Sashe 138
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Hatta Baffa Kabiru Dake Abuja ya samu Labari inna Bintalo Gulma na cinta bayan ta gama Kiran ya"yanta su Siyama ta Tseguminta musu Duk Abunda ya Faru sukayi ta Zagin Imran suna Kuma cewa Daada bata kyauta ba tayi ta Kiran Mami Asma"u a waya ammh Wayar na Ringing bata Daga ba sai ta Kira Baffa Kabiru Lokacin ma yana Office Suna da wata Sharia mai Zafi ga Damuwa ga Abunda ya Faru jiya Wanda har suka iso Abuja bai ko kalli Barayin da Mami take ba har kuma yau din nan basu kara Haduwa ba Domin Tun bayan Dawowarsu kowa ya Shige Dakinsa Bai nemeta ba itama bata Nemesa ba Khamis ma yana cikin dakinsa yana Faaman da Raunin Zuciya na Rasa Inteesar gefe Daya ga Mtsalan da Mami da Dad,Umaima ce kadai ta Leka Mamin Sai tace mata batajin Dadi ta fita ta bata waje bata kawo wani abu ba,Ta koma Dakin Dad sai ta iske ya Fita bata Damu da Rashin Ganin Sajida ba atunaninta ta Wuce makaranta chan suka Fara maidata ita kafin su dawo gida batabi ta kan Khamis ba itama Tun Safe Direba ya kaita makaranta yan aiki kadai aka Bari suna ta Bidirinsu acikin Gida.
Lokacin da Binta ta Fadamai an Daura aure bai wani Damu ba Saboda ba Shakka Jiya ya kwana bai yi barci ba yana Nazarin Rayuwarsa Tun Daga Farkon yarintarsa Har Girmansa Haduwarsa da Asma"u zuwa auransu da yadda yake sonta ya kuma nuna mata Ya Tabbata Soyayyar Dayake ma Asma"u ce Weekness dinsa itace Silar Faruwar duk abunda ya Faru,ya sakar ma Asma"u komai nashi Rayuwarsa Rayuwar ya'yansu itace Take Tafiyar da komai Rayuwarsa ma shi da yan"uwansa shi ya bata Damar Tafiyar da komai saboda baya iya yin wani abu acikin Dangi sai ya Bata Labari kuma in tace kada yayi kaza ga yadda take so ayi haka ne zai Faru ne,Tana amfani da wannan Weeknees din nashi Tana yadda Ta gama Dama a Rayuwarsa gaskiyan Daada ne shi ya bata Komai da Tun farko bai bata Damar saka baki Cikin abunda ya Shafi Ahalinsa sa ba ita bata isa ta Ja da mganar Daada ba da Tun Farko bata Nuna Jajayarta kan auran imran da Sajida ba da Imran bai Saketa ba,da ya nuna mata bacin Ransa ya Nuna mata bata isa ba da haka bata Faru ba ammh Sai ya goyi bayanta yana ganin eh Daada batayi Daidai ba Yau ga abunda ya Faru Asma"u ta Ci Zarafin Daada bataji kunya ba..Itafa Ta Haifeshi Itace Uwa garesa ammh Asma"u bata Duba wannan ba kanta Kadai ta sani Shima son kansa Shi yajamai komai da ace bai da son kai da bai kyamaci Jinin Malami ba.Da Abunda ya Faru bai Faru ba,Da Daada batayi Fushi Dashi ba da Sajida ta Samu Abunda take so take Buri.
Fatan Alheri yayi Yana kokarin Dauke Hawayen da suka acikin Idanuwansa,Sai dai ya shiga Damuwa Sanda yaji Sajida na kwance ba Lafiya Batama san an Daura auran ba Baffa Kabiru yaji Takaichi Asma"u zata Kashemai ya saboda son kanta Wlh Shi Zai kaita kara Kotu in har wani abu ya samu Sajiya ya gane kuskuransa zai nemi Daada gafara zai kuma gyara Tsakaninsa da yan"uwansa Zai gayama Asma"u ta Shiga Hankalinta in kuma ba Haka ba Komai zai iya Faruwa.
Khamis ma ya Samu Labari ta waya Daya gani a group haka ya kwanta Saman gado yana kuka kamar karamin yaro ba Soja ba Mami Ta Riga ta Ruguza komai ba,Ta yi Sanadiyar shiga Tsakaninsa da abunda yake so Sai dai bazai yi Fushi da ita ba,uwa take garesa Sai dai Dole zai yi nesa da gida in ya Tafi baxai Dawo nan kusa ba so yake yayi nesa da Duk wata Hayaniya ko Damuwa ya yarda Imran yayi nasara shi kuma He is a Loser.
