Sashe 35
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read
Allah na samu aiki a hukumar Inec ta nan Reshen Jahar Kano,Ni ne na Zama Uwa da Uban Imran da Munari na Zama Garkuwan Abba na Daukan Mai likitan Dake Zuwa Gida yana Dubasa Duk Bayan Wata Daya,koda Abba ya Fara Dawowa Hayyacinsa ya Fahimci Abunda muka aikata yayi ta kuka sai dai Bai Da Cikakkiyar Lafiyar da Zai iyq Tambayanmu meyasa mukayi hakan..? Da albashina na Siya Motan Hawa na Siya ma Imran Mashin Tunda yace bai Bukatar Mota aiki ma yace bazai koma ba,Shi Baahi da Sauran wani Buri kuma,nayi nayi na Rabashi da Shan Sigari na kasa Saboda ya Riga ya Zama Jikinsa bazai iya Awa Daya bai Sha Sigari ba,duk Wasu Sabbin Halaye Rashi ne da Rayuwa suka maida Imran haka,Ni nayi Tunanin Inganta Rayuwar Munari Tunda ita Kadai take Ragemana na maidata makaranta.. Da farko ban Yi niyyar Fara Neman aure ba sai nayi Tunanin auran nawa Zai Tamaka ma Rayuwar Imran da Munari Sai dai kash Duk inda na Nemi aure sai mgana ta kamkama sai ta watse duk inda akayi Binciken Gidanmu aka gano wani abu duk da bama Hulda da kowa abun mamaki labarin komai sai ya fita, bamu da kowa kuma Abba bashi da lafiya yana Ciwon Hauka Dalilin haka Imran ya karya Hannun Kawun Wata Asma"u Dana Nema aka Hanashi Daga Karshe shi kawun nata yaci Zarafin Gidanmu Shari"a Dakyar na iya kasheta Na nemi aure kusan sau uku bana samu sai a kanki kema din da kokarin Imu na Sameki Tun kuma Bayan Tafiyarmu Har yau wani Daga Cikin Ahalin mu baisan inda muke ba bamu sani ba ko sun neme mu mudai bamu nemi kowa ba Har Rana mai kama ta yau..Ko naso mu nemi gida Imran ke Hanani Domin shi yafi Daukan Abubuwan da suka Faru Fiye dani Kaina.