← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 163 OF 190

Sashe 163

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Fara gaisawa da Course mate dinsu Da suke ta mata Fatan Alheri Wayarta Take Kokarin Cirowa taji an Riketa ta baya tana Juyawa Taga Munari suka Saka Ihu atare suka Rumgume juna. Kafin Munari taja Hannunta su samu Waje su zauna Tunda da Sauran Lokaci.. Nan fa Hira ta Tsinke Munari sai Tsiya Take mata tana kallonta Tana Fadin"Uhm..Amarsu ta angonta..ai na ganku..Aure mai Daraja wai yau Ya Imu ne da kawoki makaranta..! Duka Inteesar ta Dagaamata suna Dariya Munari na Cemata ta Kira wayarta tace bata gani ba yana Jaka Munari sai Faman kallon Inteesar Take Tana Dariya Lokaci Daya Tace"Allah kadai yasan irin Romin amarcin da Ya Imu ya kwasa yau ya kawoki makaranta..Muma mun kusa shiga wannan karnin domin Khalil yace yana komawa zai gabatar da mganarmu..! Inteesar na Dariya tace"Munari ana son Aure..Wai daman yace yana sonki ne..?kun dace fa..! Tafada Bayan ta boyema Munari Wani abu bai Faru Tsakaninta da Imu ba. Munari tace"lalle Tun yaushe...Sagir ma ya kafa Gwannatinsa Wajen Hafsah..! Inteesar ta Zaro ido Tana Fadin"Ki bari don Allah..! Munari tace"Ki zauna mima mun kusa Shiga Daga Ciki yarinya..! Dariya suka saka Inteesar ta nuna jin Dadinta sosai aman take Fadama Munari in sun gama jarabawar yau Tare zasu tafi gida ya Imu ya barta Munari tace aiko kin ji Dadi kya yi Sallama da yan"uwa. Tsaida Hiran sukayi Suka Fara Bitan Jarabawar da zasu yau duk da basu da Mtsala suna Karatin Jarabawa tun Lokacinta batayi ba Karfe 8am na Safe Daidai suka Shiga Paper 1 sai 11am suka Fito basu Zauna wani hira ba suka koma Wacce zasu shiga karfe 12am na Rana Har zuwa Lokacin. Karfe 2pm na Rana suka Fito Shikenan sai kuma Gobe Suke da Guda Daya Daganan Inteesar da Munari suka samu adaidaita zuwa Gidan Inteesar sai Murna take kamar Wacce ta Shekara Kamar ba Jiya bane,Tabar gidan. Koda suka isa Ya Basheer da Anty Hauwa da Anty Uwani da Maman Nasara da ita kanta Nasara sun kusa isa kaduna Harda Umaima Data Bisu Zata kwana anan Kaduna Ya Basheer zai siyan mata Tiket Tabi Jirgin kasa zuwa Abuja. Inteesar bataji Dadi ba Domin ai tasan Daman bazai Tsaya ba Ya Basheer baya son Tafiyar Dare,Inna Maimunatu ma Ta mika Hanya ita dasu Zainab,Inna Bintalo ma ta wuce ita sai ta Biya wajen Daada Dukku. Sa"id ne kadai ya Rage basu Tafi ba sai Sadam su yan Gida ne. Kowa mamaki Dayaga Inteesar Munari ce ke azarbabin cewa Ya Imu yace ta Biyo ta nan in ya baro Wajen aiki zai Biyo ya Dauketa Shiyasa Abba yayi Shuru Sai Gabda La"asar su Sa"id suka Tafi da Hafsah bayan sun gama Sallama da su Munari da suka Hada kai suna ta ma Inteesar Tsiya Harda Tasleem da itana Sallar La"asar kadai sukayi Ita tatafi Gida,Bayan La"asar kuma Ya Sadam da Tawagar Matarsa da ya"yansa suka Wuce gida,Gida ya Rage Daga Anty Safiya sai Abba Dashi ma bai jima da dawowa Daga Office ba. Ya Yusuf bai je aiki ba Ranar yana Gida Sai da suka ci Abinci suka koshi kana Inteesar ta Tambayi Abba zuwa Gidan Mama ta kwaso sauran kayanta ya barta Munari ta Rakata Mama Taji Dadi Itama Gajiyan Biki bai Saketa ba Ta kara yima Inteesar Nasiha sosai kafin ta Dauki Sauran kayanta Saura kuma Tace Mama ta bada su kawai basu wani jima ba Saboda Abba yace Kada su zauna suka Dawo gida. Gyaran Gidan suka Taya Anty Safiya Kafin su Shiga Kitchen suka Dora Girki,Farar shinkafa da Miya Sukayi da Nama Sai mangariba suka gama bayan sun Jera komai Saman Dining kowa yaje yin Sallah kafin su Fito su Abba suka shigo Harda Imran Daya Dawo da Sagir a masallaci suka Hadu Nishadi yake ji kamar ya Shekara baya Gidan.. Ranar Gabadaya suka Hadu Saman Dining Harda Imran da Sagir sukaci Abinci Cikin Farinciki,Bayan sun gama Abba bai yi kasa a gwiwa ba ga kara Yi Musu Nasiha sosai mai Shiga Jiki basu sukabar Gidan ba sai Wajen 9pm bayan Hankaluna sun kwanta Baki sun koma Gidajensu Lafiya.. Suna komawa Gida sun gaji sai Barci Kowa ya Nemi makwancinsa.
Chapter 163 · 0% Book details