← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 166 OF 190

Sashe 166

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Inteesar kwana Biyu ta Dauka Tana Fushi da Imran kan Hanata zuwa Gidan Abba shi kuwa baima san Tanayi ba in ma Fushi ne tayi ta gama Shi baima nuna ya gane hakan ba Ballatana ta saka ran zai Lallasheta. Kwana Biyun ko mgana batayi mai Daga gaisuwa shikenan kuma bataje Makaranta ba basu da jarabawa daman Guda biyu ya Rage musu su gama. Abun ma nata sai ya koma basa Dariya ko Falo ta Fito da Daddare ta gansa Zaune yana aiki sai ta wani Dauke kanta ta zauna chan nesa Tana Taba wayarta ko Tana karatu Duk yana Lura da ita,bai kuma Taba nuna mata yana ma Fahimceta ba. Bata san wani abu ba Shi ko basu yi mgana ba Ganinta kawai da Tabbacin Ita din matarsa ce wani Sinadiri ne na Farimciki da Samun Salama da Sukuni a Rayuwarsa. Data gaji ne da kanta ta Hakura Sanin bazai Taba Sauya mgana ba Ballatana Ya Imu dai baisan ka bata rai kan yayi wani abu ya baka Hakuri ko ya Lallasheka ba. Imran bai taba jin Labarin Soyayyar Sagir da Hafsah data Khalil Data Munari ba shi ya Dauka da aka gama Biki sun kama kansu da rawan Jikin da suka Dinga yi kan yaran sai Ranar Yaji Inteesar na mgana da Hafsah ta Waya suna Zencen mamaki ya gama kamasa aransa yana Tunanin meke Damun Sagir da Khalil ne..? Banda Tsabar jama kai Raini ina su ina Wadanan yaran..? Yana Zaune ne saman Kujera Sanye da karamin Wando 3Quater da Karamar Riga mai Gajeren Hannu Laptop dinsa ne a gabansa yana wani aikin da gobe Manager din Branch din Gyadi gyadi zai karba yaji suna mgana ita duk azatonta yana aikinsa baya jinta bata sani ba Duka Motsinta a idonsa ne sai dai yana komai da Taku ne kuma yana da Karfin ji kamar Maciji Daga cikin Wayar ma yana jin Abunda Hafsah take Fadi Har suka gama waya bai yi mgana ba Inteesar Complex take sha batayi Girki ba Gogan bai Damu ba Daya Dawo Tea kadai yasha Cikinsa ya Cika. Sai da suka gama kana ya Dago yana kallon Inteesar Dake sanye cikin Wata Riga mai Taushi tashan Iska sai dai Tana da dan Kauri kadan sai dai bata da Dogom Hannu kanta Hula ce ta Zamani ta yanmata ta Rufe kanta Dashi Kafarta Daya kan Daya ta Dora Tana shan Complex dinta. Suna Hada ido ta Turamai baki Har da Murgudawa Ido ya Ware yana Fadin"Ni kike Harara kuma kike Turamin baki harda Murgudamin Baki Duka ni kadai..!? Cikin Tabara tace"Ni fa badakai nake ba..! Yana Sosa Gemunsa yace"Uhn..Kin rainani..?to bada ni kike ba dawa kike..?akwai wani agidan ne bayan ni dake..,? Yafada yana Tsareta da Kaifaffun Idanuwansa bazata jure ba yasa ta Kauda Kai batayi mgana ba sai Chan Tace"To ba kai bane..Sai kazo ka zauna ko fa Hira bakamin ni in nayi mgana kace zan dameka da Hayaniya kana aiki ne..! Imran na Cigaba da aikinsa yace"Yes..Ko ba aikin nake yi ba..?in na Biye miki zaki hanani aiki na ne..! Jin haka yasa bata kara mgana ba Ta Cigaba da shan abun Dake Hannunta Shima haka sai chan yace"Wai wasu yara ne Sagir da Khalil ke soyayya dasu..? Yafada yana Cigaba da aikinsa bai Dago ba,Inteesar Taji Hira ai sai ta Gyara Zama tana Fadin"Sagir yana son Hafsah..Shi kuma Khalil Munari..Don