← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 190

Sashe 77

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Zai wuce sun Shagala da aikata barnan su basu lura dashi ba. Zuciyarsa ta kusa Bugawa Daya Fahimci Inteesar ce Maza Biyu suka Zagayeta Daya na Shirin kaimata Duka Cikin Zafin nama ya Dira gabansu Lokaci Daya yana Rike Hannun wanda zai kaimata Dukam Cikin Bacin rai da Zafin Zuciya. Cikin mamaki suke Binsa da kallo na Gaban ne yace"Mallam lafiya..? Kada ka shiga abunda ba ruwanka ka barmu muyi aikinmu mu gama in ba so kake yanzu Jikin ka yayi Lahani ba..! Bai ma tsaya Sauraransa ba ya yarfar da Hannunsa Cikin Fushi wanda sai da ya Ja baya kamar zai fadi cikin mamaki suka Dago suna kara Kallonsa. Inteesar Data ga haka cikin Sauri ta Taso ta Rumgume Imran ta baya tana Mkarkyartan Tsoro da kuka Tana Fadin"Ya Imran sun karbemun waya..Sun fito da wuka zasu kasheni..! Gabaadaya ta Rukumkumesa Kukanta kuwa ji yake kamar wani Dalma na Shiga Cikin kwakwalwarsa. Ransa na baci Zuciyarsa na Zafi kamar Zata kama da Wuta Jijiyoyin kansa sun tashi Radau. Mai Wukan ne yace"kai jika aikin zaka Ma haka..?lalle ka kira Ajalinka yau..! Yafada Lokaci Daya yana Ciro wuka dake jikinsa ya Nufi Imran da ita yana zuwa ya daga zai Chakamai ya Damke hannunsa da Karfi Har sai da Wukar ta Fadi kasa ya murde hanun ka ya Saka Gwiwan kafarsa ya Daki bayansa sai da ya Fadi kasa,Dayan na ganin haka ya ja baya Cikin mamaki. Imran ya Mika masa Hannu yana Fadin"Bani Wayar da ka amsa..! Cikin Kaushin murya Tsoro ya kamashi ammh ya Dake yana Fadin"Wata Waya kuma mallam..!kai Waye..? Imran ya kara Mikamasa Hannu yana Fadin"Bani nace..Kada ka bari na Sake maimaita mganata bazaka ji da dadi ba.Kuma ni ba wanda ya isa yamin Tambaya sai dai ni na isa nayi Tambaya kuma Dole abani amsataaa .! Ya karishe Fada Cikin Tsawan da gayen da Sauri ya mikamasa Wayar yana Fadin"Baba mu gudu..Ina jin Soja ne..! Yana fadamin haka ya taketa Shima Wanda aka Daka din ya Mike nan yabar wukar nashi yabi bayan Dan"uwansa suka Ari na kare basu Tsaya ba sai da suka bar Layin.. Ajiyar Zuciya ya Sauke ganin sun Tafi ita kuwa Inteesar kuka Kadai Take yi Tana kamkame dashi Tsoro ya Riga ya kamata.. Dan Raba jikinsu yayi Saboda Gabadaya wani Iri yake jin kansa Ammh taki sakinsa sai ma kara Rikesa datake yi Tana Shasshekan kuka Ganin bata cikin Natsuwarta yasa ya Saka Hannunsa Guda Daya ya Dafa kanta yana Fadin"Shiii...Sun tafi fa..! Yake fada yana dan Buga kanta alamun Lallashi. Sai da yaji ta dawo cikin Natsuwarta ta Daina kuka ta koma ajiyar Zuciya. Kana ya Dagota yana kallonta Fuskarta Tayi kace kace da Hawaye da Majina..Cikin Kaushin murya yace"Me yasa kika kai Dare..?baki da Hankali ne..?yanzu da ban zo ba Allah kadai yasan me xasu yi miki..? Ila ma su Illataki..! Yafada cikin Tsawa da Takaichi yana jin Zafi acikin Ransa yana auna da Wani abu ya sameta vaisan yadda Zai yi ba. Kuka ta kara sakamai tana Rike da Hannunsa tana Fadin"Wlh bansani ba..bansani bane..! Take fada kamar ranta Zai fita ganin Mutane sun fara wucewa suna Kallonsu ne yasa yace"Naji is ok..Share Hawayenki ki wuce kije gida..! Yafada yana Mika mata Hanky din Dake Hannunsa tana Kallonsa ta Karba ta Goge Hawayenta ta mikamai ya girgizamata kai Lokaci Daya ya Mikamata Wayarta yana Fadin"Ga wayarki..! Karba Tayi hannunta na rawa tana Waigo Waigo ganin haka yasa yace mata"muje ko..! Tafiya ta farayi tana Waige waige Cikin Tsoro ganin yana Binta abaya ne yasa Taji dan Sanyi suna cikin Tafiya Ledan Pure water da aka sha aka wurgar iska ya kadasa ya Hau kafarta ta Saka ihu ta Dawo baya ta Rirrike Imran cikin Tsoro. Kallonta yayi yana Fadin"Ki bar rike in ba Haka ba zan koma na barki ke kadai..! Tana jin haka ta sake shi ammh taki sakin hannunsa Cikin mamaki yace"Leave my Hand..! Tana shan majina tace"Don Allah ka barni na rike..Ina jin tsoro ne kamar Zan mutu..! Take fada Tana tsiyayan kwallah sai ta bashi Tsaiusayi bai kara mgana ba Har suka zo kofar gidan har Zaure ya Rakata Kafin ya Kalli Hannunsa yadda ta kamkame yace"To sakeni ki shiga gida..! Sai alokacin ta Sakeshi kwallah na Zubomata tace"Tanque so much For Saving my Life Ya Imra..Nagode..! Tafada Tana kuka kai ya Girgizamata kafin yace"Bana son kuka nan..Ki share Hawayenki ki shiga gida..Kada ki Fadama kowa abunda ya Faru kin ji ko.? Kamar yadda yace haka tayi Tana Share Hawayenta tana Dagamai kai kafin ta Fara Tafiya zuwa Cikin Gidan Tama yi tana Waigensa Har ta shige sai da yaga Shigarta kana ya Juya yabi hanyar gida cike da Tunane tunane Inteesar Allah ya Taimaketa Mama na Bayi shiyasa ta Lallabata ta shige kurya ta Haye gado ta Dunkule tana kuka Data Runtse ido Wukanan take gani Gabadaya Taakasa Natsuwa sai kuka Takeyi dataji motsin mama ne sai ta yi Shuru ta koma Ta Lafe.
Chapter 77 · 0% Book details