Sashe 184
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da Sajida ta shafe Sati Biyu a asibiti kafin a sallameta ta dawo gida bayan taji Sauki sosai ta fara maida Jikinta ganin Rayuwa tayi kyau Mami Asma'u Ta gyara Halinta ta Rumgumi ya"yanta ta Fahimci inda ta Gaza yanzu da Ra"ayin Baffa Kabiru da duka Umarninsa take aiki. Abba da Daddy da Baffa Kabiru sun je Dukku sun zauna da Daada mganar auran dake gabansu Daada tace ita nata Fatan alheri ne da addu"a Mgana da Zartarwa Duka nasu ne sun Taru sun Tsaida Lokacin Bikin gabadaya nan da Wata Hudu kuma Duka a Dukku Za"ayi in an gama Biki araka Amare Gidan zasu zauna da Mazajensu. Mganar Abba da Mama kuma Daddy yaje Har gida yasamu Inno da Mallam Babba kan mganar su kuma suka bashi Wuka da Nama kan lamarin Kawu Salisu yace ko shi ya isa ya Zama Waliyin Mama saboda Haka sun Amince Dari Bisa Dari indai Mama ta Amince Daddy ya Kira Abba yace yaje su gama da Mama. Abba bai iya watsama ya"yansa da yan"uwansa kasa a ido ba yaje Har Gida ya Samu Mama suka Tattauna Mama bata isa taki Abba ba Domin wani Bango ne Allah ya Aiko mata dashi Tun bayan Rasuwar Mahaifin Sagir bata karbi Sadakinta ba sai da ta Samu Baba manu ta Fadamai komai Domin ya Chanchanta kanin Mijinta ne na baya ammh bayan kasa ta Rufe idon Tasiu ya kula da Rayuwarta ita da Sagir Shima Lokacin Dayaji Abba amtsayin Wanda zai auereta sai yafi Mama Nuna Murnansa da Amincewarsa Dari Bisa Dari Mama Taji Dadin haka Daman game da yan"uwanta bata da Damuwa Umma Tafi kowa Murna da wannan Hadin. Baffa Kabiru shi ya biyama Abba Sadaki kamar yadda yayi alkawari Naira Dubu 100,Dakyar Mama ta yarda ta amsa da tace yayi yawa sai dai an Rage Zata karba sai da Baffa Kabiru yayi mgana da ita a waya kana ta yarda ta amsa An Fara Daura auran Mama da Abba anan masallacin Kusa dasu inda suke Salla a wata ranar Jumma sai aka bar Tarewar Lokaci Daya dana su Munari Baffa Kabiru ya karban ma Abba Aure Kawu Salisu ya zama Waliyin Mama Aranar Bakin Imran da Sagir Dana Yusuf yaki Rufuwa Allah Sarki Rayuwa Allah ya jikan Anni da Gafara Mama tana Tare dasu Umma da Maman Nasara, Da Mami Asma"u da suka zo Tare da Baffa Kabiru da Khamis sai Mommy maman Anty Safiya duk ba Taro bane ammh Mama taci gayunta an kuma yi abinci suma chan gidan su Inteesar nata nasu Shagalin da su Anty Safiya da Munari da Hafsah da Tasleem da Nasara duk sunsamu zuwa suma sun yi kayattacen Girke girke da Ababen sha su Abba da yan"uwansa suna Haraban gidan suna cin Abinci suna ta Fira su kuma matansa suna Falo suna ta cin Abinci suna Hira Harda Sadam yazo Aneesa da yara suna Cikin Shashen Anty Safiya yan matan ba wacce ta Leko Tun bayan da suka Cika gabansu da abinci suka bace duk kuwa da yarda Samarin nasu suke ta Tura musu sakon su fito suna son ganinsu ba wacce ta Leke sanin Halin Wanda ke wajen Imu Domin Tun suna Kawo abinci yake ta Hararansu yace suyu su gama su bar nan Wajen. Khamis ne yaje ya Duka ya Nemi Izinin Babban Yaya na yana son ganin Munari Imran ya Hura hanci kafin yace an bashi,izini ya tashi yana Dariya ya Kira Munari ta Fito