*****
Abba da Daddy shiryen Shiryen Tafiya suke yi sun yi mgana da Inna Bintalo da Inna Maimunatu zasu zauna su kara kwana Biyu har Daada ta Watseke Mganar Sajida kuwa sai da Abba da Daddy suka duka suna Rokon Daada Ta amince Sajida ta zauna in ta ji Sauki sai ta koma Abuja Kana Daada ta amince ammh da Farko cewa Tayi Sajida bazata zauna mata agida ba bata da Alaqa da ita ta koma Abuja gaban Iyayenta.
Kafim su Wuce sai da Daada ta kara Jadadda musu cewa Tarewar Inteesar kada ta wuce Wata Daya bata son jan Lokaci Tana son Ta dauki dan Imran da Inteesar da hannunta Jikan Mustapha da malami kafin ta bar Duniya Daddy ya tabbatar mata da Insha Allahu bazai Dauki Lokaci ba Da Daddy yace ma Daada ko nan Dukku Za"a dawo ayi Taron Bikin Daada tace a"a bata Bukatar ganin kowa su yi Taronsu chan wannan Tsakaninsu ne sai yadda suka Tsara.
Sai dai a turo mata Inteesar tana son ganinta kafin Lokaci sannan ayi al"ada kada ace baza"ayi wannan ba saboda na gida ne A"a Aure irin auren kowa ne abama Imran Wahala sosai yayi Duka al'adu kafin Abashi Inteesar su Abba nata Dariya Imran na wajen ya Hade rai yana cema Daada nima sai ta Wahala zan yarda na Tare Dariya su Sagir harda rike ciki,sai da suka sanya Daada Farinciki kana suka Wuce Motar yusuf su Sadam da Abba suka shiga sai Sa"id wanda ya Dauke su Imran zai ijiye su kano kafin ya wuce Jigawa,Umma kuma da Daddy ya Basheer ya Tuka su,a gombe suka Tsaya sukayi Sallar Azahar kana suka Dauki Hanya.
Allah Sarki suka baro Dukku Cike da Tsausayin Sajida da ita kanta Daada,Sai bayan Tafiyar su ta Farka Ta dan samu karfin jiki kuma Zazzabin ya sauka,Inna Maimunatu ta Taimakamata tayi wanka tadan Tsakuri abinci Inna Maimunatu ne ke ta Kula da ita Inna Bintalo kuwa Gulma kadai ta iya da Munafunci ta Girma bata san ta Girma ba ita ta Lallabo bayan Fitam Inna Maimunatu Zuwa Dakin Daada tazo tana gayama Sajida an Daura auran Imran da Inteesar nan da nan ta sake Rikicewa da kuka da Inna Maimunatu tazo ta ganta Cikin Wannan Halin Tasan Dalili Bintalo ce ai bata da Girma sai na Jikinta Kullum tana Girma Tana cin kasa
Ko ta kanta bata bi ba,Ta koma Tana Ta Lallashin Sajida,wacce ke kuka kamar Ranta zai Fita Idanuwanta Jajir take kallon Inna Maimunatu Lokaci Daya Tana Fadin"Goggo Shikenan Ya Imran ya sakeni..Shikenan Mami Ta Rabani da Mijina..!
Take Fada Tana kuka Rumgumeta Inna Maimunatu tayi kamar tayi kukan itama Tace"A"a ba shikenan ba Sajida kin ji ko..? Kiyi hakuri ki Daina kuka da yardan Allah zaki samu wani Mijin Dayafi Imran komai da komai..!
Girgiza kai take yi Tana Fadin"ko na samu bazan so shi ba..Imran nake so shi zuciyata ke Zafi saboda soyayyarsa..!
Tafada Tana Dagowa Hannun Inna Maimunatu ta kama ta Dora Saman Kirjinta Tana Fadin"Kin ji yadda take Bugawa ko..?to da soyayyar Imran take Bugawa kuma Tana gabda Daina Bugawa Saboda shi..!
Ta karishe Fada Hawaye na wanke mata Fuska Inna Maimunati sai ta kasa mgana Hawaye take share mata Acikin Ranta Tana fadin anya Asma"u zata ga Daidai kuwa..?
Hakkin yarta Sajida ta tabbata bazai barta ba
Dakyar ta samu Sajidan Tayi shuru ta koma ta kwanta Tana Shesshekan kuka,Ta fice zuciyarta Cike da Tsausayin Sajida ga Daada Tayi Fushi Sosai da Yaya kabirun da duk abunda ya Shafe shi ballatana taje ta gayamata Halin da Sajidan ke ciki Lamarin sai gyaran Allah kawai.