Sashe 51
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lokacin Daya koma D'akinsa yana Sakin Huci yaji kamar yayi Bindiga Shi kadai,Saboda Zuciya sai da yasaka Hannunsa ya Naushi Dayan Hannunsa,Kafin ya Zube kan gado yana maida Numfashi,Yaso ya Busa Sigari ko ya Daina jin radadin Abunda yarinyar nan tayimai,Sai dai kuma ya kasa Saboda Abba Yana ganin kamar in yasha bai ji mganarsa ba kenan,Kawai sai ya Matse bai sha ba,sai dai Saboda Zuciyarsa tayi sanyi yasa ya kira Sagir kan yazo su Fita suje Kallan kwallo,Ko ya ji Sanyi a ransa yana kallon Kwallo Tun a Abaya sai dai da suka Dawo kano ba kasafai yake zuwa kallon ba Saboda Hayaniyar Dake Wajen,Ko yaje baya ma iya Zama yau din Yana so yayi nisa da Bacin rai Shiyaasa zai Fita Daga Gidan kada Takaichin Rashin kunyar Inteesar yasa Zuciyarsa ta Buga. Abunda yake karamai Takaichi da Mamaki Tun abaya Dayake amsa Sunansa na Imran ba macen Data Taba yimai Abunda Mara Mutumcin yarinyar nan Tayi mai ballatana Yanzu Dayake jin kanshi yana Daidai da Kugun kowa Bai jin zai iya Daukan wannan iskancin kuma ba Kowa yajamai ba Sai Sagir da Munari su su ka Fara Gayyatota Cikin Rayuwarsa ba Domin Sagir ba bazai Taba Haduwa da ita ba Tun Farko ba kuma Domin Taurin kan Munari ba Da bata Jawota Cikin Gidan nan sun Sake Haduwa ba.. Tun Dazu ya Fito da Niyyar Tafiya ammh ya kasa bai san mai ya Tsaidashi ba Yana Tsaye Jikin Mashin Dinsa kawai Zuciyarsa ta Tsaya Waje Daya Tana Wani Tunani na Dabam. Koda su Abba zasu Fita sai da Yusuf yamai Tayin Fitan yace shi ba zai je ba Haka kurum saboda ya rasa aikin yi sai ya kama Hawa Mota ana Zagayen gari dashi..? Yusuf yace"Nagode Nida Abba ne Marasa aikin yin kenan..!? Imran ya Dakuna Fuska yace"Ni dai ban ce ba..! Yusuf bai kara bi ta kansa ba,Haka ma Abba Daya kada kai kawai yana ma Imran din addu"an Shiriya. Har bayan Tafiyarsu yana nan Tsaye shi bai koma Cikin Gida ba Shi kuma bai Hau Mashin din ya Tafin ba ana Cikin Hakane sai ga Munari da Inteesar sun Fito Inteesar Zata koma Gida Munari Zata taka mata Tun Daga Nesa ya Gansu bai tsaya kurama Munari ido ba Sai dai baisan Ta ina kuma wani Lokaci ko kuma Sanda Idanuwansa suka Raja"a a kallon Tsarin Hallitar Inteesar din Tun Daga nesa,Zuciyarsa ce take Turasa shi kuma yana so ya kaucema hakan sai dai ita Daman Zuciya ita ke Sarrafa gangar Jikin Dan adam Wannan karon Duk yadda Imran yaso ya kaucema Bin Umarnin Zuciyarsa abun ya gagara Tundaga nesa yake kare mata Kallo Har suka Kariso gabda shi basu gansa ba Hankalinsu na Wajen Hiran da Sukeyi suna Dariya Cikin Nishadi Tundaga Kallon Sama da Kasa yake Bin Inteesar Dashi Mamakin Sirita kanta yake yi yana mamakin Daman mace ce wannan..? Abu kamar Kara ai wannan inda ma ya Damketa ya Tabbata Babu abunda Zai dauka ajikinta sai dai ya Kasheta Tabe baki yayi a Fili acikin Ransa yaji sam Tsarinta bai Burgesa ba a tsarin dai Mace,ko abaya bai cika karema Mata kallo ba Tsakaninsa da mace Kallo Dayane Na Addini Shima in ya Zama Dole aiki ya Hadasa ko Mu"amalan Data Zama Dole a wajensa. Sai dai Duk bai Maida Zabinsa a wani abu mai Girma ba,Bashi da Burin auran karamar Mace irinsu Munari kayan Raini da Lalaci maimaikon Ita Zata kula dakai