← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 190

Sashe 11

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Cikin Shirinsa na Fita ya Fito Daga Dakinsa Cikin Shigar riga da wando Black and white,na kamfanin Armani sai kafarsa sanye Cikin Bakin Rufaffen Takalmi na Fatar Damisa Sai hannunsa Dake daure da Bakin agogo na Fatar damisa mai kyau da yarari,Kwantacciyar suman kansa tasha gyara ta kwanta ta karama Fuskarsa kyau da Annuri Sai Bakinsa Wanda Bakin hayaki ya Fara mai dashi Duhu hakan sai ya karamai kyau da wani Haiba.. Fuskar nan nashi a Hade babu Fara"a ko kadan Key din Mashin Dinsa ne a Hannunsa yana Dakawa Sanda ya Fito Falon kamshin Turaransa na Man Daya saba amfani Dashi ya Fara ma Yusuf da Maimuna Sanar isowarsa Cikin Falon. Ya yusuf na Zaune kan Daya Daga Cikin kujerun Falon Yana makale da waya a kunnensa yana mgana kasa kasa Cikin kwantar dakai Daga gani Da Safiya yake waya ko da wata Macen da Zuciyarsa ta gama yarda da ita. Maimuna kuma Tana Wajen Dinning area Tana jera Warmers da Filets din Data kwaso Daga Kitchen Tunda ya Fito ta Kuramai ido Ganinsa kamar kullum Ba Fara"a da Anuri yasa da Sauri Ta Daga murya Tana Fadin"Barka da Fitowa ya Imu..! Bai amsa mata ba Sai ma wani kallo Daya Bita dashi kafin ya Dauke kansa Ya Juya ya nufi Dakin Abba Bata damu ba sanin Halinsa baki ta tabe kawai ta juya zuwa Kichen ta Dauko Ruwa da Kofuna,Yusuf kuma Dake waya bai katse ba ya bishi da kallo Har ya Bude Dakin Abba ya Shiga da yar Karamar sallamarsa Ciki ciki kamar wanda akace yayi ta Dole. Har Gaban gadon da Abba ke kwance ya karisa cak ya Tsaya yana Kallon Abba Dake kwance Sambal akan gadon da ya zame masa Kamar wani Maginjini ko nace abun Dogaro ya kwana akai ya tashi akai ya kuma karishe wuninsa akai sanye yake da Farar Jallabiya a jikinsa Gashin Bakinsa da gemunsa ya cika alamun yana Bukatar a Rageshi Dogon Hancinsa ya kara Fitowa da Kyakyawan Fuskarsa ta Fulanin asali. Kuramasa ido Imran yayi yana jin Taruwar wasu Hawaye a kwarmin Idanuwansa Durkusawa yayi agaban gadon yana kallon Idanuwan Abba suna Lumshe alamun ya samu natsuwa Cikin Barcinsa. Hannunsa ya Riko Cikin Nashi yana Faman kokuwa da Numfashinsa Wasu al"amura da suka Shude suna kokarin Dawowamai Daki Daki yana Tuna Abba da Sadaukarwarn sa kan Iyalinsa da yan"uwansa ammh yau Dalilin Wata kaddara Kalli Halin Daya koma. Rauninsa ne ya Fara Bayyana Kamar zai yi kuka ammh kuma bai yin ba yayi maza ya Matse Hawayensa suka koma Lokaci Daya ya Mike Bayan ya saki Hannun Abba Yana Fadin"Allah ya Baka Lafiya Abba..! Daga Haka ya juya ya Fice Daga Dakin da Sauri Cikin Sassafarsa Daya saba akoda yaushe. Wannan karon Munari bata Falon Sai Yusuf kadai Dake kan Dinning yana cin Abinci Fitowar Imran Da kokarin Fita Dayake yasa ya Daga murya ya kirasa "Imu...! Tsayawa yayi Lokaci Daya ya waigo yana kallonsa abincin gabansa ya Nuna mai da ido kafin yace"Ina zaka kuma ga abinci Munari ta gama..? Yamutsa Fuska yayi kadan kafin yace"Am ok..! Ya juya zai Sake yunkurin Fita yaji Yusuf din na Fadin"Wai ina Zakane da Daran nan kake ta wannan Uban Saurin..? Kodai kodai..? Yafada Cikin Sigan Zolaya Jin haka yasa Imran ya juyo yana kara Hade Ransa yace"Kodai What..? Yusuf na kai loman Shinkafa da Miyar