← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 190

Sashe 60

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Imran na Sawo kansa Cikin Falon suka Ci mummunar karo da Inteesar Da Sai da Kafadarsa ta Daki kanta Tunda ya Fita Tsawo,bata san dashi ba da Karfinta ta Jefa jikinta Munari na Binta zata Rakata Haraban gidan,Kafadarsa ba kadan bace kuma Shima da Sakin jikinsa ya Sawo kansa Falon baisan da ita ba Shiyasa ya Bangajeta Bangazan da ta kasa Tsayuwa da Kafafunta tatafi Luu zata Fadi ta Gefenta da Wani Zafin Nama ya Saka Lallausan Igarman Hannayensa ya Tarairayota ta Fado kan Kirjinsa da karfinsa Har Karan Hancinta da Kirjinta suna Dukan Faffadan Kirjinsa.
Munari Dake tsaye har ta Sadakar Inteesar ta gama shan kasa,sai kuma ta kame gefe Daya tana kallon Inteesar Rike hannun Ya Imran hannayensa Zagaye da Kugunta Yayi mata Riko sosai.
Inteesar abun ya Faru cikin Lokaci kadan ne shiyasa bazata iya Tantance komai ba,sai da taji wani Ingarman Namiji mai Zatin jarumta yayi Saurin Tareta kuma ya Tallafota zuwa jikinsa Maida Nunfashi take sama sama Inteesar akwai tsoro ta Tsorata da Fadin da Zatayi yasa ta Saka Hannayenta Guda Biyu ta Rike Rigar Imran dashi Idanuwanta a Lumshe Tana maida Numfashi.
Imran kuwa wani Sanyi yaji yana Shiga Jikinsa da Zuciyarsa wanda Tunda yazo Duniya bai taba jiba ba..Kirjinsa Duka kawai yake yana Fat..! Fat..! Da karfi kamar wanda yaga wani abu tsoro..
Fuskar Inteesar ya Kurama ido Wacce ke kan kirjinsa Tana Rirrike dashi Da karfi,Kallonta yake kamar yana son ya Haddacr komai na Fuskarta Kada ta bacemai,Yana jin kamar Rikonta wani Salama ne da Farinciki awajensa kamar in ya Saketa zai Tagayyara ko zai Lalace yana jinta acikin jikinsa kamar Wani gafara ne Daga Allah.
Abba ya Bude Kofar Dakinsa ya Fito Dauke da karamin Littafin azkar Jikinsa Sanye da Wata Farar shadda Dinkin Riga da wando har da Hula.
Ganin Imran da Inteesar a wannan yanayin sai da gabansa ya Fadi Cikin Azama ya Karisa Cikin Falon yana Fadin"Kai Imran Lafiyar kuwa ka Rike Diyar mutane..,?
Yafada da dan Karfi wanda ya Dawo dasu Dukkansu Cikin Hankalinsu.
Inteesar jin muryan Abba asama yasa ta Dago Tana kallon Fuskar wanda ke Rike da ita ai Tana ganin Imran taji wani Yam! acikin jikinta da Sauri ta Kwace Jikinta Ta mtsa baya tana Maida Numfashi
Shi kuwa Daman jikinsa ba Karfi ga Kasalan data Rufeshi shiyasa Inteesar ta iya kwace Jikinta..
Da Lumsassun idanuwansa ya Kalleta Kafin ya juya ya kalli Abba batare da yayi mgana ba ya Fara tafiya zai shiga Dakinsa,Abba ya Daga baki yace"Kai IMRAN ya ka nan ya ina maka mgana kana wucewa..?
Yafada cikin bacin rai baya Fatan ace Ya Doke yar Mutane ne Juyowa yayi yana jin mganar tamai nauyin ya Fada Munari ce tayi Saurin cewa"Abba Karo sukayi da Intee...Basu ga juna ba Shine zata Fado ya Rikota..!.
Ajiyar rai Abba ya Sauke Kafin ya Maida kallonsa kan Inteesar Dake Jin wani iri acikin jikinta yace"Sannu Baki dai ji ciwo ba ko..?
Inteesar Dakyar ta iya Bude baki tace"A"a Abba..Sai da safe..!
Tafada tana Juyawa,ta gefen ido Take kallon Imran yana Shiga Dakinsa Abba yanata ta gaida Mama,Ta fice Munari ta Bita abaya suna Fitowa Munari ta Riko Inteesar tana Fadin"Kai Besty kinga yadda kikayi ajikin Ya Imu..? Na Rantse har ga Allah kunmin kyau kamar a Indian Film din nan irin Jarumar zata Fadi Jarumin yayi AzAman rikota ta Fadomai..!