Kaine ZAka koma kana Bin Bayanta kamar Wani Sakarai Yafi son auran Babbar Mace Wacce Ta san Ciwon kanta Wacce Zata iya Kula da kanta wacce ta san komai ba sai an zauna ana Fama da ita ba. Yana wannan Tunanin Daidai Lokacin da Inteesar ta Dago idanuwanta Daga Mganar Datakeyi ma Munari Karo na Uku Suka kara Hada Idanuwansu Kuma Alokaci Daya Suka ji Bugun Zuciyarsu Kamar yadda yasha Faruwa in suka Kalli Juna Cikin ido. Inteesar Taji Jikinta ya Fara rawa da Sauri ta kauda kanta Lokaci Daya Tana Damke Hannun Munari Tana Fadin"Na shiga uku na Munari..Ga Yayan ki chan zai Dake ni ko..? Wayyo Gashi Abba baya nan yanzu ya Zanyi..? Sai Alokacin Munari ta gansa yana Tsaye Jikin Mashin dinsa Sanye da Riga da wando na Kirar Armani Rigar Farace mai Dogon Hannu Tana da Layin Zanen Ash ajikinta Sai Wandon Jikinsa Ash Colour ne,Kafarsa Sanye Cikin Wani Bakin Takalmi mai Igiya Booth,Na Fatar Damisa,Kansa yasha Gyara sosai yana kyalli Key din Mashin Dinsa na Hannunsa yana Kadawa Ayayinda yayi Tsayuwar Nauyin Kafa Daya kan Daya yana Binsu da Wani kallon da suka kasa Gane Manufarsa. Ita kanta Munari Jikinta ya DAuki Rawa Cikin Dauriya ta kara Rike Hannun Inteesar din Tana Fadin"Kada mu nuna mu gansa..Lallaba Besty ki Tafi Kada wata mtsalan ta kara Faruwa..! Jin haka yasa suka Fara Taku Sadaf Sadaf kamar wadanda sukayi Sata,Ganin haka yasa ya Daka Musu Tsawa Cikkn Dakakkiyar Murya yace"Kai ina Zaku..? Cak suka Tsaya sun kasa gaba Ballatana Baya,Cikin Daure fuska da Yanayinsa yace"Tsayuwar Uban me kuke yi anan..? Ku zo nan..! Yafada Cikin Kaushin Muryansa na koyaushe ba waasa. Inteesar tazaro Ido Tana kallon Munari itama ita take kallo Kafin Tace"Sai muje wai Besty..!? Munari tace"Tafiyarmu karin wani Babban Laifi ne..Wato Raini gwara Muje kawai Insha Allahu bazai mana Komai ba..! Inteesar tace acikin Ranta"Tabdijam wazai je..?ya sumar dani..Dole ne na Sama ma kaina Mafita. Da wannan Tunanin taji Munari ta Fara Janta suna Nufarsa Sai da suka kusa kawowa garesa Inteesar ta Kara Rike wayarta sosai a Hannunta Ta Danke Takalminta Dakyau Munari ba Zato kawai taji Inteesar ta Warce Hannunta ta Kwasa da Gudu Kamar Walkiya sai gata Bakin get Ta Tsaya Tana Haki Munari da Imran suka Bita da kallon Mamaki. Kallon Imran Tayi ta Juyamai ido Kafin ta Rike kunnuwanta ta Marairaice Fuska Alamun ban Hakuri kana ta Juya da Sauri ta Fice Har da Gudunta Gudun kada ya Biyota.. Munari ta Tsure Tana Tunanin Kila yau Kafin su Abba su Dawo Ya Imu ya kusa Kasheta Ga Laifin Fitowa ga Laifin Inteesar Da zai hau kanta. Ammh sai mai Data saci kallonsa Karo na Farko Tun Bayan Dawowarsu Kano Dataga mirmishi Saman Fuskar Imran sai abun ya bata mamaki Inda yake Kallo tabi da kallo Bakin get ne inda Inteesar ta Wuce. Sai abun ya kara bata mamaki Matuka ganinsa yana kada kai yana Mirmishi Haka kurum yaji Wani Nishadi da abunda Inteesar din Tayi duk da ba Komai ke basa Nishadi ba. Munari ne taga kamar ya manta da ita yasa Cikin Rawan Murya tace"Ya Imu g..Gani..! Sai alokacin ya kalleta Cikin Daka mata Tsawa yace"Da kika Fito ina Zaki..? Munari taja Baya Jikinta na Rawa tace"Dama..Da..man ina so Zan Rakata ne..! Wani kallo ya watsa mata kafin yace"Shiga Ciki kafin