Sashe 31
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
iya Zama Dashi.. Nifa aganina..Shifa bai Damu ba..Da ya Imu yayi aure mace ta Rainasa Ya kuma zama akwai wacce yake kula da ita bayan kansa gwara ya To ya Mutu bai yi auran ba bari ma Kiji na gayamiki..! Safiya ta Zaro ido tace'Bala"i..! Me Munari Zatayi ba Dariya ba sai itama Safiyan tabiye mata suka yi Dariya Sosai Har da Tafawa Hira Tayi Dadi. Safiya tace"Nidai bani Dan satan amsan yadda Zan zauna dashi..Kada watarana nayi mai Ba daidai ba ya Chanxamin kamani..!suka saka Dariya atare kafin Munari tace"Bazai Dake ba..Ai Baya Duka sai Ransa ya baci..Ko ni bai taba Dukana ba yasha Dai Fadan zai Dakenin a baki,Sai da mari ko tokari..kawai ki kiyaye baya son yawan gaisuwa,Baya son Hayaniya bayason ana Bugamai Kofar Daki ko kwana yayi bai Fito ba Kada wanda ya Nemeshi,Bai cika Cin Abinci ba yafi shan Fruit sai abu na Karshe Yana Shan Sigari kuma yana bata Muhimmaci..sannan koda baka son Warinta indai yana wajem Dole kayi Hakuri ka Shaketa ya tsani ka Toshemai Hanci Saboda gani yake Kamar shi kake kyama in kika Kiyaye wannan Babu wani abunda Zai Hadaku kila sai kuyi Sati Baku Hadu ba..Shi bamai Sakewa da mutane bane Yafi jin Dadin Rayuwarsa Shi kadai ko afalon nan baya Zama a koda yaushe in bai Fita ba yana Dakinsa ne..! Safiya ta jinjina kai kafin tace"Ai indai Wannan ne zan kiyayemai kada Watarana yace Min Safiya Kin rainani ko..? Gabadayansu suka Saka Dariya Suka Tafa jikake Tass..Har sai da kaji karan hannuwansu in ka kallesu alokacin kamar sun Shekara da sanin juna. Safiya ce tace batayi Sallah mangariba ba jin ana kiran Sallar Isha"i Ita kuma Munari tace Tayi mangariba Saura Isha"i su tashi suyi Sallah kafin Ya Yusuf ya Dawo. Nan suka Mike Safiya ta Fara Shiga Tayi alwala itama Munari Ta Shiga Tiolet din Yusuf tayi Alwala Dayake ita ke gyaran Dakin koda yaushe ba inda bata sani a ba adakin. Tare sukayi Sallar adakin Safiya tayi mangariban ta Ta Dora da Isha"i Ita kuma Munari Tayi Sallar Isha"i din da batayi ba,bayan sun idar suka Dasa kuma wata Sabuwar Hira Zuciyoyinsu ta Cika da Farinciki ita Munari ta Murnan Zuwan Safiya a Rayuwarsu Farincikin da suka rasa zai Dawo ta kuma Samu abokiyar Hira ita kuma Safiya Tana Murnan Ta samu kanwa Bayan Tasleem,Bazata yi kewa mai yawa ba,kuma nasan Ta Tabbata bazatayi nadaman Auran Yusuf ba. Suna tsaka da Hiran nasu Daidai Lokacin Yusuf ya Turo kofar ya Shigo da Sallama da Ledoji Guda Hudu a hannunsa na Tambarin kamfanin Gidan Abinci. Yadda ya gansu sai da yaji Zuciyarsa Tayi sanyi,Suna ganinsa suka Mike Ita Safiya Tana gyara Zaman mayafin kanta Ita kuma munari baki ta washe Tana fadin"Sannu da zuwa Ya yusuf..! Lokaci Daya tana karisa garesa da Niyarvkarban Kayan Hannunsa. Bakinsa Shima a washe ya amsa mata Lokaci daya yana kallon safiya yace"Babe kina samu akun Abba ko..? Nasan munari tayi keeping dinki Company..Nasan kanwata akwai son Hira..! Safiya kanta na Kasa ta Murmusa Tana wasa Da Gefen Mayafinta tace"Yes She so so Nice..I love her..! Munari najin Haka ta saka Tsalle Tana Dariya Shima Yusuf din sai da ya Dara Lokaci Daya yana Fadin"Ke kullum