da Munari tayi yake Fadin"Ko dai Zence zaka ne..? Imran ya wani Kallesa Sheke sheke kafin yace"Menene kuma wani Zence..? Yusuf yace"Nufina Tadi zaka je wajen Budurwan ka Dakayi..Domin wannan gayun ina hasashen nata ne..! In ba domin ya yusuf bane Ashar yaso ya Dankara mai sai kuma ya Fasa ya karkace kai bayan ya Tusa Duka Hannuwansa Cikin Aljihun wandonsa yace"Abba nata barci ya ko tashi yayi Sallah..? Ya kauda Hiran Saboda bayaso Tayi tsawo Lokaci Daya kuma yana Fito da hannunsa agogon Dake Tsitsiyan Hannunsa yake Dubawa. Yusuf ya kada kai kawai yace"bai yi ba..Kasan Dr.Ya sauyamai mgani wannan karon so akwai masu saka Barci sosai..Zuwa 9 insha Allahu zai Tashi da kansa.Ammh fa bazan fasa Fadin Zence zaka ba..! Ya karishe Fada yana kunshe Dariyansa Lokaci Daya yana Tsiyaya Ruwa a glass Cup yasha ya koshi kana ya mike ya Zari Tissue yana goge bakinsa kafin ya Fara takowa Tsakiyar Falon. Yana kallon Fuskar Imran din wanda yayi shuru kawai yana Kallon Yusuf din kamar ya Makeshi haka yaje ji..? Shi Imran ne zai je Tadi ko menene ma yace..? Allah ya Tsareshi.. Karamin Tsaki yaja kafin yace"Ni Imran ne zan je Zence kace ma kofar gidan wata yarinya..?Ni..Over my Death Body Wlh..! Yafada yana wani mele baki Yusuf ya karosa gabansa Lokaci Daya yana Fadin"Common Kada ka Cika baki..Sai dai in bazakayi aure ba in ko Zakayi Dole sai ka Sauke wannan Ra"ayin naka kaji..! Imran yace"Saboda me..? Nifa Shiyasa bana son Hada Shirgina da mata..Kasanni bana son Raini ko kadan su kuma da sunga kana Sakarmusu Fuska sai Raini ya Shigo Ciki..Ni aure bai Taba Zama Dole gareni ba sai don yana Sunnar ma"aiki in ma ya Zama Dolen zan yi auran sai na Ga wacce ita take sona zata iya Zama Dani tayi Hakuri dani kuma In har taji Tagani Shikenan Fine ammh ni kam bazan iya Lalacewa gaban Mace ina Rage Murya ba Allah ya tsari Imrana..! Tunda ya Fara mgana Yusuf ke Dariya har yana zama kan kujera Ganin haka yasa Imran ya juya kawai ya Fara Tafiya batare Dayace wani abu ba Gabda zai Fice Daga Falon Yusuf yace"Shikenan Imran Abubukar Malami We shall see..! Cikin son Tabbatarwa ya juyo ya saki wani Mirmishi kafin yace"We shall see..! Daga haka ya Fice Daga Falon yana sakin karamin Tsaki ganin Bata Lokacin Dayayi alhalin shi ba Mutum ne mai african Time ba. Mashin dinsa yaHau ya kunnata Lokaci Daya yayi Hon Iro megadi Dake kan Bencinsa zaune yana Dafa Shayinsa ya Tashi da Gudu ya Bude get din Imran ya Fice da Gudu Baki Iro ya Rike kafin yace"Nidai Allah ya kawoni gadi Wani Gida..Gidan da ban taba ganin kamar sa ba.! Yafada Lokaci Daya yana maida get din ya Rufe ya koma ya Cigaba da Fifita Rushin Dake Cikin karamin murhin gawayin Dake gabansa mai Dauke da Karamar Butar shayi yana Dafawa. Yana isowa kofar gidansu Sagir din yaji wayarsa na kuka,Kafin ya Cirota Daga Aljihu Sagir ya Bayyana gabansa Cikin Harara yace"Karfe Takwas din kenan..? Kasani na Fito ina jiranka kamar wani yaron aiken ka..! Karamin mirmishi Imran yayi yana Fadin"To da wanene..? Mallam Hau muje bana so mu yi Dare sosai..! Sagir na Hawa mashin din Lokaci Daya yana Fadin"Dare na nawa kuma..Ai mun gama yinsa..! Imran dai bai kara mgana ba suka Dauki Hanya Sagir ne ke ta maganarsa yana Fadama Imran din ya kira Baba Manun yace maizasu