nayi kwallo Dake..! Ai da gudu Munari ta Nufi Cikin Gida aranta Tana ayyana ai ta isa Barka da ya Kyaleta bai Tabata ba itama da Gudun ta Shiga Cikin Falon suka yi Kicibis da Anty Safiya ganinta haka yasa ta Tambayeta Lafiya nan take Labartamata Abunda ya Faru Safiya Tayi Dariya batace komai ba Illah Allah ya kyauta Domin Lamarin Imran Sai dai Allah ya kyauta kawai. Haka Itama Inteesar ta Shiga Gida a Tsorace,Sagir da Mama suna Falo Sagir ke Cin Abinci suna Hira SAma sama da Mama ganinta yadda ta Shigo Duk a tsorace Yasa Sagir da Mama suka Hada bakin Wajen Tambayanta Ko Lafiya..! Sai da Ta Zauna ta Sauke Tagwayen Numfashi kafin tace"Ya Sagir Ashe Abokin naka mai Shan Sigari Yayan Munari ne..? Tab ayau Allah ne ya Kwaceni ba Domin Abbansu da ya Sumar dani nima Domin na Lura Shaye Shayensa ya Fara Tabamai Kwakwalwa..! Sagir ya Zaro ido Kafin ya ijiye Spoon din Hannunsa yana Fadin"Kai badai Imran ba..! Tabe Baki Inteesar Tayi Tana Fadin"Oho ni ina nama nasan Sunansa Inga shi..! Nan ta Fara basu Labarin Abunda ya Faru ta karishr da Fadin"Ina zan je Ina jin Besty Muna tana Labarin in ya Fara Duka sai ya Sumar da Mutum aiko na Gudo chan na barsa da Munari Allah Sarki Allah ya kareta Kada ya Huce akanta gashi su Abba sun Fita..! Sagir Da Mama suka Kalli juna Cikin Mamaki kafin Sagir ya kada kai yana Fadin"Imran baya Shan komai sai Taba Inteesar..Kuma Lafiyarsa Kalau haka Hallitarsa yake yana da Zuciya ce sosai wanda Wani Lokaci Baya iya Contolling din Fushinsa..! Mama ta Jinjina Kai tace"Koda ga Alamunsa..Yata ki Daina cemai yana Shaye Shaye kin ji ko..? Inteesar ta Gyada kai alamun Taji Sagir ya Mike yana Fadin"Ita kanta Taban da kika ga yana Shanta abaya bai ma Santa ba..Kawai yanzu din waniYanayi ne na Rayuwa ya kawosa Haka..Zaman da kikaga nayi kiransa nake jira ya Kirani yau zamu je kwallon Ball Daganan na gane Ransa yana bace ne zai Shiga Mutane in Ransa ya baci baya Kadaice kansa Saboda Kada Zuciyarsa ta Buga ya Gwammace ya Shiga Cikin Hayaniyar Daya Tsana Daya Zauna Takaichin Abun ya illatashi..! Inteesar ta Jinjina kai kafin Tace"Kai Shi dai Matarsa ta Shiga uku..Allah yasa ma ya Samu mai auransa Mama..! Daga mama Har Sagir sai da sukayi Dariya Mama Tace"In bai samu mai Auransa ba sai na bashi ke..! Inteesar ta Kwalolo ido kamar Taga Wani abun Tsoro Lokaci Daya Ta Dafe Kirji Tace"Ni kuma Mama..?wlh ko Narasa mai sona Sai dai na Mutu ba aure bazan Taba auran wannan ba Tabdijam. Allah na Tuba Mama bari wannan mganar kada yan Ameen su Amsa..! Ta karishe Fada Tana wani Dakuna Fuska Mama Dariya ta sakamata Shima Sagir din Dariyan yake ya Fice yana Fadin sai ya Dawo Mama ta Bisa da adawo Lafiya. Wannan mganar da Mama Tayi duk sai ta Damu Inteesar Bini Bini ta Tuna ta yanka tsaki afili Tana Fadin Allah ya Tsareni da auran wannan Mara Mutumcin..! Har tayi wanka Tayi Sallar mganriba ta Dibo Abinci tazo Tana ci Tana Tsaki Mama na lura da ita batace mata komai ba sai Dariyan Wauta irin ta Inteesar take Daga wasa sai ta Dauki abun da Gaske kadan taci Abinci sai ta Sha Tea kawai Saboda Zata kwanta ne. Washagari da Daddy ya kirata da Safe Abun na Ranta sai da ta bashi Labari Komai Daya Faru Harda mganar Mama ta