Sashe 148
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tana ganunta ta Hade Rai Inteeaar na Danne Dariyanta ta isa kusa da ita Zauna ta Fara bata Hakuri Dakyar Munari ta Hakura ammh ta Dauki alkwarin bazata Taba yarda su hadu ba Ballatana Har yayi kwallo Da ita. Sai 6pm Suka Tashi Daga makaranta Direct Gidan su Munari suka Wuce,Sun iske Abba baya nan sun Fita gari shida Yusuf a Sabuwar Motar Abba din Anty Safiya ce agidan ita kadai agajiye suke abinci sukaji Sukayi wanka Lokaci Daya da Dauro alwala Tunda an Kira Sallar mangariba. Shashen Anty Safiya sukaje suna Hira Cikinta Har ya Fito sosai yana cikin Watansa na shida Suna nan har aka Kira Sallar Isha"i suka tashi sukayi Sallar sai lokacin sukaji Dawowar su Abba Falo suka Fita suka gaishesu ya amsa yana Tambayansu makaranta Suka ce Alhamdulillah. Nan falo suka Zauna Tunda Ya yusuf ya Dawo yana Tare da Anty Safiya Abba kuma ya shiga Ciki. Inteesar ta kalli Munari Lokaci Daya Tana kallon Kofar Dakin Imran tace"Ya imu ya dawo kuwa..? Munari na Dannar wayarta tace"Ki Dubasa mana..! Tafada cikin gatsali Inteesar Sai da tayi Dariya tashi tayi ta Leke Haraban Gidan Taga Motarsa ta Dawo Tana cema Munari"Ya dawo fa ga Motar sa chan..! Munari bata ma kara kallonta ba Inteesar ta koma Ta Zauna kenan Imran ya shigo cikin Sallama karama iya Saman Lebensa. Gabadayansu suka Dago suna kallonsa Munari sai da gabanta ya Fadi Da Sauri ta Mike tana gaisheshi ya amsa bai ko kalleta ba Inteesar ya kalla Wacce tayi Saurin Sadda kanta kasa bai ma Tsaya bi ta kan Munari Data Kwashi Sauri zuwa Dakinta ba Hannunsa Cikin Jallabiyansa ya Tura Kofar Dakinsa ya shige. Inteesar ta Sauke ajiyar Zuciya tshi tayi ta shiga Kitchen ta Dauko Ruwa mai Sanyi da Nutri milk ta Dora saman wani Tire da Karamin Kofin glass guda Daya sai da ta tabbatar Abba bai fito ba kana Tayi Sadaf Sadaf ta Kwankwansa Dakin Imu yana jinta jikinsa ya bashi itace shiyasa yace mata ta Shigo. Shigowa Tayi Lokaci Daya da Sallama,Ya amsa mata iya saman Lebe yana Zaune gefen gado yana Duba Wayarsa Kiran Khalil ya gani kila Lokacin Daya tafi masallaci ne ya bar Wayar agida. Daburcewa Tayi ganin yadda ya Dauke kansa Kamar bai san da Wanzuwarta acikin Dakin ba ganin ta Tsaya mai kikam a saman kansa yasa ya Dago yana kallonta Cikin Dan Hade Rai yace"In bazaki ajiye ba ki koma Dashi mana..! Yafada Kai Tsaye yana kallonta Da Sauri ta ijiye nan saman Drower din gadon,Ta koma gefe Tana Fadin"Ruwa na kawo maka sannu da zuwa..! Yana kallonta baya so ya gwasaleta Yasa yace"Is ok..Nagode..! Da haka ya mike Laptop dinsa ya Dauko Cikin Briefcase dinsa ya Dawo ganinta nan Tsaye tana waasa da Zoben hannunta Daga sama har kasa Tana Sanye cikin Riga da Sikat na wani leshi kayan sun mata Das ajiki gabadaya Sturcute dinta ya bayyana Saurin Dauke kansa yayi jin yanayinsa na Sauyawa,Karamin kugunta yake kallo ta gefen ido kan gadon