← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 190

Sashe 17

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tunda suka shiga cikin makarantar ake ta Cuku cuku anan sukayi sallar azahar da La"asar suka kuma ci Abinci da Taimakon Abokin Daddy Inteesar ta kamallah registration dinta Sai abunda ba"a rasa ba,basu Fito Cikin makarantar ba sai wajen Biyar da Rabi na yammah 5:30pm Inteesar ta gaji Tubus,Sai raki take yi ita kuma ba yunwa take ji ba Domin taci abinci Kawai tagaji ne so take taji tayi wanka ta kwanta ta Huta abunda ke karamata Tashin Hankali Irin jin datayi gobe ma Zata koma ta karisa ita kadai ba Daddy yaushe zata iya wannan Wahalar ita kadai .? Ta iske Jami"ar Ta bayero ba yadda Tayi Tsammani ba ashe babbar makaranta ce mai Cike da Dalibai kala kala kabilu Dabam Dabam. Suna tafe amota bayan sun Fito Daga Cikin makarantar,Umma da Daddy suna Hira da yaba tsarin Jami"ar Inteesar na Baya tana Jinsu duk ta gaji so kawai take Tayi wanka Taji ta kwanta ko ta samu ta Huta ganin suna ta Tafiya har yanzu ba su iso ba yasa Ta Dago Dara Daran Idanuwanta Wadanda suka Cika da gajiya tace"Daddy bamu kawo gidan Inna Aminan bane..? Tafada Cikin Sangarta da gajiya a Muryanta. Cikin Tsausayamata ya juya Ammh Hankalinsa na wajen Tuki yace"Mun kusa Intee..Sannu nasan kin gaji anya zaki iya wannan Wahalan karatun ko mu koma gida na nema miki nan KASU ne..,? Ya karishe Fada cike da Tsausayawa jin Abunda yace ne yasa Inteesar tayi saurin Wartsake gajiyarta Tana Fadin"A"a Daddy..Ka barni anan Nafi son Jami"ar Bayero fiye da kowacce Jami"a..Kuma Tunda na taso Daddy ban taba Fita wani garin nayi Rayuwa ba Shiyasa na zabi karatu a garin kano Saboda na kara sanin wasu abubuwan! Daddy ya jinjina kai alamun jin Dadi Umma Dake jinsu Ta Tabe baki Tana Fadin"Ashe dai Kina da Hankali..? Hararanta Daddy yayi kafin yace"Me kika Dauke mu..? Umma na Dariya tace"Sangartattu mana Miye ku in ba hakan ba..? Tafada Tana kallon Inteesar da Bakinta ya kusa Fadowa kasa Cikin Kunkuni tace"Daddy kaji umma ko..? Wai nice Sangartattaciya..? Daddy yace"Manta da ita..Eh kin ji ke Sangartattaciyace wani kikayi ma Sangartanki ba Daddy ki ba..?kyaleta sai tafi kowa kewarki ko bakomai Gidan zai mata Shuru inta koma baki..! Sanda ya Fadi haka Dukkansu sai sukaji wani iri Tabbas Bai yi Karya sai taji Dabam ita ta Haifi Intee Tasan ta da Kulafucin Gida ko Wani waje bata yarda Taje ta kwana Bata jin ta taba takama Gidajen Baffaninta,sai dai in sun Hadu gidan Daada a Dukku Shima Din bata yarda ta kwana Kafarta kafar Daddynta Shiyasa Umma tayi matukar mamaki da Intee ta Zabi kano,Sai dai kuma batayi mamaki ba ganin yadda Ta Dora ma kanta yin Jami"ar Bayeron Tun ba yanzu ba Tasan Shi kadai ne Dalilin da zai saka Inteesar Tayi nesa da gida. Ba wanda ya kara mgana sai Umma Dake nuna ma Daddy Hanyar gidan Yaya Amina Tunda sun Shigo gadan kaya. Sai gasu a kofar gidansu Sagir wanda ke Cikin Shagonsa da yaransa suna ta faman Dinkin yau Tun safe bai