← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 187 OF 190

Sashe 187

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Daga Kano Inna Maimunatu ta wuce Bauchi ya"yanta suma kowacce ta koma Gidanta Umma kuma bata Kwana ba ta koma kaduna Tunda Daddy da ya Basheer sun koma Shi da Anty Hauwa da Little Inteesar Anty Safiyama Da Imran karami Daya Fara Wayau duk sai sukaji Gidan Shiru ba Gilmawar Abba yana Barayinsa ba Munari sai su kadai Allah yasa ma ga Kirniyar imran karami.
Munari kuma Dagachan Abuja Inna Bintalo kwana Biyu tayi ta so tayi ta Koma Baffa Kabiru yace taa Tsaya ta Raka Munari Dakinta haka kuwa akayi kwanansu Uku a Abuja suka wuce Porthercourt da Rakiyan Inna Bintalo kwananta Biyu suka Hadota da sha Tara na arziki suka Sakota ajirgi sai Gombe Ta koma Gidanta Domin ta Sauke gajiyan bayan ta Kira Duka yan"uwanta tasanar dasu ta Dawo Lafiya ta Raka yarta Munari Dakinta.
Sai da suka Shafe wajen Sati Biyu suna Sauke Gajiya Domin fa an sha Zirga Zirga Munari suna waya da Inteesar da sauran yan"uwanta Inteesat tasha Korafin irin Wahalan da Abokan Mijinta suka gana ma kawayenta Harda Sajida ma suna mgana Ita tabama Imran Labari yayi ta Dariya To Daman Tunda suka auri wadanan Tazuran ai sun gama yawo sai Fatan Allah ya basu Zaaman lafiya ita kanta Inteesar din ai ta gayama aya Zaginta Domin kwanakin nan kaf sai da Imran ya Famshe ita Duk Sauke gajiyan da Kowa yayi bata samu wannan Damar ba.
Allah Sarki Inteesar ita kadai ta Cigaba da zuwa makaranta kafin Transfer din Hafsah ya samu ta dawo nan da Karatu Gidansu Imran ya kara Zama Gida Saboda Mama ta kama su Imran ta Rike gam kamar ya"yanta Abba kuma yahada kan Iyalansa Waje Daya Sagir Daya kasance Dan Gida ne bai da wata Mtsala Anty Safiya na jin Dadin Zama da Mama sosai Gabadaya Renon Imran karami ya koma Hannunta ashashenta yake wuni Ta Tabbatar ita da Abba zasu kwaceshi ne Ita kanta Anty Safiyan in ba Abba ko Ya yusuf ne ya dawo ba tana Wajen Maman.
Sagir ma shi da Hafsah suna Gidan kusan kullum sai da Abba yayi musu irin na Imran yace su zauna Gidansu kada su kara zuwa kana akaji Shiru Gabadaya Imran Dayaji Labari yana ta Dariya Harda gwalo.
Munari ta Bude musu Group isu isu Ita Hafsah,Inteesar, sajida Nasara da Tasleem Nasara itama an saka Ranarta anan Kaduna Zatayi aure wani ma"aikacin NNPC zata Aura Saura Tasleem da itama Zata Fara Karatu anan jami"ar Bayaron Inteesar nata Murnan ta samu yan uwa sunan Group din SISTER"S FOREVER❤️,Chan suke Haduwa suna Baza Iskancin su son Ransu suna Tadin mazajensu da yarda zasu kara Zama Taurari a Wajensu da bama Juna Shawara Kowa Tana Fadin in Mijinta na kwararamata Ihun Dadi Inteesar taki cewa komai suna ta Tambayanta To ai in Ta Fada ta gama Tona asirin Ya Imu Daya Dade a Lullunbe bazata so kannensa su ji wannan mganar ba ganin Taki Fada suka Zageta suka Kyaleta ita sai dai Dariya kawai.
Ba Dadewa Hafsah ta samu Transfer ta Fara zuwa makaranta ba Depatment daya suke da Inteesar ba haka ma Tasleem data Fara zuwa sai dai kusan Kullum suna Haduwa Tasleem Direba ke zuwa Daukanta ita kuma Inteesar watarana Imran in yazo suna Tare da Hafsah ya Daukesu Dukkamsu in kuma sun tashi da Wuri kowacce Tayi gidanta Domin sun Fara Biya biyen Gidajen kansu ko na Abba Imran ya Tsawatar yace kowa ta Zauni Gidanta.