Allah basu Dace b..?munari tace min yace soon iyayansaa zasu zo ayi mgana Hakama Sagir..! Mamaki ya Cikashi Cikin karin mamakin ya Dago yana Fadin"Wacece Hafsah..!? Inteesar tace"Laa..Hafsah Autan Goggo Maimuna,wacce ke karatu nan Dutse tana zaune tare da su Ya Sa"id..! Kai ya gyada yana Fadin"Su yaranan suke so..?yaran da yaushe aka gama Share musu majina..Khalil da Sagir sun ji Haushi basu da Girma sai na Jikinsu..! Inteesar ta Rike baki Tana Fadin"Munarin da Hafsah ne yara Ya Imu..!,? A karkace yace"Eh in ba yara ba manya ne..? Inteesar tace"Tab..Age mate dina ne fa Nima kenan yarinya ce..? Imran ya Dage gira yana Fadin"To ai kema Duka Kina Layinsu yarinya ce Baki san abunda kike yi ba..! Yafada kai Tsaye Inteesar ta Mike Tsaye Har tana neman Ture Mug din Dake Hannunta Kan Centet Table din Dake gabansa ta Dankwar dashi Tana Fadin"Ni ce ma yarinya..?ni ce bansan Abunda nake yi ba..? Tafada kamar zatayi kuka Imran ya Hade rai yana Kokarin Danne Dariyansa yace"Eh mana..! Ai sai Inteesar ta Fara Buga Kafa tana Tsallen Shagwaba da kukan karya Tana Fadin"Ni Wlh ba yarinya bace..Babba ce Tunda nayi aure..! Mirmishi yayi yana Kokarin Boye Dariyansa yana kallonta yace'"Ai wannan aikin ma da kike yi na yaran ne..Kuma kin ce ke Babba ce Tunda kin yi aure ko..? Kai ta gyadamai Tana Jan Hanci kamar mai kukan gaske,Kansa yake Shafawa yana Fadin"Ai fa ga Babba nan..Sannu Babba..! Yake Fada yana Dariya Inteesar an samu Waje kawai sai ta koma ta Zauna Dirshan saman Cafet ta saka kuka Baki ya saki yana kallonta Kafin ya Gimtse Fuska yana Fadin'"Lalle ma yarinyar nan Duka kike so inaganin ba Lallashi ba ko..!? tsayawa Tayi da kukan Tana kallonsa kafin Ta waro ido Tana Fadin"Duka..? Kai ya gyada mata yana Fadin"Eh mana nan fa ba Umma ba Daddy..Wlh kika Dameni Zanemiki jiki Zan yi.U..! Ai bai gama mgana ba Ta Mike da Sauri ta Dauki Wayarta da Mug din Datake shan Complez suma sum Ta Shige Kitchen bata Dade ba ta Fito ko Gud Night din ma batacemai ta Shige Dakinta Dariya yayi yana Fadin"Better..! Domin bai Shiryama Rigimarta ba a wannan Lokacin Ita batasan Tana Dagulamai lissafi bane Shiyasa take kara yin wasu abubuwan. Abun na Ransa bai manta ba Washegari Daya Fita aiki Bayan sun tashi Lunch ya Kira Sagir yana Cemai yanzu banda Tsabar Raini da Zubar da Girma ina su ina soyayya da yaran da ko Hankalin kansu basu gama mallaka ba..? Ga mata nan manya masu Hankali acikin Gari sai su yarda Girman ku kuna Biyema yara..! Sagir yayi Dariya kamar me kafin yace eh sun ji shi ba yarinyar ya aura ba..?Sanda yake makale Murya yana Fadin don Allah Baby in d'an kara suna ina..? Imran ya Rike baki yana Dariya yace"Sangiru ka zama Dan iska In kara uwar me..? Sagir na Dariya yace"Koma miye ka sani in kuma kana son na Fada ne to..! Imran yace"Basai ka Fadama ba kada Kasa Kunnena ya Toshe..Sangiru Allah ya Shirya ka Zama D'an iska har kana san Abunda miji da mata suke yi.. Gabadayamsu Dariya suke yi Sagir yace"Bamu sani ba sai kai Tunda kayi aure .! Imran yace"Kai dallah..Ni fa bana son Raini sam.Kagani nan ko zan amshi Hakkina umarni zan bada kawai..Allah ya kyauta in zauna ina Wani