zauna ba ya Shiga makaranta bai Dade ba ya Fito Mama ta hanashi Sukunu da Murnam zuwan Inna Salaha da yarta Tun asuba tatashi ta gyara Dakinta da gidan Gabadaya tasa yaje kasuwa yayi mata Cefenan Abunda Zata Dafa musu Duk ta kasa Sukuni Shima Daya Dawo makarantar ne Mama ke shaida mai Inna Salaha ta kirata tace suna Cikin makaranta sai sun gama Zasu Biyo nan zasu kwana sai Gobe zasu Juya zuwa kaduna. Dinki gareshi kacha kacha Shiyasa abinci kadai yaci ya Dawo Shago ya Hau keke ya Fara Dinki Sallah kadai ke tadashi Tundazu Dayaji karan Mota sai ya kalli bakin Shagon nashi ammh Sai yaga basu bane,Duk da Kofar gidan ba kwalta bane,ammh akwai Kasa mai kyau wanda Yawan Zirga zirgan Motoci da mashina ya Shimfideta kamar an saka kwalta. Lokacin Dayaji Dirin Motarsu yana Dagowa da Inna Salaha ya Fara Cim karo wacce ke gaban Mota itama kamar an ce ta waiga sai ta ganshi Cikin Murna ta Fara Kiciniyar Bude Murfin Motan Tana Fadin"Mun iso..Gama Sagir din Yaya Aminan chan Cikin Shagonsa yana Dinki..! Tafada Lokaci Daya tana balle Murfin Mota ta Fito Shima Daddy Fitowar yayi yana kallon Sagir daya taso Daga kan keken ya Fito Daga Cikin Shagon Cikin Fara"a Daddy bai wani Sanshi ba,Sanin da yayi mai bai yi Girma ba Haka ba. Sagir karisowa yayi ya rankwafa yana gaida Umma ta amsa mai Tana Fadin"Sagir idon ka kenan..? Rabona da ganinka tun zuwan da kayi gaida Inno Muda ya Kawomim kai..! Kansa na kasa yana Sosa keya yace"Inna ai Karatu ne ke Hanani Zuwa ko"ina ..Ammh Insha Allahu da mun kamallah sai kun gaji da ganinmu..! Umma na Dariya tace"Hakane kuma..Ga Shago nata Habaka Allah yasa albarka..! Tafada tana kallon Shagon Tama kara ganin Cigaba Domin zuwanta na karshe bai kai haka Cika da kekuna da yara ba. Sagir Daddy ya juya yana gaisawar ya amsa mai Cikin Sakin Fuska yana Tambayansa karatu yace Alhamdulillah Afizge Sagir ke kallonsa Haka kurum yaga kamar Fuskarsa da yanayinsa yana mai kama da wani sai dai kuma ya rasa ta ina zai kama..? Yana wannan Tunanin Yaga Daddy ya Bude Kofar Baya yana Fadin"Inteen Daddy Fito mana..Ai mun so gidan Innam taki..! Yafada yana Bude mata kofar Motar,Sagir ya Dago Idanuwansa yana kallon wata kafa mai kyau da Tsari Cikin Cover na kamfanin Gucci ta Zurosu waje kafin ita kanta ta Bayyana Masha Allah ya Furta akasan Ransa ganinta kamar Inna Salaha sai dai ta Dauko Tsawon Babanta da yanayin karam Hancinsa sai dai Fatanta irin ta Inna Sahala ce mai Duhuwa. Sanye take da Doguwar rigar Abaya Kirar Armani ta amsheta Tayi mata kyau sosai sai gyalen Abayan Datayi Rolling dinsa Daga Tsakiya tudun gashinta Data Tamkesa da Band,Hannunta kuma karamar Jakarta ne da wayarta sai takardunta wanda Tayi Cike cike a makaranta.. Lumsasun idanuwanta ta Lumshe Tana Bin yanayin wajen da kallo Lokaci Daya tana Shan iskar wajen kafin ta wani Dakuna Fuska Tana Fadin"Allah Daddy am Tired..! Umma ta Harareta Tana Fadin"Kedai Raguwa ce..Baki ga yayanki bane ba gaisuwa..? Tafada Tana nuna mata Sagir Daya gama kare mata kallo