Sannu Sannu bata Hana zuwa sai dai a Dade ba"a je ba Gashi har Cikin Inteesar ya isa Haihuwa, Tana zuwa awo a wani asibitin kudi Ciki yayi Kato yayi Girman da bata iyama kanta Komai Allah yasa sun samu Hutun shiga aji Uku Daada Dataji Labarin Halin da Inteesar ke Ciki ta Kira Umma Tace tazo ta Dauke yarta ta Haihu agabanta Imran yaso ya Hana sai dai Abba yayi mai mgana Dole ya Kyaleta Daman ta Zama abun Tsausayi Ciki ya hana komai..
Umma tazo ta tafi da Inteesar ta Dawo gabanta ko kwana Goma batayi da dawowa ba ta Haihu a asibitin Barau Dukku Dake kaduna Yan Biyu ta Haifa mace da Namiji masu kama da Imran Murna Wajen Wannan Ahalin sai wanda ya gani Imran kamar ya Zuba ruwa akasa yasha a Kaduna akayi Shagalin suna Yara sukaci sunan Abba da Anni Wato Abubakar da Zuwaira kuma da Abba da Anni Za"a Rika Kiransu,Hafsace kadai tazo suna Sajida da Munari ba wacce tazo duk da sun so zuwa Munari Laulayi ne ya Hanata Sajida kuma Suna Jarabawa Domin ta Fara Karatunta Hafsah kuma Daman Tana da Karamin Cikinta..
Imran yayi bajinta sosai a Haihuwar Inteesar ya siyamata kyauta Mota karama 206na Murnan Haihuwan yan Biyu nan tayi jegonta Cikin Kulawar Umma da Daddy Kamar ya maidata Intee Ciki su Anni kuwa suna ganin gata Bayan Tayi arba"in bata koma Kano ba sai da ta Zaga Dangi sune har Abuja,Gidan Baffa Kabiru sai da suka Kwana Biyu suka Dawo Taje Bauchi Wajen Inna Maimunatu taje Gombe Daganan ta Karisa Dukku Burin Daada ya Cika ta Dauki Ya"yan imran da Inteesar jikokin Malami da Abubakar Sauran Jikokin Malami da Kabiru.
Har Dutse sai da Inteesar taje gidan ya Sa"id bayan dawowarta Daga Kadunna ammh shi ita da Imran sukaje suka kwana Daya suka Dawo Ta Dawo da Kwana ashirin ta koma Bikin Nasara sai a wannan karom Sajida da Munari suka zo murna ba"a mgana da suka Hadu sai Tashin Hira Gabadayansu suna da ciki banda Sajida Da suke mata Tsiyan ko Tana planing ne tace musu AllaH ne bai kawo ba Dukkansu da mazajensu suka zo bayan Biki kuma kowa ya tasa abarsa suka koma Amarya nasara ta tare agidan Mijinta Dake Malali kaduna.
Inteesar mai Taya Reno aka Daukan mata Wata yar yarinya saboda makaranta Mama ta samo mata nan kasansu take kwana wajen Inteesar din sai Weekend take zuwa Gida sunanta Hanne,Inteesar Tana Wahala sosai ga makaranta ga Renon yaran har Biyu ga Ubansu bai iya Komai ba sai fadan in anyi ba Daidai ba.
Sagir ya gama Karatunsa ya Cigaba da Dinkinsa Tunda aikin bai Samu ba suna dai Cigaba da nema.
Ashekaran suka je Lagos ita da Imran da yaran su an Turasu Seminar Gidan Abba suka sauka ba Hotel ba,Tunda Matan Lurwani maigadi suna kula da gidan ko"ina Tsab,Sati Daya sukayi kafin su gama Seminar,Su Inteesar taje Gidan Sajida suma sun zo musu Har Gidan Dr Ali argungun sunje,Bayan sun dawo Sukaje Parthecourt,Harda Sagir da Hafsah suka gano Munari suka Dawo.

******

*MURFI...*!!!
_AFTER 7 YERARS BACK..._
Chapter 187 · 0% Book details