suka Kebe Sagir ne yace wlh bazai nemi Izinin ba Imran yace ba kuwa zai ga Hafsah ba yace bai isa ba Imran yace To sai ya gani. Duk da Sagir ya Kirata Tana Fitowa kallo Daya gogan yayi mata ta Koma Ciki da Gudu Sagir ya Saki baki su Yusuf na Dariya Imran ko ya Hade Rai Zaginsa yayi bai damu ba sanin ai Sagir ba Girmansa yake gani ba Khalil ya Kira ya Fadamawa shi kuma yace ya Kyalesa na Lokaci in suka yi Ciki da kannin nashi ya isa ya kafa musu Wata Doka ne,Dole ya Kyalesu suyi yadda suka ga dama. Imran bai yi magana ba Sanin Halin Khalil in suka Hade da Sagir sai Allah,Shi da yake da Sauran mai Cutar Xuciya Kafin auran Jinya zai tayi ko nacema yana kanyi Tunda Sajida Har yanzu Tana agida Karkashin Kulawar Likita Gefe Daya Khalil na bata Kyakyawan Kulawan Datake kra Taimaka mata batare data sani ba ta Shaku dashi sosai Kamar sun Dade da Sanin juna. Washegari kowa zai koma Inda ya Fito Da Daddare Da Imran yace Intee ta Fito su tafi sai ta yo mai gayyar su Munari da Hafsah da Nasara zasu Bita su kwana agidansu da Imran yaga haka Ransa ya bace har Intee ta koma su kwana Tare Ita bata gane ba Tana ta Murna batasan Talala yayi mata ba Washegari da baki suka Watse suka koma Gida sai da ta Raina kanta Daya Damketa sai da ta koma magiya da Ban baki kana ya Ragamata Hukuncin ta kenan na Hanasa Shagali Daran Jiya. Inteesar sai dai Tura baki bata ta tacewa Daman haka yake mata yace Tunda bata son Fada to Hukuncin Daya Dace da ita kenan ba Duka ba Zagi zai ladabtar da ita Hankalinsa kwance. Ta kowani Bangare sun Fara Shirin wannan Gagrumin Bikin Duk da basu yi wani Wahala ba ko Daura ma kai Nauyi ba Dukkansu Sadaki Kadai Baffa Kabiru ya Zartar Domin shine kamar makwafin Alkali Dukku marigayi Allah ya basa Girman kuma ya karba,Mami Asma"u ba Zama Zata aurar da manyan ya"yanta Guda Biyu sun Hade kai da Umma Kamar yadda kawunan Mazajensu yake a Hade Mami duk ta Zubar kawayenta ta kama Umma Hannun Bibbiyu ta Fahimci zama da Mutanen kwarai yafi Zaman da Mutanen Banza. Wannan Karon an Raba Daddy shi ya Dauki Nauyin yima Amare Jeren Daki Baffa Kabiru kuma Baban angwaye shi ya Dauki Nauyin yima Duka Zaratan Mazan akwatuna aure Da Sagir da Khalil da Khamis Harda Abba Wannan karamincin yasa Dr.Ali Argugu ya taso Tun Daga Lagos Har Kano yayi ma su Abba Godiya Domin koda Khalil yaje musu da Labarin Chanji Daga Munari zuwa Sajida basu ce komai ba Sanin Daman ai Matar Mutun kabarinsa kuma wani baya auran Matar wani daman chan Allah ya Rubuta Sajidan da ita Za"ayi... Mama ma Tana ta Godiya Baffa Kabiru yace bayason Godiya Da Khamis da Khalil da Sagir Duka Dayane a Wajensa. Imran dai na gefe bai Zake ba ya Kama Girmansa na Babban Yaya Khamis ne kadai ke basa Girma yana Shawara dashi banda Sagir Daya gama Rainasa gwara ma Khalil yana Ragamai Tunda dai yana Kularmai da yar kanwarsa Sajida wacce kusan koda Yaushe yana Kiranta yaji Lafiyanta ya Dauki alkwarin Kula da ita na Musamman acikin kannensa ba Domin in ya aureta bazai yi adalci ba Daya Aurota ya Hadata da Inteesar to ya kwana da sanin baza"a zauna Lafiya ba,Rigimar Inteeear