← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 190

Sashe 121

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka ya Rubuta kafin yabi Khalil wani dan Cafe inda suka Siya Coffea da lemu Anan Imran ya siya Sigari Khalil yaji mamakin ganin Imran na shan Sigari har sai da ya Furtamai Bai ce komai ba amsa Daya ya basa da cewa Life kenan.
Imran yasha Sigarinsa sosai,Saboda Tunda sukazo bai shafa ba,Har da Guzurinta yayi Khalil sai mamaki yake da Tsausayin Domin ya Tabbata Rayuwace ta maidasa haka abaya ko Kusa da ita baya zuwa.
Da suka koma gida basu ma Kowa bayanin inda sukaje ba Suma ba wanda ya Tambaeyesu..
Sai gashi bakin da zasu yi kwana daya sai gashi sai da suka kwana Hudu Tunda sai da suka jira Lurwanu ya Dawo da Iyalansa,Matan sa Biyu da yaya Bakwai irin auran Wuri ne ayi ta Tara ya"ya suka shige BQuaters Matar Buba da ya"yansu suka Tayasu gyara Komai har Cikin Gidan ma suka share suka Goge suka gyara kayan wasa kuma nasu Imran dasu Anni duk afito dasu wadanda bazasu Mori ba aka Zubar masu kyan suka Dauka sauran kuma zasu Sadakar dsshi ga Mabukata ana Gobe zasu tafi acikin Gidan suka kwana Saboda an gyara komai,Daga Gidan Dr.Isa Ali Argungun ake kawo musu Abinci Washegari Tun Safe suka Dauki Hanya bayan Abba da Dr Isa sun karbi Lambar juna haka ma Khalil da Imran sun Rabu kan in an nemesa zai gayamsa Insha Allahu.
Sai Cikin Dare suka iso kaduna anan suka kara kwana Sai Ranar Alhamis suka Dawo Kano,abun da ya bama Abba Da Daddy mamaki Har sukayi wannan Tafiyar Baffa Kabiru bai kira yaji Ya akayi ba sai dai sune suka Kirasa Daada kuwa Hankalinta kwance Koda yaushe Tana Waya da Malami Jininta ya Daina Hawa sai Dai ma yana ta kara Sauka ne.
Abba ya wakilta Yusuf ya Turama Daddy duka CV sa na Takardunsa Shi kuma ya Tuttura ma abokansa na nan Jami"ar Buk suka kuma Tabbatar da za"a dace Daman ana neman Wadanda suka kware kan Abubda Malamin ya karanta ya jira Lokaci kawai za"a kirasa.
Intee tafi kowa Murnan Dawowarsu daman Rashin ganin Imu duk ya Ramar da ita da kuma Gidan ba Dadi basu Abba Mama bata nan Taje Kaduna Bayan Tafiyan su Daddy Lagos jikin Inno ya Motsa sai sukayi mgana da Umma Maman ta Shirya tatafi Wajen kwananta uku kenan Daman Tun kafin tatafi suka dawo nan Gabadaya Saboda Taya Anty Safiya Zama.
Har ya dawo basu Hadu sunyi dogowar mgana ba sai dai sukan Hadu su kalli juna tayi mai Dariya shi kuma ya Hde rai ya Harareta,Sun Dawo Alhamis Ranar asabar da Daddare bayan sun gama Dinner gabadayansu Imran daman ba Zaman Dinner yake yi ba Tea kadai yasha sai gashi ya Fito Daga Daki ya Duka gaban Abba yana Fadamai Gobe yana so yaje Dukku.
Sun ji mamakinsa sosai Abba cikin mamaki ya kallesa yana Fadin"Dukku..?.
Kai ya gyada batare da yayi mgana ba Ya Yusuf dake Zaune gefen Abba ya kada kai yana Fadin"Dukku..? kodai Abuja mallam gayamana gaskiya..Kana son ganin Sajida ka Fake da Dukku..,,!
Kamar ya watsamai Ruwan Zafi haka yaji kallon Ya Yusuf yake yana auna in ba Domin shi bane wlh sai ya Duramai Ashariya Saboda Haushin mganarsa.
Inteesar ya kallah Dake gefen Munari da Anty Safiya itama kallonsa take Gabadaya Sai taji Ranta ya baci da aka ambaci Sajida kenan da gaske wajenta Zai je.
Kauda kansa yayi bai ce komai ba Abba na Dariya yace"Ai kamar tana makaranta bata dawo ba..Barsa kila ganin Kakarsa ne ya tasomai in yaje ya Dawo sai ya shirya yaje yaga matar tashi Lokacin ta dawo gida Tunda Ya Kabirun yace min suna Test ne..!
Har Abba ya gama mgana bai Dago ba.
Abba ya kallesa yana Nazarinsa kafin yace"Kwana zakayi in ka tafi goben..?
Dakyar yace"In Dare yayimin sai jibi zan Dawo..!
Abba ya kada kai yana Fadin"Allah ya kaika Lafiya Daada nada manyan Baki..!
Imran yaji Dadi da Abba bai kara Cewa komai ba ballatana ya Tambayessa me zai je yi wajen Daada yana Haararan Yusuf Dake Dariya ya Shige Dakinsa da Haushin Inteesar ta Kauda kai taki yarda su hada ido wai itana nan taji Haushi ne ko..?
Karamin Tsaki yaja yana jin Takaichi ya Riga yagama Shirinsa gobe sai Dukku waya ya Dauka ya Turama Intee Sako.