zo,Imran Yana Tuka mashin din yace"Waya aike ka..?. Sagir yace"Bangane ba..? In mukaje bai dawo daga gareji bafa..! Kai tsaye Imran yace"Mu bisa chan..! Sagir yace"Mganar bata kamata ayita achan ba.Agidan dai ya Dace..! Imran yace"Naji sarkin Tsari..Kamin shuru kasan na tsani ina Tafiya mutum na min Surutu a bayana..! Sagir ya Gimtse bakinsa bai kara mgana sai da suka isa anguwan su Baba manu dake mandawari Road,Daman Imran yasan gidan Domin In Sagir zashi Wani Lokacin Tare suke zuwa da Imran din sai dai bai taba Shiga Gidan ba sai dai ya Tsaya Daga waje Sagir din ya Shiga ya Fito Shima Baba Manun ya san Imran din Abokin Sagir ne sau Daya suka Taba Haduwa Har ya gaishesa shima Sagir ne ya Dinga Taka kafar Imran din yana mai in kiya Daya gaida Baba Manun. Akofar gidan suka Faka mashin din kafin Sagir ya kalli Imran Daya Coge gefen mashin dinsa yace"Shiga fa zamu yi..? Imran yace"Saboda mene.? Ya fito waje mganar bamai tsayi bace! Sagir yayi tsaki ya wuce yana Fadin"In kaga dama kazo mu shiga in kuma baka ga Dama ba ka koma! Daga haka ya saka kanshi Gidan ya bar Imran din nan Tsaye yana kallonsa Kamar bazai Bishi ba kuma komai ya Tuna sai ya Daga kafa ya Rufama Sagir din Baya. Da Siririyar Sallamarsa ya Shiga Sagir da Inna kaltume matar Baba Manu suka amsa,Wanda ke Zaune kan Tabarma kusa da Sagir din mgana yake a waya. Kamar Imran ya juya sai kuma ya Tuna Abunda ya kawosa yasa yayi karfin gwiwan karisawa ganin yadda Daga Baba Manun har Inna Kaltumen suka Sakarmai ido suna kallonsa Dayake akwai Wutan Lantarki Haske ya gauraye Tsakar gidan. Daga nesa ya Durkusa Kamar a Dofane yana Gaishesu sau Daya ina Wuni? Inna kaltume ne ta amsa mai Cikin Fara"a Tana Tambayashi Mutanen gidan Dakyar yace Lafiya lau yana kauda kai itama ganin haka bata mtsa ma kanta ba Ta juya kan Sagir Tana Tambayansa Mama yace Tana gaishesa Daidai Lokacin da Baba Manu ya gama waya ita kuma Inna Kaltume ta mike tana cema Sagir azubo Tuwo yace a koshe yake ta kalli Imran wanda kansa ke kallon gefe yana jinsa kamar a Takure tace koshi bazai ci ba..?.Sagir ya kallesa kafin ya girgizamata kai yace mata Ta barshi kawai bata ja da Nisa ba ta Shige Daki ta basu waje suyi mgana. Juyawa Sagir yayi yana gaida Baba Manu wanda da ga kanshi Zaka san sun Hada Jini da Sagir Saboda Zubinsu iri Dayane da kuma yanayin Dogon Fuskarsu Amsa mai yayi Cikin Fuska Lokaci Daya yana Fadin"Ina Ita Aminan..? Ina fatan lafiya kalau take..? Kan Sagir na kasa yace"Eh Baba Lafiyanta Kalau tace a gaisheka..? Yana kallon Imran yana Nazarinsa acikinsa Ransa yace"Ina amsawa Daman gobe nake cewa zan leka mu gaisa kwana Biyu! Sagir ya gyara zama yana Fadin"Baba ga abokin nawa danace maka zamu zo Tare..Imran yana so yayi mgana Dakai..! Baba Manu ya maida Hankalinsa kan Sagir kafin ya kalli Imran yana Fadin"Topha dan Saurayi in ce dai ko lafiya..?ba wani abu Sangirun yayi maka ba..? Imran da sai yanzu ya kallesa ya Girgiza kai yana Fadin"A'a ba mganar Sagir bane..! Baba manu yace"To to..Ina jinka..! Sagir ne ya kalli Imran din yana Fadin"Ka cire Takalminka ka Hawo kan Tabarman mana Imu..! Bai kallesa ba ya gyra Tsugunnonsa yana Fadin"Nan ma is ok..! Baba manu dai bai ce komai yana ta Tunanin wata mgana ce
Chapter 11 · 0% Book details