baki san kin girma ba Lilsis..? Above 20 fa..Kuma kina Yar jami"a Nan da Shekaru uku masu zuwa u are Going to become a Graduated in Ecocomics..! Sai ta Daina Tsallan Ta koma ta Natsu Tana Fadin"Wlh kuma hakane Yaya..Na bari..Yanzu ai am Mature ko..? Tafada Tana nuna masa kanta Dagashi Har Safiya sai da suka Dara Ledan Dake hannunsa Guda Uku ya mikama Munari Dayan kuma ya ijiyeta nan kasa sai dai ta karba yace mata"Ur Dinner..! Munari ta karba Tana Fadin"Allah yasa Fride rice ce Ya yusuf..! Yana Dariya yace"Mayar Fride Rice itace..Ki Dauki Dayan Ledan Is Urs..Daya kuma na Abba ne ki Tabbatar kin Bashi yaci yasha Mgani ya kwanta..Dayan kuma is for ur Brother Imran..! Munari tayi Narai Narai da ido Tace"Is He at Home..? Yusuf yace"Check his Room..! Munari ta Kara narke fuska Tana Fadin"Kasan He warning me kan Bugamai Room dinsa ko Ya yusuf..? In ba so kake ya Sauyamin dis My Beatifull Face ba is ok sai naje..! Yusuf ya kada kai yana Mirmishi yace"Shikenan ki aijiye Cikin Frigde din Kitchen if He Wanta Zai Shiga ya Dauka..Daman Choice dinsa ne Kayan Lambu! Munari tace"Tanque Ya yusuf..Sai da Safe..Anty Safiya see u Tomorrow..! Tafada tana Daga mata Hannu itama Safiyan Dagamata Hannu Tayi Tana Fadin"Ok see u Lilsis..! Daga haka ta Sa kai zata Fice yusuf ya Kirata ta waigo yace mata"U make Sure kin kwanta da Wuri..No Chart no Reading ko..? Kai ta gyadamai Tana Fadin"I promise u bazan yi ko Daya Daga ciki ba sai Barci..Basai kazo Dubani ba Ka zauna ka kula da Anty Safiya Dakyau asha Amarci Lafiya..! Tana Gama Fadar haka ta Fice da Gudu ta Rufo Musu kofar suka Bita da Dariya dukkansu. Sai alokacin Yusuf ya juyo zuwa ga Safiya ya Fara takawa Zuwa gabanta Idanuwansa kyam a kanta Ita kuma gabanta na Fadi kanta na kasa. Sai da ya iso gabanta bata Tsammaci Haka ba taji ya Rumgumeta Kamkame kamar wani Zai kwaceta sai kuma Taji ya saki kuka Cikij kukan yake Fadin"Tanque so Much Babe..Kin yimin Abunda Har na koma ga Allah bazan manta ba..Allah ya bani ikon Rike ki Cikin Aminci da kauna kamar yadda kika Nunamin..! Sai kuma ya kara Sakin mata kuka Tuni Taji ta Rude itama bata san Sadda Ta Saka hannu ta Rumgumeshi ba ta Saki nata kukan Tana Fadin"Basai kamin Godiya ba..Ka Chanchanta My Dear..Kaunarka gareni ce ta Sanya ka ganni Tsaye acikin Dakin nan a kuma Cikin Gidanku nidai Fatana ka Rike da Amana My Dear Ka soni Sosai Fiye da yadda nake sonki..! Yusuf na jan Majina yake Fadin"I do..Wlh I do..! Haka kurum yake Fada Kamkame Juna Sukayi kowannensu na kukan Fitar da Abunda ke Cikin Ransu Har sai da suka gaji suka koma suna Lallashin Juna gefen gado ya jata ya Zaunar da ita kan Jikinsa yana Fadin"Babe don Allah kiyi alfarman bazaki gayyatomin kowa Daga Barayinki ba Nan kusa Har sai na gama Gyara Miki Bangaranki na Saka miki komai na kuma yi miki kayan Lefen da kowani Namiji ke yi ma wacce yake matukar so ya ganta Zai Aura..! Safiya ta Sakarmai Ido Cike da kwallah Kafin tace"Ban yi maka wannan alfarman ba My Dear..!. Cikin mamaki ya Tambayeta"Saboda Mene Babe na..? Safiya ta Runtse ido ta bude kafin tave"Kayan Lefe na yafe maka su..Kayan Daki kuma ai ba Harumin ka bane na