ya zauna yana Bude Laptop din gabansa Lokaci Daya yana Fadin"Kina Bukatar wani abu ne..? Yafada yana kokarin Daidaita kansa Cikin Shagwaba ta Dago Tana Fadin"Bakai bane kana ta Fushi Dani ba..! Waro ido yayi yana kallonta kafin yace"Ni..?yaushe..nace ina Fushi Dake ai kin bani hakuri kuma na Hakura..me kuma nayi Ni Imrana bawan Allah Sarkin Laifi..! Yafada yana Tattara Duka Hankalinsa akanta Cikin Sha"awar kallonta. Lamgwabe kai Tayi tana Fadin"To naga sai Fushi kake dani kaki Sakin Fuskarka..! Kai ya gyada kafin ya Mike Lokaci Daya yana Ture Laptop din gabansa yace"kinsan yanayina..Ni bakimin komai ba..! Sake Bata Fuska tayi Zatayi mgana yayi Saurin cewa"Kada kimin kuka..Plz am not in d mood..Kuma ni ban iya Lallashi ba sai duka..! Baki ta Tura kafin tace"Yanzu sai ka Dakeni..!? Gira ya Dagamata yana Fadin"Yes of course kina ganin bazan iya bane..! Zaneki Zan yi Tsab yadda baki da wani kiba nan..! Yafada yana yar Dariya Lokaci Daya yana kallonta kasa kasa. Cikin Tura baki tace"Laala..Matar taka Zaka Daka..? Tafada Tana kallonsa ido na cikin ido,irin yadda yake kallonta yasa tayi Saurin Sadda kanta kasa Imran ya Dage giransa yana Fadin"Really..?Hakane fa ke Matatace! Yafada yana shafa Sajensa kafin yace"Zo...! Da sauri ta Dago Tana kallonsa kafin tace"Ni..? Daure Fuska yayi kafin yace"A"a Ni..! Yafada yana kauda kansa jin haka yasa ta Fara takawa zuwa gabansa Kanta na kasa sai da taji Tana jin Hucin Numfashinss kana ta Tsaya Tana Fadin"Gani..! Yana kokarin Daidaita kansa yace"Ai na ganki..! Yafada yana kallon kirjinta da suke mai Maraba,jikinsa ya Fara Shaking bai san yaushe ne ba kawai ya jisa ya Saka Hanmu ya jawota jikinsa ya Rumgumeta kamkam kamar wani zai Kwace masa ita atare suka saki ajiyar Zuciya Cikin Salama Inteesar kara gyara Kwanciya tayi a Faffadan Kirjin Imu Tana shakan kamshin Turaransa mai Dadi da Tafiya da zuciya Har Lumshe ido take yi shima kansa ya Dora Saman kanta Lokaci Daya yana Zagaye bayanta da Faffadan Hannunsa Jinsa yake kamar yana yawo a gajimare saboda Farinciki da Salama. Dankwalin kanta ya Sabule ya Fadi kasa,Inteesar ta kara Rikesa sosai Ta saka Hannunta ta Zagaye kugunsa cikin yanayin da batasan ma Tayi ba Wani irin yarr Imran yaji wanda yasaa ya Tusa kansa cikin Kitson galaban Dake kan Inteesar Neman rasa Control dinsa yake yi yasa Cikin Wata Murya yace"Waya miki wannan kitson..? Inteesar Dataji kamar tayi ta barci Har Abada a jikin Imran tace cikin Wata irin murya"Munari ce..! Hannunsa Daya yasa yana shafa kan nata gabadaya sai inteesar taji Tsigar Jikinta na tashi Wuyanta ya Shafo Takara Rikesa da karfi jin wani Zirr acikin jikinta Lokaci Daya Tana Fadin"Washh..!!! Tafada cikin wata kasallaciyar muryan da bata san tana dashi ba Wannan Muryan datayi amfani da Rikon Datayimai yasa gabadaya yaji yana neman rasa Controlling dinsa yasa yayi Saurin Sakinta ya koma ya Zauna