← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 190

Sashe 37

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

*****
Washegari Wasu Zukatan sun Tashi ba Dadi yayinda Wasu Zukatan suka Tashi Cikin Farincikin,Cikin Wadanda Suka kwana Cikin Bakinciki Imran ne Farko Kwata kwata Barci Barawo ne kadai ya iya sacesa Daya Runtse ido Sai ya rika ganin Inteesar Sanda Take Tofar da Miyau Lokaci Daya da. Toshe Hancinta In kuma ya yi Shuru kunnuwansa Amon Muryanta suke ji Inda Ta Kallesa Tana Kiramai Ta"awizi kamar Taga Shedan kwana Yayi Busa Sigari sai da ya karar da Kwalaye uku kana ya Saurara Gabadaya Bakincikin Yadda bai Sauyama Yarinyar nan kammani bane ya kamashi,Daya sani ko Mari ya Tsinketa Dashi ya Tattakata Wanda nan gaba bazata Kara Raina wani bama Shi ba,Ammh Takaichinsa Daya Da ya bari ta Subucemai ya Zama Dole ya Nemi Sagir ko wacece zai Santa Koma Daga ina take yana da Masaniyar komai ya Zama Dole ya Nemota ko domin yaci Ubanta ya Nuna Mata Karyanta Imran Ba wajen Wasanta bane.
Bangaran Inteesar kuwa Tayi kwanan Farinciki Hankalinta kwance Tuni ta manta da wani Imran Ballatana Abunda ya Faru Daman koda Mama ta Dawo Ta gaji ta Fara jin Barci Sama Sama Sukayi mgana tace mata ta Shiga Makota ne,Daganan Ciki Ta Shige.Bayan Ta Tatarra Littafanta,Tayi Sallar Isha"i tabi Lafiyan Gado Barci ya Fara Daukanta Taji Mganar Sagir din nan Falon Mama Ita dai bata kara Samun kanta ba sai da asuba da Mama tasheta Sallah.
Bayan ta idar da Sallar ne Tayi azkar ta Fita Tsakar gida Taga Mama na Shara ta gaisheta sai ta amshi Sharan Mama bata Hanata ba tunda Umma tace ta rika bata kowani aiki ne Saboda Ita Macece Domin amfanin kanta Watarana.
Ita ta Share Tsakar gidan Tas ta koma ta Gyara Cikin Dakin da Falo ta Share ta Goge kafin ta gama Mama ta Dafa mata Ruwan Zafi sai ta Juye tayi Wanka Koda ta Fito 7:30am na Safe kuma ta Kira Classrep dinsu yace mata 8am suke da Lacture,Shiyasa Take Sauri Ko Tea da Buredin da mama ta Hadamata bata Tsaya Sha ba Complex Kadai ta sha..Sai Cake Data Diba ta saka ajaka ta Dauki Littafanta ta Fito Tana yima Mama Sallama ta Dauki Kudi ta bata taki amsa tace Tana da Kudi a Hanunta Jin Haka yasa Mama Ta kyaleta ammh Sai ta Buga ma Sagir Kofa tace ya Fito ya Raka Intee ta samu abun Hawa Zuwa makaranta.
Haka kuwa akayi Shi ya Rakata Har Bakin Titi suna Tafe suna Hira sai da ta Samu Abun Hawa Zuwa Cikin makaranta Sannan ya Dawo yayi wanka ya karya ya Fita Zuwa Shago yau bai da Shiga makaranta sai Gobe.
Bangaransu Yusuf da Amaryansa Safiya Lafiya kalau suka Tashi Cikin Farinciki ba domin ya Hanata Fitowa da Wuri ba da Tun Safe taso ta Fita Kitchen Ta Taya Munari Hada Breakfast,yusuf ya hanata sai dai ta Tayashi Shirya wa zai tafi Wajen aiki Domin ya Sanar da yayi aure ko Zai Samu koda Hutun Sati Daya ne..Dukkansu sunyi wanka Safiya ta Shirya Cikin Daya Daga Cikin kayanta na Gida,Shi kuma Yusuf yana Sanye da kananun kaya ne,Sun Fito Falon kenan Sukaci karo da Munari ta Fito Daga Dakin Abba itama Cikin Shirin Fita Tana ganinsu ta Washe baki Tana Fadin"Mr and Mrs Yusuf Abubakar Malami.. Gud Mrning..!