Rage murya kamar wani Sakarai..! Sagir yace"Uhm..Lokaci na zuwa..Lokacin da zaka gane Karuwa ba yar iska bace..! Imran yace"Wlh yar iska ce..! Sagir yace"A"ah fa Sana"arta take yi kada kace haka..! Gabadayansu Dariya suke yi Daga Karshe Imu yace Wlh su nemi mai musu Best friend Allah ya kyauta yaje Cikin yara yana Bude baki da Girmansa,da komai. Sagir yace bakomai sun ji gari da yawa maye ai baya ci kansa ba kuma ko bai zama Best friend ba ai ya Zama Babban yaya..! Haka ya Kira Khalil yana gayamai Shima cewa yayi ai karamar yarinyar ya aura Daga Wajensa suka koya shiyasa Haka shima yace mai Bazai je Cikin yara yana mgana ba in sun neni manyan mata shikenan yana Tsausaya musu ga kayan Raini ga Dawainiya maimakon Ta Kula Dakai kai ne Zaka koma kana kula da ita Dukkansu sukace mai sun ji kuma sun gani sun gode da Shawara ji ya Zama Dole yadda ne ba Dole ba. Khalil sai da ya bama Munari Labari batayi mamaki ba Sanin Halin Ya Imu Tace ai ita kanta Inteesar Wahalar sa Take sha Kafin ta Samu Lagonsa sai Ta yi kamar tanayi irin su kana yi ne kamar Baka yi ba irin Mazan da suke Laushi bane lokaci Daya,Ammh Zai yi Laushin In Tafiya Tayi Tafiya In ji Khalil. Ranar Friday ta kama Zasu yi Second to d the Last Paper dinsu Sai Tafiya Hutun da zasu dawo su shiga Aji Biyu sai karfe 12pm suke da Exam gida Imran ya Barta In Lokaci yayi Zata Kulle Gida ta Hau adaidaita Tatafi makaranta Bata Tambayashi Zuwa Gidan Abba ba sai da ya Tafi Wajen aiki ta Kirashi bai Dauka ba sai ta Turamai Sako Don Allah ya barta Tabi Munari zuwa Gidan Abba. Daya gani sai ya Shareta Aiki yayi mai yawa sai da ta kara Kiransa Sannan Mganar ta dawomai Sako ya Tura mata Cikin Gatsensa "Bana ce kada ki kara Zuwa ba..? To ki Tafi din..! Haka ya Tura mata ita kuma Tana ganin haka sai ta Zata ya barta ne suna gama Jarabawa tace Zata bi Munari zuwa gida Munari tace Ya Imun ya barta ne..?saboda ai aganbansu Abba yace kada su kara zuwa nan kusa Har Imran din yayi Fushi Daman Haka Abba yake so su Dauke Kafa na kwana Biyu su Zauna agidansu su kara Fahintar juna. Sai Inteeaar tace eh ya barta Munari bata kara mgana suka tafi Abba baya nan yana cikin makaranta sai da ya dawo ya ganta Dayayi mgana Tace Imu yace tazo in ya taso aiki Zai Zo ya Dauketa Abba yayi mamaki yafa san Halin Imu bazai Huce nan kusa ba ammh dai bai ce komai ba. Har bayan Isha"i Shuru ba Imran ba Dalilinsa kuma a ka"idarsa yana Tashi aiki Hudu zuwa Biyar na yammah in ya Tsaya wani abun ne Shida na yammah Kafin mangariba ya iso ammh Yau shuru Inteesar Tayi ta Kiransa bai Dauka ba sai idonta ya Raina Fata Munari ta Kalleta Tana Fadin"Wai Daman bai barki ba kika Taho..! Inteesar na ta Fito da Wayarta Tana Dubo Test din da yayi mata ta Nuna ma Munari Tana Fadin"Shifa yace naje kalli ma ki gani..! Munari ta amsa ta karanta Cikin Mamaki ta kalli Inteesar Tana Fadin"uhm..ni ban ma san me zan ce miki ba..?Kalli fa abunda yace Keji din..?shine kuma kika je din..?Allah ne kadai yasan yadda Kika Batamai rai kila don ma kene Da yau wani ne ko Wata da ya Raina kansa..! Inteesar Idonta ya Raina Fata Tayi Shuru ta kasa
Chapter 166 · 0% Book details