← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 190

Sashe 33

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*DR.ABUBAKAR HAMISU DUKKU* (Malami) shine Asalin sunan Mahaifinmu,Dr ne a bangaaran Ilimi kuma Malami ne Daya shafe fin shekaru Goma yana koyawar a Jami"ar Lagos, Wato a University of Lagos Fanni Sanin Hallayar Dan Adam Wato Phsychology Sunan Malami kuma da Abbanmu ke Amfani Dashi ya samu asali ne akan Tun yana karami yake kaunar Zama Malami Dalilin haka yasa Mahaifinsa Marigayi Alkali Hamisu Dukku ke kiransa da Malami Tun yana amsa Sunan Abubakar Hamisu Dukku Har Dukkun ya bace bat ya koma amfani da Abubakar Malaminsa Duk wanda ya sansa da wannan Fitattacen Sunansa ya sansa. Mahaifinmu asalin Bafullatanin Gombe ne ta Uwa ta Uba,Daada da Marigayi Alkali Dukkansu Haifaffun gombe ne,A karamar Hukumar Dukku Dake Jahar na Gombe. Awajen Mahaifinsu su Biyar ne Uku Maza Mata Biyu Abba ne D"a na Biyu awajensa,Akwai Baffa Kabir,sai Baffa Mustapha,sai Goggo Bintalo sai Karamarsu wacce Munari taci Sunanta Maimunatu. Abaya kafin Rayuwa ta Juyamana Gidanmu Gida ne na Soyayya da kaunar Juna da kuma Hadin kai. Mahaifiyarmu Hajiya Zuwaira auran Zumunci ne Tsakaninsu da Abbanmu,Domin Daada Mahaifiyarsu Diyar kanwartace ta Dauketa ta Riketa awajenta Har ta aura ma Abba ayadda Anni ta sanar Damu Lokacin Abba ya kawo wata tace da Niyyar ya aura Wata Shatu wacce suka Hadu da ita a Jami"ar Jos,inda yayi Karatu Sai Daada Ta nuna A"a ta kuma wanke Mahaifiyarmu Anni ta bashi bai Mata Gaddama ya saka Hannu Bibbiyu ya karba Domin Shi Mutum ne mai Sanyin Hali da Biyayyah. Da Farko ba a Lagos su Abba suka Fara Zama ba sai da suka zauna a nan Cikin garin Gombe,Lokacin yana Assistan Lacture ne a jami"ar Gombe Bayan Kamallah Degree dinsa na Biyu ne Ya samu aikin Bayan auransa da Anni kuma ya Daukota Zuwa Gombe. A garin Gombe aka Haifi Yaya Nura da Ni da kuma Imran Sai Zuwa Lokacin Abba ya gama Hada Phd dinsa Ya samu Sauyin aiki Daga Jami"ar Gombe da Tuni Daman ya koma mataayin Senior Lacture. Muka Tattara muka koma Lagos da zama acikin Tsakiyar garin Lagos A wata anguwa mai suna Vitoria Inland..! A lagos muka Dora Sabuwar Rayuwa,Daman Tun a gombe Ya Nura da ni mun Fara zuwa makaranta Dayake Dukkanmu Har Imu Haihuwa Kai kai ne Cikin Shekaru Hudu Anni ta Haifemu mun taso Gabadayanmu kanmu Daya ne,Da muka koma Lagos ne Abba ya Sanyamu a Wata makarantar kudi mai kyau mukaci Gaba da Zuwa,A kuma garin ne aka Haifi Asma"u da Salima sai Munari Itace Auta. Yusuf Daya kawo nan a Labarinsa Safiya Taji shuru Tana jinsa ta Muskuta ta Dago tana kallonsa jin yayi Shuru Duk da bata ganin Fuskarsa Tace"Ina jinka My Dear sai akayi yaya..? Ina Anni ina Ya Nura da Salima da Asma"u..? Ina kuma yan uwanku na Dukku Sauran Yan"uwan Abba..? Kuma wani Dalili ne ya Dawo Daku Rayuwa A kano Bayan komai naku yana Lagos..? Me kuma ya Faru da Abba Har ya samu wannan Rashin Lafiya..? Kuma meneme ainihi yake Damunsa..? Ta karishe Fada Cikin zumudi da son Jin karshen Labarin Gidansu Yusuf. Yusuf Da Jikinsa yayi sanyi Baya son Tuna Labarin nan ko kadan Ammh Ya Zama Dole ya Karishe ma Safiya Labarin nan ko Zata Fahimci ba Wai Da gangane ko Rashin asali ne ya Maidosu Rayuwa su kadai ba Wani Kadaddaran