← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 190

Sashe 142

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

da kara For What Turai..?Wlh ki shiga Hankalinki kema ki Fadama yarki Kada ta Sake ta shigar da wata kara in kuma taki ji bataki gani ba..! Daga haka ya Dauki Farin Glass dinsa ya sanya ya Cigaba da karatun Jaridarsa yana jinta Tana ta Masifa Tana Zagin Kabiru wai dan Talaka bai da komai Mirmishin gefen baki yayi aransa yace"A"a fa Kabiru fa ba Talaka bane...Shi wani ne Mahaifinsa Har ya bar Gidan Duniya Alkali alkalai ne na Kotun musulunci kuma Talaka bai Taka wannan Mtsayin..! Hajiya Turai Daki ta koma ta Kira Yarta Tana Fada Tana Fadin ita ta bata goyon baya Shari"a zuwa Kotun koli su bazasu ji tsoronta ba Mami Asma"u ta Fashe da kuka tana ta Fadamata irin yadda yan"uwan Baffa Kabiru suka Tozarta tare da Mahaifiyarsu Ta kare da Fadin"Hajiya Sun Rabani Da Sajida..Wlh neman zagina take saboda wannan Tsinannen yaron..! Hajiya Turai tace"Rabu dasu duk zasu gane basu da wayau..Saki ne dai Matakin da Kabiru zai dauka na karshe ko..? To in ya fasa ya sake kin yagani in baki samu wani Babban goron Daya Takasa ba..! Dayake Idanuwanta ya Rufe bata Fahimci Zata Tafka kuskure ba Mami Asma"u na Fadin"Wlh Hajiya..Ai daman ance Babban goro sai magogim karfe..! Sun dade suna mgana Hajiya Turai bata Taushi Yarta ba ko Daya sai ma kara zugata Da tayi shi ya kara mata Kwarin gwiwa suna gama waya tayi wanka ta Fice a gurguje ko Karyawa batayi ba Ta fita taje Office suka Hadu da Brr. Zailani kan Tana so Ashigar da karar kai Tsaye ne Daga Kotu ta Cike Complain Form kuma ta na karan Daada ne da ya"yanta Guda Biyu Mustapha Hamisu Dukku da Abubakar Hamisu dukku..! Abunda bata sani ba suna gama mgana da Brr.Zailani ya zagaya ya Kira Baffa Kabiru ya sanar dashi komai,Daman tun sanda Mamin Ta Kirashi kan Complain din yaji mamakin wai zata shigar da kara kan Mahaifiyar Brr. kabiru da Yan"uwansa Shiyasa ya Kirasa ya Fadamai shi kuma yace da Zarar ta Cike Complain Form ya fadamai Lokacin ne zai yi mganin Asma"u Zata ga True Colour dinsa da bata taba gani ba sai ya Koyamata Hankali Zai nuna mata ana Sauya mata ammh ba"a Sauya Uwa da yan"uwa. Gabadaya Ransa ya gama baci yau Za"ayi ta kare Baya so ya yanke Hukunci cikin Fushi shiyasa bai Dawo Gidan ba yana son ya yanke komai a Saukake. Yana Office Sajida ta Kirasa Tana Fadamai ta Dawo makaranta yau daga Dukku yana ta mamaki Tsausayinta ya kamashi Data gayamai a Motar Haya ta dawo ya sani itama ta Guji Gidan ne saboda Mahaifiyarsu ta gama Illata Zuciyarsu,Yaji kamar yayi mata Kwallah Fatan alheri yayi mata da kuma Nasihan ta Cire Damuwa tayi Facing din karatunta ta amsa mai da Insha Allahu. Dukkansu sun kashe Wayar kowa Zuciyarsa ba Dadi,Baffa Kabiru kamar yayi kwallah,Kudi ya Tura mata 30k yace ta siya abunda bata dsshi Lokacin Dataga Sakon nasa Tana libary ne tazo Karatu ba Domin Tana Fahimta ba sai domin shine Mafitanta. Yau da Safe goggo Maimunatu ta koma Bauchi Mijinta yazo duba Daada Daganan ya wuce da ita Daman itace ke Kula da ita goggo Bintalo ba Ruwanta Ballatana Daada da Fushin Mami da Dad ya shafeta Ta riga tasan tayi rashin Rashim Masoyin da bazata taba maida kafarsa ba,Mami Ta riga ta gama Lalatamata Farincikinta gani tayi Zaman bai da wani amfani yasa ta fara shirin Tafiya Duk bata wani jin Dadi ga Sakewar jikiga na zuciya. Sai da tagama Shiryawa kana taje Dakin Daada Tayi mata sallama Daada Tsausayin Sajida ya kamata ta Rumgumeta tana Lallashinta da ban baki Sajida na kuka tana Rokon Daada ta yafema Dad dinta Daada tace bata Rikesa ba in ya gano kuskuransa ita Tafi kowa Murna da haka. Ita ta bama Sajida 5k duk da tace tana da kudi tace ta kara Tunda makaranta Zata koma Bayan Tafiyar Sajida Daada tayi kuka,Yarinyar abar Tsausayi ce Dama Dama haka bai Faru ba data Hakura da Cin Mutumcin Asma"u sai dai ai ba ita auran ke hannunta ba Wanda Auran ke hannunsa ya warware kuma bazata Tursasamai kan sai ya maida Sajidan ba, tayi alkawarin ta bar kara Tursasa kowa koda ya"yanta na Cikinta ne.
Chapter 142 · 0% Book details