← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 190

Sashe 36

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

*Shakira...*
3/22/22, 23:04 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*DEDICATED TO:*
*Aisha alto(Sisinah)*
*Chubado muhammad(Uwar dakina)*
*Yahanasu Soupnass(Qawalli1)*
*Kausar salis(My jika)*
*Rahma Ladingo(Dota)*

             *🅿�14*

"Kinji irin kaddaran Data Fadama Gidanmu Babe..Tun bayan Faruwar Al"amarin Komai namu ya tsaya Cak Kawai Rayuwar muke gamu nan bawani Jin dadi ba Farinciki ba Walwala.
Kinji Kuma Dalilin daya sa muka Baro komai namu kinji kuma irin Halin da muka Shiga da wanda Abba ya Shiga Da Dalilin mu na barin Komai namu muka Dawo muna Rayuwa inda ba"a Sanmu ba kuma kinji Irin Lalauran Data samu Abba Shi din ba Mahaukaci bane yanayin Rayuwa da kaddaran Allah ne suka Maidashi haka.
Ya karishe Fada yana Tsiyayan Hawaye,Safiya ma Dake Jikinsa Hawayen Take,Cikin Sarkewar Murya tace"Allah ya jikansu Anni..Allah yayi musu Rahma Allah ya kyautata Makwancinsu.Hakika kunga Babban Rashi..Tabbas kun Hadu da Jarabawa Mai girma Mutuwar Rai har Guda Hudu a Lokaci Daya dole Zuciya Zata Raunana..Allah ya karbi Shahadarsu..!
Yusuf na jan majina yake amsa mata da Ameen Ameen..
Safiya ta Cigaba da Fadin"Tabbas su Baffa suma basu kyauta ba..kamata yayi su ja ku ajiki da Lallashi da Nasiha da komai sai kuFara manta abunda ya Faru..Su Rika Nuna muku ku Fauwalama Allah komai su Nuna muku Hakan bashine Karshen Rayuwar ba akwai Wasu agaba..Ya kamata ace sun Zauna sunfi Kowa Fahimtar Halin da kuke Ciki..Abba kuma ya kasance koda yaushe Suna Lallashinsa da kokarin Nuna mai Komai Daya Faru da Sanin Allah kuma Mutuwa Dayace Muma Jiranta Muke,su da suka Tafi basu yi Sauri ba Muma da muke Duniyan Jiranta Muke na Tabbata da yanzu baku kai ga Daukan Wannan Matakin ba My Dear..!
Yusuf Dake Sauraran Safiya yace"Gaskiya ne Babe..! Yafada Cikin Sanyin Murya mikewa Tayi Daga Jikinsa,Tana Fadin"My Dear Tashi muyi mgana..!
Bai mata Musu ba ya Mike Zaune ya saka hannu ya kunna Hasken Dakin Suka Kurama juna ido Kan kirjinsa ta koma ta Lafe Tana Fadin"Ina da Wata Shawara My Dear game da Situation din Abba He Need a Help..ba na kai ka dai ba..Taimako yake Nema Awajenmu Dukkanmu matukar muna so ya samu Lafiya ya Daina Tuna Abunda ya Faru.!
Da Sauri Yusuf yace"Wata Shawara ce Babe na..?
Dagowa tayi Tana Kallonsa Hannunsa ta Riko Duka Biyun Tana Fadin"Bai Kamata ku bar Abba yana Fuskatar wannan Abun shi Kadai ba..Kada kuyi Treeting dinsa kamar su Baffa My Dear..Bai dace ace Abba yana Rayuwa acikin Daki ba ko Falo baya iya Fitowa Ahalin yana da lafiyar Kafarsa..Bai kuma Dace arika barinsa Shi kadai ba..Sai Tunanin Da ba"a so Sai yaRika Samun Matsugguni acikin Zuciyarsa ..Masu irin Laluransu suna Bukatar Wani a kusa Dashi a Koyaushe..Ba kamar yadda kuke Barinsa ya Wuni Shi kadai ba Hakan yakan Kara Haifar da Ruruwan Raunin Dayake Cikin Zuciyarsa..Abba yana Bukatar ya Riks Fitowa yana Sakewa yana Walwala,Ya Chanchanci yayi Farinciki..Duk Abunda Zai sakashi Farinciki Shi zAmu Rika Kokarin Yi agabansa muyi Keeping dinsa Yadda Tunani da Damuwa baza ma su samu Damar Nukurkusan sa ba..Kaga Ta hakane kadai Magungunan Likita Zai yi Amfani ajikinsa amfanin na Har Abada ba na dan Lokaci ba..!