Iyayena ne..Ni ka kyaleni nan Dakin bai Ishemu Rayuwarmu bame Dagani sai kai..? Ga falo chan ga Kitchen ga komai na Bukatar Rayuwa..?me kuma nake nima Ni Safiya banda Kwanciyar Hankali da Zama Lafiya da Mijina da Sabon Gidan dana Tsinci kaina..! Ta karishe Fada Hawaye suna kwanroyomata Da Sauri Yusuf ya Rumgume tsam yana Fadin"Ba Saboda Ke zan yi kayan fa..Saboda kaina ne ki Rika sakawa kinamin kwalliya Dasu..Mganar Kayan Daki kuma ba Ruwanki Zamu koma wanchan bangaran nan da wani Lokaci ba Saboda ke saboda kyawawan Ya"yan da Zaki Haifamin nan gaba..Ni su Abbu sun gama min komai Tunda suka Bani ke bana Kuma Bukatar Komai Daga Wajensu! Ta Dago kanta ta Bude baki Zatayi mgana ya Hanata bayan ya Dora Hannunsa saman Lebenta yace"Shii...Zamu je mu gaishesu in muka Samu Natsuwa..Ammh all i say hakan ne Zai Faru..! Bata da ikob Sake mai gaddama sai ta koma Bisa Kirjinsa ta Lafe yana Rike da ita kamar wani zai kwaceta. Ahaka ya sauko Da ita saman Cafet ya jawo Ledan dan ya Fito musi da Takeway din Daya yi musu sai kaZa Gashashiya da yourghot,mai Sanyi Dakyar taci Shinkafar ya Hadamata da Kazan da Madaran sai da ta kusa amai ya kyaleta kana Shima yaci Sosai yasha Madaran Daga gani kila ya Wuni bai ci komai bane Kamar Tayimai Hawaye,bayan sun gama Tana Nokewa ya kwasheta zuwa Tiolet ya sakarmusu Shower Dole suka yi wanka Bayan sun gama Nanikan juna Duk da Yusuf din bai mata komai ba sai dai Rumguma da Kiss haka. Alwala suka Dauro,ya jasu Sallah Raka"a Shida Bayan sun Idar yayi musu addu'o"i sosai na Zaman lafiya kafon suyi Shirin Barci Shi ya Bude akwatin Safiya ya Dauko mata Wata Rigar barci guda Daya wacce wajen Tuso kayaneta Shigo ammh ko Barayin kayan Barcinta bata Bude ba Tana Nokewa Tana komai ya Dauketa ya aza kan gado ya Cire mata Doguwar rigar Data sakata yanzu Tunda kayanra sun Jike suna Tiolet Yusuf ya Shanya mata. Hakan nan ta Runtse ido ya sakamata Rigat barcin Shima ya Tube Dagashi sai Boxers ya Hayo gadon ya Ciccibita ya sakata Cikin Jikinsa ya Nadesu Cikin Blanker Bayan ya Rage Hasken Dakin yana jinta yadda Take Mutsu Mutsu da kuma yadda Zuciyarta ke Bugawa. Cikin Mirmishi ya Sunkuya kunnenta Yayi mara Rada yana Fadin"Relax babe Babu Abunda Zan yi miki ayau din nan..Ban kuma ce Gobe ma haka ba kawai dai kafin mu Zama Daya Dani Dake nake so na baki Labarin GIDANMU..labarin da kika so kiji ban Taba Fadamiki ba Labarin da ban Taba Gayama kowa ba sai ke yau din nan..Ba saboda komai ba sai Saboda Daga yau din mun Riga mun Zama Abu Daya Komai nawa naki ne Komai naki nawane haka Sirrina naki ne kamar yadda Sirrinki yake Nawa Babe na..! Safiya Dataji Abun kamar a Mafarki ta Dago da kanta bata ganin Fuskarsa Saboda Duhu sai dai tana iya ganin Shedar Fuskar tashi Cikin Tsananin Farinciki ta Damke hannunsa Tana Fadin"are u Serious..! Kai ya Gyada mata kafin yayi mata Kiss a goshinta cikin so da kauna Rumgumesa Tayi sosai Tana Fadin"Tanque Dear..Uhm...Am all Hears..! Yusuf ya kara Riketa ajikinsa Bayan ya zagayo da Hannyensa Bayanta zuwa Saman Cikinta lokaci Daya ya Sauke ajiyar rai Dana Zuciya Tuna abunda ya Faru dasu Shekaru uku Zuwa Hudu da suka gabata.