma Baya yafi akan yanzu.."
Imran ya shafa Gashin kansa Dayayi Uban Dada yace"Ai ba Laifin Likitan bane.."Yusuf ya Kalleshi yana Fadin"Kake gani..? Imran yace"Kaima ka sani ko..?
Yafada yana kallon Maimuna Dake kallonsa Cikin Hararanta yace"ke Lafiya kike kallona kamar Wata mayyah..? Da sauri ta kauda kanta karamin Tsaki yaja yana Fadin"Tashi ki Fita ma..Kinsan bana son yawan kallo ko..? Kwalkwal Tayi da ido kamar Zatayi kuka Zaburo mata yayi yana Fadin"Au bazaki tashi ba kin tsayane kina neman min kuka.? Fice anan kafin ki Tunzurani na Miki Dameji da Fuska.."Da Sauri tatashi Ta Fice Dauke da Mug din da Abba yasha Taa da Bread din.
Yusuf ya kalleshi yana Fadin"Wai waya bata maka rai ne..Kazo ka sauke kan Munari.?
Bai samu Zarafin mgana ba sukaji Muryan Abba yana Fadin"Kabi ahankali IMRAN...'Yafada ahankali Cikin Sanyin Murya duk sai Jikin Imran din yayi sanyi Kawai sai ya gyada kai yana Fadin'"Mubar Abba ya samu barci..Muje Dakina muyi mgana achan..!
Daga Haka ya Fice yana Takunsa na Daya Bayan Daya.
Sai da Yusuf ya ggyarama Abba kwanciya kana ya Baro Dakin Gidan Shuru kamar ko Yaushe Munari yassn ta kwanta Tunda Imu yayi mata jan ido.
Dakin Imran din ya Shiga Cikin mamakinsa ya samesa yana Busa abar tashi Girgiza kai yayi yana Fadin"Wai kai baka gajiya da Busa Hayaki ne..? Kada ta maka illah Fa Imran..!
Cikin Lumahe ido yace"Me yayi saura..? Ai ni Daman Tuni Illah ta gama illatani Hayakin Saura ya samu!
Jin haka yasa Jikin Yusuf yayi sanyi kawai sai ya zauna Gefensa yana Fadin"Hakane..Ammh akallah muyi kokarin ganin mu Rayu Cikin Farinciki ko Saboda Abba.."
Har ya Fidda rai da zai bashi amsa sai yaji yace"Ya mganar Tura mgabatanka gidansu yarinyar nan..?
Yusuf ya sauke ajiyar rai yana Fadin"Nima bansan ya za"ayi ba..Kuma Mahaifin nata niyake Sauraro.."
Imran ya Busar Tabarsa yace"Wazaka Tura..? Yusuf ya kalleshi yace"Bansani ba..Ammh nafara Tunanin kiran gida na Sanar dasu inda muke da kuma abunda ke Faruwa akallah koda bamu koma wajensu ba zasu zo sukaga inda muke kuma Duniya Zata shaida bamu kadai bane AGIDANMU  muma muna da Ahali.."
Chapter 7 · 0% Book details