Al"amari ne da Allah ya Riga ya Rubuta sai ya Faru. kara kamkameta yayi ajikinsa Kafin ya Cigaba da mgana Cikin Sanyin Murya da Sarewa. Mun taso Cikin Soyayya da kauna ta Kowani Fanni Abba Mutum ne mai Dattako da Sanin ya kamata mai kula da Iyalansa da Danginsa Duk da muyi Nisa ammh kusan Duk wata yana Hanyar Gombe zuwa ganin Daada Bayan Rasuwar Mahaifinsu Alkali Hamisu Wani Lokacin Tare da Anni suke Tafiya wani Lokacin kuma Shi kadai mu kuma muna Zuwa makaranra Tun safe sai yammah in mun Dawo gida akwai malamin da Abba ya Daukar mana yana Koyamana Karatun addini Sakamakon ba Lokaci sai ya kasance sai mu Fi Shekara bamu Taka garin Gombe ba,gwarama ya Nura Dani mukam bi Abba Gombe in zai je Hutun Karshen Shekara sai abar Anni da su Asma"u a gida Kafin mu Dawo Shiyasa Duk Cikin mu muka Sanin Dangi Dangi ma suka fi Sanin mu. Lokacin gaskiya Zumunci yafi karfi ta Bangaran iyayanmu mu ya"ya bamu Damu dashi ba Kowanne ya"yansa na makaranta gashi ba"a zaune waje Daya,Ballatana arika Ziyarar juna akai akai Ballatana asan juna Sosai. Bamu san kowa ba sai Abba da Anni sune Duniyarmu Gaba da Baya Abba ya Sadaukar da komai nashi Saboda mu Anni kuma ta Sadaukar da Lokacinta da Lafiyanta Wajen Tarbiyantar damu da kula da mu,Lokacinta da komai namu ne Muna Matukar sonta da kaunarta Domin Duk Fadin garin Lagos Daga Anni sai Abba sai sauran yan Gidanmu kadai Muke Dashi Duka Dangi Basa kusa Baffa Kabiru yana Abuja Baffa Mustapha yana Kaduna Sai Goggo Bintalo tana aure a gombe ne Goggo Maimuna kuwa Tana aure a Bauchi ne Daada kuma Tana Asalin Gidansu na Dukku ne sai dai Aje Chan adubata. Duk Cikin mu Imran ne kadai yayi makarantar kwana acikin Garin Lagos yayi karatun Karamar Secondary Dinsa har Zuwa babba Primary ne Kadai yayi ta Jeka ka Dawo,Ba wanda Yayi mamakin Zabinsa Saninsa Shi bamai Son Sakewa da Mutane bane da Hayaniya Shiyasa yana garin Lagos ammh Sai an Samu Htu kamar Sauran Dalibai yake Zuwa Hutu Gida Shiyasa Gwara Kowa Dashi Ko Dukku Sai ya fi Shekara uku bai Taka ba,ko ya Dawo Hutu in Abba yace ya Shirya aje Dashi Sai yacFara Ciwon karya Saboda Bayason Zuwa Ballatana ya Shiga Mutane ko acikin Gida kowa yana Zaman Falo banda Imu Shi din Hallitarsace Miskilanci da Rashin Son Sakewa,Kowa Daya Fahimci halinsa ne sai kowa ya kiyayemai Ammah banda Asma"u itace Sakon sa Shiyasa Take Shan Wahalansa Kusan in ya Dawo Gida Hutu Kafin ya koma Sai ya Barta da Tabbai Akwai Lokacin da Ya Daketa Har sai da ya Sumar da ita Ran Anni ya Baci ta Mareshi Shine Imu yayi Fushi Lokacin yana Farkon Shiga SS3 NE daya Koma makaranta bai kara Waiwayan Gida ba sai da ya Zana Jarabawarsa Duka ya gama da makaranta ya Dawo Lokacin Ni da Nura Mun samu Gurbin Karatu a Jami"ar Lagos,Tsakanina Dashi Shekara Daya ne shiyasa Karatun namu yake Tafiya kai da kai. Abun bai bama Kowa mamaki ba Da Imran ya Cike Jami"ar Ibadan,Sanin Halinsa Chan ya Tattara ya Tafi karatu inda ya Zabi bangaran accounting,Wani Lokacin sai ayi Hutu Nawa bai zo Gida ba sai dai Abba Ko mu mu kai Ziyara Abba ma yafi Zuwa wani Lokacin in ya Dawo Daga Gombe yana Biyawa ta Wajensa Tunda Shi ya Haifi Abunsa yafi Kowa Sanin Halin kayansa Anni ce ke Damuwa Tayi ta Fadan Imran bayason yan"uwanshi Ballatana Danginsa Tunda bayason Zama