"Yayi miki kyau Tunda nine kike Turama baki kina kauda kai baki san ganina..!

Ba Dadewa ta bashi amsa da Cewa

"Eh din..Gobe zakaje kaga Amaryanka ina Ruwanka dani..!

Sai da ya waro ido Daya ga mganarta Dariya ta kamsa Yarinyar nan ta gama Rainasa cikin gatse yace mta

"Kamar kin sami ta Abuja zan sauka ko kina da sako wajen Amaryan tawa..?

Ya tura mata Sakon yana ta Dariya Har yana jin Sautinta yasan ya gama Kunno yar shagwaban kamar ya sani Dataga sakonsa sai da Zuciyarta ta Buga Saboda Takaichi da Kishi Cikin Tura Haushi ta Turamai.

"Ka gaisheta..Ango mijin Amarya..In kaga Nawa Mijin ka isar mai da Sakon i Miss Him Khamis Kabir Dukku nake nufi.."

Ai sai nata yafi Zafi Daya sakon nan kamar yayi Bindiga kiranta yayi taki Dauka sai yaji kamar Zuciyarsa Zata Fito Saboda Kishi Wai Mijinta..? Lalle nema to ba sai ya zama mijin nata ya gani ba haka yake ta Fada yana Sakin Tsaki.
Itama chan bangaranta haka tayi ta jan Tsaki tana kunkuni ita kadai Daga Karshe ma barin Falon Tayi,Ta shige Ba wanda ya Lura da yanayinta sai Munari ga Dariya ga Tsausayi..
Tana shiga Daki Ta Fada kan gadi ta saka kuka ranta na kuna Afili ta Furta"To ni ina ruwana ya ma je su Tare tare achan babu Abunda ya Dameni..!
Take Fada Cikin tura Haushi Lokaci Daya ga Hawaye Munari shigowarta kenan taji Abunda Intee ke fada Ssi ta bata Tsausayi bata nuna mata taji ba ta Basar ammh Tana Lura da ita bata wani samu barci ba Bini bini ta juya ta saki Tsaki shi kanshi Imran din Rabi da Rabi ne barcin nasa kowa ya kwana da Takaicin kowa.