Tafada Tana yar Dariya Yusuf ya Kalleta Lokaci Daya yana Lakuce mata yacw"Mrning How was ur Nite..?
Safiya tace"Lilsisy kin Tashi Lafiya..?
Munari tace"Lafiya Lau Anty Safiya..Ya yusuf Yanzu Abba ke Tambayanku..!
Yusuf yace"yanzu Wajensa Zamu Shiga..ya karya..?
Kai ta gyada mai kafin tace"Eh yau kunun Gyada nayi mana Sai na Soya Dankali..Yanzu na gama bashi yasha na bashi mgani Sauri nake tayi Yaya Zan Shiga makaranta 8am muke da Karatu..!.
Yusuf yace"Sannu da kokari..Bazaki jirani na Sauke ki ba..?
Agogon Fatan Dake Hannunta Ta Kallah Kafin tace"A"a Ya Yusuf bari na Tafi in na Tsaya jiranka Zan makara..!
Bai mata Musu ba ya Ciro 1k Cikin Aljihun Wandonsa ya Mikamata yana Fadin"Take Care..!
Ta karba Tana Fadin"Tanque Ya Yusuf..Anty Safiya Bye..!.Tafada Tana Daga mata Hannu,Hannun itama Safiyan ta Dagamata Tana Fadin"Sai kin Dawo ki kula da kanki..!
Mirmishi Tayi musu kafin ta Fice su kuma suka Shiga Dakin Abba suka Iskeshi yana Zaune kan gado yana Tunani Kasa suka Zauna suka Gaisheshi ya amsa yana Saka musu albakar.
Yusuf ya Kalli Abba yana Fadin"Ya karfin Jikin Abba..?Hope dai ba Wata Mtsala..!
Abba ya Girgizq kai kafin yace"Ina Samun Sauki..!.
Atare Shi da Safiya suka amsa da Allah ya kara Lafiya Kafin Yusuf ya Muskuta yana Fadama Abba Shawarwn da Safiya ta kawo Abba ya Dade kansa na Kasa kafin ya Dago ya Murmusa yana Fadin"Cikamakon Mutum Shine Samun Mace ta Gari...NAgode sosai yata..Kuma nayi Miki alkawarin Zan baki Kowani Hadin kai Domin Tamkar Munari nake kallonki..Sannan ni kaina Ina son na Warke Ko Domin na Koma ga Yan"uwana da Mahaifiyata..Itace araina Domin In har ina da Rai akwai Hakkinta Daya Rataya a Wuyana..!
Yusuf ya kalli Safiya itama ta Kallesa suka Gyada kai atare Kan Safiya na kasa Tace"Insha Allahu Zaka Samu Lafiya Kamar baka Taba wannan Laluran ba. !
Abba yace"Allah ya amsa..!.
Suka amsa da Ameen sun Dade Zaune Abba yana ta Tambayan Safiya matakin Karatunta Tana Fadamai sai ga Abba na Hirar Karatu da Safiya Data gayamai Fannin Data Karanta yake Fadamata abaya Daman yace in bai Zama Malami ba zai zama Masanin Na"ura ne .
Sai ga Yusuf Farinciki yaki barinsa Ransa Har sukayi ma Abba Sallama suka Fice,Su Biyu Suka yi Breakfast Saman Dining sunayi suna Hira Bayan Sun gama Safiya ta Rakashi Har Haraban gidan bata koma ba sai da Taga Fitar sa Daga Gidan kana ta Koma Cikin Gidan.