Dasu,Abba ke Tausanta Lokacin yana Fadamata ta Cigaba damai addu"a Halinsa kenan,Tayi ta Korafin Dangi ba wanda yasan sa sai dai sunansa Tun yana karami Rabon Daya Taka Gombe Duk Zuwa sai Daada Tayi Mita da Korafi Sai dai Imu bai Damu ba yafi Damuwa da Abunda ya sakama Gaba Fiye da komai a Rayuwarasa. Haka Rayuwarmu ta Cigaba da Tafiya Ni da Nura muka kamallah Digree din mu na farko muka Dora na Biyu da Kwarin Gwiwan Abban mu Asma"u kuma ta Fara Karatu a Lagos state university Lasu Dake Lagos, Tana karantar phamarcy Salima kuma Tana Shekarar Karshe a matakin Secondary,Munari kuma Tana baya Saboda ita din Daga Karshen Anni ta Haifeta Bayaan Salima ta Shekara bakwai a Duniya. Zuwa Lokacin mun san Dadin Dangin mu da kanmu mukan Shirya mu Ziyarcesu ko da Abba baice ba Barin ma Nura yafi kowa son Zaman arewa Domin yace yana Burin ya samu aiki a arewa Yayi aure ya koma Chan da Zama,Shiyasa Duk bayan Wani Lokaci muna Ziyartsu Munje Har Gidan Baffa Kabiru da Baffa Mustapha da kuma Goggo Bintalo,Da goggo Maimuna kuma sun ji Dadi Sosai Daada kuwa Muna da Lambar ta Lokaci Bayan Lokaci muna kiranta muna gaisawa Sai dai Koda yaushe mukayi Waya da ita Zencen ta Daya kenan Imu,Shi kuma Yana Chan makaranta ba Sosai ma yake zuwa Gida ba. Sai Lokacin Daya gama Degree dinsa na Farko yazo Gida Hutu Lokacin ne Abba ya Rutsashi ya iza keyarsa Har Zuwa Dukku Gaban Daada Sai da suka kwana Biyu suka Dawo a wannan Zuwan ne Har su Baffa Kabiru sun zo Sun gansa Shima Lokacin yazo da' Wajensa Khamis Sa"an Imu din ne ammh Har suka Rabu Wata kyakyawan Mu"amala bata Hadasu ba imran bai da Sakin jiki Sam da Mutane Daada Tayi mai Nasiha yayi bakam Kamar yaji yana komawa gida ya yi Cuku cukun ya koma Ibadan ya Dora Degree dinsa na Biyu,ya manta Da Fadan Daada. Rayuwarmu Gidanmu Mun ginata Cikin Karatu Mai Zurfi ne Duka Dana Arabi Dana Bokon Harta Salima itama Tabi Sahu Ta Fadama Jami"ar Lagos ita Fanni Abba take karanta Wato Physchology Muna gama Hada Degree din mu na Biyu Muka Samu manyan ayyuka Nura ya samu aiki a Federal Inland Revenua Service(FIRS)Wato Hukumar Haraji ta kasa Dake Jahar Lagos,Yaso ya samu a arewa sai kuma Allah ya Rubuta nan ne wajen cin Abincinsa. Ni kuma na samu aiki a Hukumar INEC,rejen Jahar Lagos muka Fara aikin mu Cikin Lokaci kadan Cikin Naaara da Sa"a bamu Rufe Shekara Daya ba muka mallaki Motocin Hawa Dani da Nura,Da kudaden da muka Fara Ragema Abba Wasu Hidimdimun Ko Chan Dukku baya sanin muna turama Daada Sako Sai dai in ta Kirashi Tana Godiya ya sani. Asma"u ma Ta gama Karatunta Har ta Fara aiki a wani State Hospital na Lagos a phamarcy, Dake Garin Lagos Salima ita kuma Tana Karatun ne bata gama ba,ita Burinta so Take ta Zama Dr.Salima Watarana Ta gaji Abba Ashe Ashe Burinta bazai Cika ba Domin Lokacinta aduniya bamai yawa bane..! Yusuf ya Fada Hawaye masu Zafi suna kwaranyomasa Jikin Safiya yayi Sanyi Gabanta ya Fadi Cikin karyewar Murya tace"Innalillahi badai Rasuwa Tayi ba..? Yusuf yaji Rauninsa ya Bayyana Cikin Karyewan Zuciya Dana Murya yacCigaba Da fadin"Imran ma ya gama Karatunsa ya Fara aiki da Bankin GT reshen Jahar Lagos Shima ya mallaki Motar Hawansa,da kudaden Daya Tsaya kan Kafafunsa.. Faruwar al"amarin Daya Faru damu
Chapter 33 · 0% Book details