*Shakira*
3/22/22, 23:15 - Ummi Tandama😇: *GMB2🅿�12*

*Wannan Littafin na kudi ne don Allah kada ki karanta in har kinsan baki biya ba N300 ne kachal kan wannan acct din 0552179550 Gtb ku sani ku kara Sani Mace mai aji mallakan komai nata nakeyi bata jiran abun Sata 09069067488*

Da garin Allah ya waye saboda ita da Safe yazo ya Tsaya a Haraban gidan Saboda yasan suna da makaranta yau da safe so yake ya ganta kafin ya tafi.
Sai dai duk yadda yaso Inteesar da suka Fito ya yusuf zai kai su kafin ya wuce wajen aiki bata yarda ta Hada ido dashi ba,Duk yadda yayi kokarin haka yaga Idanuwanta sun tasa alamun Tasha kuka jiya da Dadaddre..
Munari ce kadai ta gaisheshi Inteesar kuwa Mota ta shige Fuskarta ba Fara"a ko kadan ta maida ma kanta wani gefe Ran Imu ya sosu yaji ba Dadi yau shine Intee bata son ganin Fuskarsa abun is so painfull acikin Ransa.
Ya yusuf ne Daya fito ya gansa Tsaye Jikin Mashin dinsa ya Hade Hannuwansa Saman Kirjinsa kamar ko yaushe Kallonsa yayi yana Fadin"Yaushe zaka wuce ne..?
Kai Tsaye Imran yace"Yanzu..!
Yafada Kan Sa tsaye Kuma Duka Kallonsa naga Inteesar wacce ta maida kanta gefe batama yarda ta Dago ba ballatana su hada ido ba duk da ta Lura ita yake kallo kuma jikinta ya bata Wadandan Kafaffun Idanuwansa suna kanta ne.
Ya yusuf yayi sakake yana kallonsa Kafin yace"Yanzu..?kuma kake Tsaye anan ba wani Shirin Tafiya..?
Imran gajiya ma yayi da mganar Yusuf ya barsa yaji da abunda ke gabansa mana bai ce mai komai ba ya Taka zuwa Cikin Falon ko waige Yusuf ya Bisa da kallo kafin ya Tabe bakinsa sai alokacin Inteesar tabi bayansa da kallo Cikin Samun Sukuni da Salamar Dake Tattare da ganinsa din Munari na Gefenta Tana Lura da Komai acikin Ranta tace Allah Sarki Soyayyah..
Yusuf shima Shigowa Motar yayi ya Kunnata yayi Riverse suka Fice Daga Haraban gidan.

Suna Tafiya ba Dadewa Imran ya Fito Cikin Shirin Tafiya yayi shigar Riga da Wando Rigar Fara ce mai Dogon Hannu Tana da Layin Baki ajikinta Sai Wandon Jikinsa baki ya kamasa daga kasa Kadan kafarsa sanye Cikin Bakin Takalmi Sawu Ciki na Fatar Damisa,Ahannunsa na Hagu sanye da bakin agogon Fata na Kamfanin Rado Kan nashi yasha gyara,Bayansa ya Rataye da Jakarsa baka ta baya kamar ta yan makaranta Bawani Kure adaka yayi ba ammh ko sau Daya ka kallesa sai ka kara kallonsa Cikar Zatinsa baiwa ce Daga Allah kwarjinsa da Kyansa kuma Hallitace ta Ubangiji Duk Takamar mace da Kudinta da Iliminta in Imran ya Tsaya a gabanta ya Kalleta ido Cikin ido sai taji ta Raina kanta da Duk Abunda ta mallaka Maza kuma yan"uwansa Dole in suka kallesa sai sun kara kallansa sun kuma Tabbatar ma kansu Babban Goro sai magogin karfe.
Ko afitowar da yayi Abba Dake kan Dining yana karyawa Sai da ya Dago ya kallesa acikin ransa yana Kirari ga Allah mai gagara Misali da ya Hallici Imran a yadda yake,Safiya ma Dake Zaune afalo bayan ta Rako Yusuf ne ta Jabe anan tana Hutawa ta kasa karisawa Shashenta Cikinta har ya Fito Domin ya Shiga watansa na Biyar,Itama Dake Zaune sai da ta kallesa ta kuma Jinjina Kwarjinsa Ya gaisheta ta amsa mai Cikin Sakin Fuska yana gaisheta Wani Lokacin In suka Hadu Gab da gab ammh fa baya Binta ya gaisheta in sun hadu shima din yana Cikin Mood mai Dadi in Ransa na bace kuwa baya bi ma ta kan kowa.
Chapter 121 · 0% Book details