Dakin Barcinsu ta koma ta gyara Shi Tsaf kana ta koma ta Tatttara Abunda suka Bata Daga Dining zuwa Kitchen Tana ganin yanayin Kitchen din bai Wani Samun gyara Saboda Munari ce Ita kadai kuma Saboda makaranta Bata Samun Lokacin kanta Ballatana ta Tsabtace Kitchen din
Ga kwanukan Wanke wanke nan Kamar sun fi na kwana Biyu Munari bata samu Damar wankewa ba,Nan Safiya ta Zage ta wanke komai ta maidaahi a Muhallinsa,Ta kuma Share Kitchen din ta Gogeshi Tas ya Fara Kyalli,Ta leka Store Taga akwai komai na Bukatar Girki na Gidan Masu Rufin asiri Ta gyara Store din Shima ta Duba Fridge Shima Shake da Abubuwan amfani bata san Sadda tace Masha Allah ba Domin Komai akwai Babu Abunda kuma Zata Nema Yusuf bai waasa da Cefane Duk Sati,Tasio tamai mganar Cefanen sai Kuma Ta fasa Domin bata san yasan Zata Fara Girki yau din ta tabbata Zai Hanatane..
Bayan ta gama da Kitchen din ta Fito Falo Shima ta gyarashi ta Dauko Abun Shara ta Share ta goge ko"ina Haushinta Daya ko Dan Turaran Wuta Bata Dashi,Sai taji kamar Tayi kuka Sai kuma ta Daure,Ammh Zata Fadama Mommy Abubuwan Data keso Ta Siyamata in sunje da yusuf Sai Ta Taho Daahi kafin Abubuwa su Daidaita.
Daki ta koma ta Dauki Wayarta Da Niyar Kiran Mommy sai kuma Taga Kiranta sai Tabi Bayan kiran Har ta kusa Katsewa Kana Mommy ta Dauka Suka Gaisa Safiya tace"Mommy ina Falo ne na bar wayar a daki nazo Naga Kiran ki.. !
Mommy tace"Tasleem ce ta kiraki..Sai da na Hanata..Yanzu kuma Direba ya tafi kaita Makaranta..!
Safiya tace"Allah Sarki Tasleem..!
Mommy tace"Da kinga bazaki iya Zama ba Safiya ki kirani kinji ko Ni Dakaina Zan zo na Tafi Dake..!
Safiya tace"Bafa komai Mommy..!
Mommy ta Sauke Numfashi Tana Fadin"Shikenan nima yau Zan je gida na Gayama su Baba abunda ya Faru Bazqn iya Kyale Mahaifinku ba Safiya Kada ya ga yayi yaji Dadi ya maimaita akan Tasleem kuma..!
Safiya tayi Shuru kafin tace"Kiyi Hakuri Mommy..!
Mommy tace"Sai na Dauki mataki..Kiyi ma Shuru Kawai..ya mganar Kayan Daki da abubuwan Da kike so ki Rubutomin komai ta Waya ki Turomin Fatana ya Tanadi Muhallin da Zamu saka Miki kayan Duk ga yadda Auran ya kasance..!
Safiya sai ta Kasa cema Mommy Yusuf yace a barshi sai kawai tace Mata"Kibari nazo Mommy Zamu yi mgana..Domin yace in aka kwana Biyu Zamu zo mu Gaisheku..!
Mommy tace"Shikenan..!
Daga Haka sukayi Sallama
Daganan bata zauna ba ta Fita Zuwa Falo Bayan ta Duba Lokaci 9am ta kusa ya kamata ta Shiga ta Duba Abba koda ta Shiga Sai Taga baya Dakin Data Saurara sai taji karar Ruwa yana Wanka kenan sai ta Fito Falo Ta Zauna tana jira Shuru ita Kadai ga Tv ammh kuma da alamu ma ba"a Taba Hadata ba,Batayi mamaki ba ammh Zata Saka Yusuf ya Hadata Saboda Shima kallon yana Rage Damuwa ko da Tashar Wa"azi ce tafi a rika Zama Shuru.
Sai da ta Kwashe Minti Talatin Kana ta koma Dakin Abba ta iske shi tsaye yana Saka Botirin rigar Shaddar Dake Jikinsa Sai dai Bai saka Wandon Shaddar ba Wata ya saka yayi gamin Gambiza kenan.
Tana Shigowa da Sallama ya Waigo yana amsa mata Cikin Sakin Fuska.