gefen gado da sauri Saboda kada taga Girmansa yadda ta Mike Tsaye Sambal ta bayyana kanta. Kansa ya Dafe ya kasa ma Dagowa saboda yana so yayi kokuwa da yanayin Dayake ciki. Inteesar sai Lokacin taji kunya ya kamata tayi Saurin Daukan Dankwalinta ta Daura Ta juya Cikin Rawan jiki dana Kafa Zata bar Dakin taji yace"Baki fadamin abunda yasa kika shigomin daki ba..? Yafada cikin Sanyin muryan Datake cike da sha"awa. Cak ta Tsaya bata waigo ba tace"Dama..Dama.! "Dama me.?Malama ki juyo kimin mgana ni yaro ne da zaki juyamin baya kina min mgana..! Bata da yadda Zatayi gabanta na Duka ta Juyo Bata yadda ta Kallesa ba shi kuma Duka Shanyayyun idanuwansa ya Zuba mata. Cikin Dakewa tace"Dama na Tambayeka yaushe ne Ka Tsaida Bikin Tarewar mu..? Kallonta yake cikin mamaki kafin yace"Kin kosa ne..? Da Sauri ta Dago kamar tayi kuka Tace"Wlh A,a..Su munari ne suka mtsa suna so suji saboda Shirye shiryen fa..Ni yaushe nace na kosa..! Tafada Tana Tura baki. Kansa ya shafa yana Fadin"Yaran nan sun cika azarbabi..To da suke Tambaya Kayan Daki zasu hada miki ko su zasu min akwatin auran ne da suke Tambaya..? Inteesar ta marairaice Tace"Sufa Saboda Events din da zasu shirya ne..! Kasan kuma hakan na Bukatar Tsare Tsare..! Imran ya Hade Fuska yana Fadin"Event..? A bikin waye zasu yi Event din..? Yafada yana wani Kara Dakuna Fuska. Inteesar tayi narai narai kafin tace"Bikin Tarewar fa..! Tabe baki yayi yana Fadin"an gama mai wuyar Tunda aka Daura auran..Ba wani shanshanci kuma dazai biyo baya in nagama Shirina ni da kaina zan Daukeki mu tafi bana son Hayaniya da wata mgana Ok..! Inteesar ai mamaki ya Kasheta bata samu Damar mgana ba ya cigaba da Fadin"Kuma ma Wa yace a zo a Tambayeni..?meyasa baku kira Daada ko su Daddy ko Abba ba..Kun Rainani ko..?ke kuma mara wayau kece yar aike ko..?da sun sani sun Tare ni da kansu..! Inteesar tace"Ai Daddy ne yace kai zaka Tsaida Date din Imran na Dariya yace"Nagodema Daddy..Ki Fada musu nan da Next year lokacin nima na Tara kudi sosai Kema kinga Lokacin kin Shirya tunda ai yanzu kin ce baki kosa ba..? Inteesar takallesa Kafin ta kauda kai Lokaci Daya Tana Tura Baki yana Danne Dariyansa yace"Eyye ni kike Tura ma baki..? Ai bata ma bari ya kara mgana ba ta Fice da Sauri ya Rakata da Dariya aransa yana Fadin"Yaran fa basu da Hankali so suke su min bidia a bikina...Ashe kuwa zan karya yarinya..! Daki ta koma ta iske Munari na Charting nan ta zauna ta Fadamata Abunda Ya Imu yace Munari tace"Bari zan kira Ya Sagir muyi mgana..yasin Bazamu yardaba sai munyi Bidian da baya so..In yaki ma Daada zamu hadasa ko da su Abba..! Inteesar tace"Gaskiya..Shifa yarda yake so dagani sai shi ba biki ba komai fa..Kamar wata mara Galihu..! Munari tace"Bafa zai sabu ba yadda mukaci Burin bikin nan sai fa an sha Hidima iya Hidima Amaryan Oga Imu..! Dariya suka saka gabadayansu kafin su cigaba da Hiransu sama sama.