Ta Kariashe Fada tana Dariya Inteesar ta Harareta Lokaci Daya tana Tuno yanayin data Fada kan kirjinsa sai da jikinta ya amsa domin Bayan Muharramanta wani namiji bai Taba koda taba Hannunta ba sai yau wanda Komai ya Faru bisa Rashin sani.
Ganin taki mgana yasa Munari ta Cigaba da Fadin"Nayi mamakin Ya Imu yau..? Kun bala"in dacewa kamar ace ku din Couple ne..!
Da sauri Inteesar tace"Da wa..?Allah ya Tsareni baki man fatan kwarai ba..Indai na auran wannan Muradadden yayan naki ne..!
Munari zata kara mgana Inteesar ta Dakatar da ita da Fadin"Kinga ni kyaleni..Nagode Daya Taimakeni Daga Faduwa kawai..Sai da safe ki koma gida malama..!
Munari ta kada kai Tana Fadin"Daga waasa..? Allah baki Hakuri..!
Inteesar ko kulata batayi ba ta wuce Munari ta Bita da kallon Cikin Rashin jin Dadin yadda ta Bata mata rai ita Har ga Allah waasa take mata kada kai Tayi ta koma Cikin gida Tana Fadin gobe zata bama Inteesar hakuri banda Abunta Ya Imu ai ba Aure ma yake da Ra"ayin yi ba Ballatana wannan mganar ta Dameta.
Inteesar har takai gida ta rasa yanayinta Kowani Dakika abunda ya Faru ne yake Dawowa mata Kuryan Daki ta Shige ta Fada kan gado ko Hijabin Jikinta bata iya Cirewa ba,gabanta sai Fadi yake Data Runtse ido sai ta ganta Rike da Imran Kirjinta yana Saman kirjinsa Runtse ido Tayi a Fili ta Furta"Shikenan Mara Mutuncin nan ya gama dani..!
Take fada tana kara jin wani Takaici Da ta Tuna abun sai ta Saki Tsaki kuma abun yaki bace mata acikin Ranta da Zuciyarta Har Mama Sai da ta Tambayeta ko Lafiya jin yadda Lokaci Bayan Lokaci take sakin Tsaki Sai ta sanu kanta da Boye abunda ya Faru tace bakomai.
Bangaran Imran kuwa ya kasa Gane Yanayinsa In ya Runtse ido Sai yaji Fadowar Inteesar a Kirjinsa sai gabansa ya amsa Yana jin alokacin Yanayinsa ya sauya kamar bashi ba yana Tuna yadda ya Saka Hannayensa ya Zagaye kugunta dashi,yana kwance da Silasin Dare ya kasa barci Ya Busa Sigarin nasa Ammh duk a banza Yana kwance yana Tunani kafin ya Murmusa afili ya Furta"Kugun nata ma D'An karami ne kamar yadda take karama da ita..!
Yafada yana Bin hannuwansa Daya Daga da kallo.
Kafin ya kara Juyawa yana Yin Filo da Hannayensa yace"Sai Rashin kunya kuma..!
Yafada shi kadai kuma yayi Mirmishi kamar wanda ya zare,Rufe Manyan Idanuwansa yayi Yana Fatan barci ya Daukesa sai mai gabadaya Fuskar Inteesar ne take mai Hazo da Gilmawa acikin Rufewar idanuwansa,Sai Mirgina yake yi yakasa Barci in ya Bude Idanun nasa ba Fuskarta yake gani,Mikewa Zaune yayi Cikin Duhun Dakin Sai dan Hasken Dake shigowa ta Labulan Dakin Dayake Dagawa ta Window.
Kansa ya Dafe yana Fadin"meke Shirin Faruwa dani ne..?taya ya ko ina nake ganin Fuskarta..?
Kodai ba Mutum bace Aljanna ce..!?
Wata zuciya tace"Mutum ce ba Dazu kaga Kafarta ba..Bata da Kofato..!
Sai kuma ya Saki Mirmishi kafin ya koma ya kwanta Ringingine yana mai Dora kansa saman Hannayensa acikin Ransa yace"Koma aljannace...Ni Imran nafi karfinta..!
Daga haka barci ya kwasheshi Dakyar ammh Abun mamaki masu cike da mafarkin Inteesar
Chapter 60 · 0% Book details