ba Ko yanzu ma Bata kaunar Taga yana Mganar Sajida ko Taga ya Kirata a waya yanzu Zata Chanzamai fuska sai ya koma yana Lallashinta Tana da Kishi sosai,shi kuma bai iya Hayaniya ba Ballatana ya jawo ma kansa aiki Masu Shirin Shagali su Intee ce ana gaba gaba sune manya. Sajida a Lagos Zata zauna Gidan Khalil,Hafsah kuma agidansu Zata Zauna Inda Sagir yasa aka Fara Bugesa za"a Sauyamai Samfarin Ginin Zamani Falt mai kyau da Tsari Tunda Mama Gidan Abba Zata koma Shima Abba yasa an Fara Gina wani kayattacen Shashi Daga gefe nan Shashen Gabadaya zai barma Yusuf ne. Khamis kuma porthercourt Zasu Zauna Domin ya samu Transfer Daga Anambara zuwa Porthercourt,chan zai Tafi da ita ammh sai sun yi Sati Biyu a Abuja,Ta kowani bangare Shirin Bikin ake Gudanarwa,ba kama Hannun yaro Dayake Allah ya Rufa asiri sai komai yayi Daidai ba wata Mtsala sun Tsara zasu yi Events dinsu a Dukku zasu yi Fulani Day,sai Lonching,sai Matan da zasuyi Walima. Inteesar duk ta Fara Damuwa Munari Zata tafi ta barta ita kadai a makaranta da garin gabadaya,Saboda Chan Khamis zai nema mata makaranta in tasamu Transfer ta Cigaba Saboda Shirye Shiryen Bikin Har sun Fara wasa da karatun nasu Dayake suna Second Semester ne na aji Biyu sai da Imran yayi musu Fata Fata kana suka maida Hankalinsu. Bangaran gyaran Amare kuma Inna Maimatu da Inna Bintalo suka Karbi Mangaran suka aika da Jarkunan mganin Sanyi da Gumbar mata Abuja da kano Da Dutse Munari da Hafsah da Sajida duk sukace su fara amfani Dashi Umma ma ta Dakema Mama kan sai ta gyara itama Tana ta Korafin wai Ta girma wannan aikin yara ne Umma tace sai fa ta gyara ita da Maman Nasara suka Hade mata kai suna Fadin ai ko Manyan ma suna son agyara musu suji Dadi Dukkansu Dole ta Fara karban gyara Daga garesu Domin kaunace ta kawo Haka. Sagir da Taimakon Filinsa daya Gada ya Saida ya Fara aikin Ginin an Sauya Fasalin Gidan Gabadaya an Fitar da kayattacen Falt mai Dauke da 2Bedroom da falo da Kitchen sai wani karamin Shashe mai Falo Daya da Bedroom Daya,Sai Haraban Gidan da Get domin Shiga da Mota Tunda ai Cigaban Rayuwa ake nema sai Daga Shagonsa ya Bigeshibaka kara Fili aka Bude Babban Shago mai girma ya Bude Kofa ta Waje data Cikin Gida Saboda yana so nan gaba ya kara Kekuna Da ma"ikata Tunda dinkin nan Dashi Yake Rufama kansa asiri yau ko ya gama Makaranta ba Lalle ne ya Samu aiki da Wuri ba Imran ya Bashi wannan Shawaran Domin shima yayi ma Sagir alkawarin Hada Hannu Dashi Wajen Bunkusa Kasuwancinsa sosai. Wasa wasa Biki nata Matsowa Dama kuma Hausawa sunce Duk Abunda aka Sakama Lokaci sai yazo gashi yau Bikin ya Rage Saura Wata Daya Tuni Ginin Abba Shima ya kamallah Gabadaya an sauya Fasalin Gidan An Hade Shashen gabadaya An kara Fadada Bangaran Yusuf da Anty Safiya Sannan anyi bangaran Baki Daga Ciki Daga Chan Gefec kuma Kayattacen Falt din Abba ne mai Dauke da 3bedroom Da Falo Guda Biyu Daga Bakin get kuma an Fitar ma Iro megadi Dakuna Biyu Ciki da Falo Shida Direban Abba Tunda duk nan suke kwana an Sauya Fenti Har da Duka Sabbi kayan Cikin Gidan Abba yace baya Bukatar komai sai