Kanta na kasa Tace"Barka da Hutawa Abba..!
Abba yace"Yauwa yata..Sai dai Gidan Duk ba kowa sub barki ke kadai ko..? Sai Imurana Kuma Dashi ba Babu Duk Daya na Tabbata har yanzu bai fiti ba..!
Safiya tace"La bakomai Abba..Dama na Shigo na Dubaka ne..Nace ko Zaka Fito Falo yau ka Huta Kafin anjuma..!?
Abba ya Murmusa Kafin Yace"Nagode yata..Naji Dadin hakan ni kaina Nagaji da Zama Waje Daya muje..!
Kanta ta Sadda kasa kafin Tace"Amh..Abba Kayan ba iri Daya bane. !
Sai da ta Fada ya Duba ya ganu kai kawai ya Girgiza Kafin yace"Kinga ba Domin kin yi mgana ban Ma Lura ba..!
Bata Damu ba tace"Bakomai Abba...In ba Damuwa bari na Duba maka wandon Rigar ko..!
Yace"Yauwa to Dubomin ni Duk idona ma ya Cinye Saboda Rashin Ganin Hasken Waje..!
Tana Bude Wardrope din Tace"Zai Washe Da yardan Allah Abba..!
Cikin Farimciki yace Allah, yasa bata Wahala ba ta gano Wando ta Daukomai ya karba Sai ita kuma ta Fice Bayan ta Daukan mai Matashi,Falo ta koma ta Sakamai Matashin Saman kujera mai Cin Mutum Biyu,ta Shiga Kitchen ta Daukomai Ruwa da Kofi tazo ta Jawo Karamin Table zuwa gaban Kujera Ta rasa Ma Zata Dauko ma Abba ya Daukemai Hankali Sai ta Tuna Taga karamin Qur"ani acikin Dirowar Yuauf da Sauri taje ta Dauko Ta yanke Shawaran Zata kira Yusuf yazo da Jaridun Datayimai mgana Jiya.
Tana Fitowa Abba Shima na Fitowa Mirmishi yayi mata itama ta maidamai Yau Rana Daya yana jin kansa Kamar bashi ba,Bai Taba Fitowa ya Zauna afalon nan ba Tun Dawowarsu Gidan koda yaushe yana Cikin Daki in baya kwance yana Zaune yana Tunani.
Sai da ya Zauna kana ya Rika sakama Safiya albarka tana amsawa ta Tsiyayamai Ruwa ta mikamai yasha Kadan ya Miko mata Tana Karba Tana Fadim"Abba badai kajin Barci ko..?
Abba yace"Gaskiya yau ban ji Barci ba..Ko Saboda na baro Katifar Dake Rinjayana Barcin ne..?
Ya karishe Cikin Zolaya Kanta ta Sunkuyar Tana Mirmishi sai ta Mikamai karamin Qur"anin Tana Fadin"Kada ka Zauna Shuru Abba..Saboda Tunani marasa kyau..Ka karanta iya Abunda ya Sauwaka Zan kira Yusuf nacemai ya Taho Maka da Jaridu ka Rika karantawa kana Sanin Abunda Duniya take ciki..!
Abba ya saka Hannu Biyu ya karba Hawaye sun kawo Idanuwansa yace"Barkallahu Fiki..Nagode..!
Yafada yana jin Rauni ya bayyanamai Domin bazai iya Tuna Ranar Karshe Daya yi Karatu ba Lalle Mace agida Shine gida Matukar Bata kuwa sai a Hankali.
Gefw ta koma ta Zauna akasan Cafet Abba yayi ta koma Kujera Taki sai ya Kyaleta Bude Qur"anin yayi ya Faraa Dubawa,Duk da Raunin Idanuwansa sukayi Qur"ani na Dabam ne,Ballatana ai yana da Hadda akansa nan da nan ya Bude Suratul Yusuf ya Fara Karantawa a Hankali Safiya na gefe Tana Kallonsa Cikin Tsausayi ganin Lokaci Bayan Lokaci yana Share Kwallar da suke Cikamai ido..
Chapter 37 · 0% Book details