Tunda ta Fara mgana ya kafeta da Ido Zuciyarsa ta Cika da Farinciki Da Alfaharin Samun Macen Kirki kamar Safiya DAmam ance Duk Tunanin Namiji Ita mace Tamkar Garkuwa ce Garesa Gashi Cikin Lokaci Tana Warware Musu mtsalan da Shekara da Shekaru suka kasa mganceta.
Girgizashi Tayi ganin yana ta Kallonta bai yi mgana ba tace"Bakace komai ba My Dear..?
Yusuf ya Lumshe ido Kafin yace"Ina Jinki..Zuciyata ce ta Cika da Girma da alfaharin Zamowa Miji gareki Babe na..Ina jinki cigaba da Fadamin yadda komai Zai Tafi Wlh har na Fara Ganin Abba ya samu Lafiya na Har Abada..!
Safiya tace"Insha Allahu Abba zai Samu Lafiya indai muka Taru muka Tallafamai..!
Na farko Abba zai Daina Zaman Daki Zai kasance yana Wuni a Falo,sannan Zamu samo mai Abubuwan da zasu Debemai kewa kamar su Karatun azkar da karatun Karamin Qur"ani wanda Zai Rika Karantawa koda yaushe....Ko Jaridu Domin yarika karantawa yana Sanin Abunda Duniya take Ciki..Littafan Karatun Daya Shafi Fannin sa Wato Physchology,Abu na gaba kuma ya Daina Salla agida ya kasance yana Shiga Cikin mutane ko da bada Wata Mu"amala ba,Ya rika Sallar Cikin Jam"i hakan ma zai kara Taimakamai sosai Wajen Rage Damuwa da Tunani Sannan ya kamata Mu Rika Haduwa dukkanmu Da Daddare muyi Dinner Tare,Bayan mun gama kafin kowanne ya Shiga Barci mu Zauna dashi muyi Hira Labarai na ban Dariya wadanda Zasu Sanyashi Nishadi sannan kuma ya zama Dole ya rika ganin kowa Cikin Walwala ta hakane Shima zai yi kokarin manta komai sabi da ku..Masu irin Laluran Abba suna Bukatar taimakon Mutanen Dake kusa Dasu...!
Bata gama mganarta ba tajita a Jikinsa Ya Rumgumeta Kamkam Kamae wani Zai kwaceta Cikin Farinciki yake Fadin"Tanque so Much Babe na..Allah yayi miki Albarka..U are a Bleesing From Allah..!
Safiya itama ta saka Hannuwa ta Rumgumshi Tana Fadin"My Pleasure My Dear..Is My Duty Amtsayina na Matarka na Tallafeka a Dukkan Komai na al"amuranka Shine Zamantakewar..!
Kamkameta Kawai ya karayi yana Fadin"Alhamdulillah..Allah ne Abun godiya..!
Sun Dauki Tsawon Lokaci ahaka kafin ya Dagota yana Share Mata Guntun Hawayen Dake Idanunta Itama ta Saka Tattausan Hannunta ta Gogemai Nashi a Tare suka Sakarma Juna Mirmishi Hancinsu ya Hada Waje Daya yana Fadin"I love u Babe na..!
Itama cikin Wani Shauki Tace"Love u More and More My Dear..!
Komawa sukayi suka kwanta Bayan ya Dauketa Gabadayaanta ya Dorata Saman Jikinsa,Ya Kashe Musu Hasken Dakin Lokaci Daya ya ja musu Blanket yana Fadin"Oya Barci..Zamu karisa mganar dq Safe..!
Tana Dariya tace"Ok..My Dear..!
Chapter 36 · 0% Book details