yana ganin ikon Allah katuwar Budurwa Tana Shagwaba kamar yarinya..Tabdijam wannan ne zata Zauna agidansu?akwai aiki..! Kallo Daya tayi mai ta kauda kanta kafin ta Rausayar da kanta Tace"Umma kinsan fa in nagaji bana gane kowa..Ina yini..? Ta fada Tana wani Yamutsa Fuska Kamar ta wurgar da kayan Hannunta Amsa mata Sagir yayi yana Fadin"Barka da zuwa kano kanwata..! Jin abunda yace ne yasa ta Sakarmai Mirmishi har Fararan Hakoranta suka Bayyana tace"Thanks yaya sagir..! Yaji Dadin haka Umma ce ta katse su da Fadin"Alhaji Bude Booth Sagir samu yara su shiga da kaya Ciki inteesar mu karisa Ciki nasan Yaya ta gaji da jiranmu..! Daga haka ta wuce gaba Inteesar ta Daga kafarta Dakyar dataji sun mata Nauyi tsskani ga Allah ta gaji inda wani zai karban mata kayan hannunta Datafi kowa Murna. Sagir ne yafito yaran Shagonsa da Hannu suka Fito suna Shiga da kayan da Daddy ya Bude Shake da Booth din Motarsa akwatunan da Kayan abinci Cike aciki haka suka dinga kwasa suna Bin bayansu Umma zuwa Cikin Gidansu Sagir. Sagir kuwa da Daddy basu Shigo ba sai da aka gama Shiga da komai kana Sagir yamai Jagora zuwa Cikin gidan. Suka iske su Umma a Falon Mama dan madaidaici mai Dauke da Saitin kujeru Sabbi wadanda Sagir ya saka akayi mata,Har da Cafet din ga Tibinta da Reseventa,Sai karamin Center Table a tsakiyar falon da karamin Fridge dinta Daman Daki Ciki da Falo ne sai Tiolet aciki Ko"ina Tsab Mama bata da Kazanta ko kadan. Tana ta ina ta saka da su Umma Inteesar kuma na kan kujera mai Zaman Mutum Daya ta lafe Tunda ta samu ta Zube kayan Hannunta tasha Ruwa taji ta fara Dawowa daidai. Mama ce ta cika gaban Daddy da Lemuka da ruwa sai Kololin Abinci kansa na kasa suna gaisawa Tana Tambayan Bashir da matarsa da yaransa duk yace mata suna gaisheta ta gangaro Kan Lafiyar Daada yace mata alhamdulillah. Mama ta juya tana kallon Inteesar da idanuwanta ke Lumshe Tana Fadin"Yata..Barci kike ji ne..? Tashi kici abinci ko wanka zaki fara ne..?naga alamar duk kin gaji..! Umma na Dariya tace"Baki ga alama ba..Dayake kun iya Haihuwa Raguwa y'a ba..! Mama na Dariya tace"Eh munji bakomai..Tashi ki Farayin wanka kafin kici Abinci.Kai kuma Sagir Tafi da Alhaji Dakin ka sai yaci Abincin a natse..! Daddy yaji Dadin haka Duk da ba wani yunwa yake ji ba Ammh zai fi Sakewa achan Sagir yamai Jagora Zuwa Dakinsa Dake kallon na Mama Shima yana Shimfide da Cafet da katifa Daya yada akasa sai littafan karatunsa na makaranta Dana addini sai Akwatin kayansa da Hanger Dayake Sagale kayansa na sawa sai wasu Drowers Daya kan ijiye wasu kayan Daya Dinka in yagama wadanda ba"a amsa da Wuri ba Komawa yayi ya Daukomai Abincin Ruwan yana kara mamakin Girman Inteesar ya Dade bai ganta ba Tun tana karamarta Kamar tun wani Zuwa da Inna Salahar tayi da ita,Bata kara zuwa ba sai yau Dayake yanzu wannan zamanin ba damuwa akai yi da Zumunci yara ba In manya sukayi Shikenan,Kuma ita bata cika Bin Umma anguwa ba basa Shiri bata Daukan Sangartata Tafi Tafiya da Daddyta Shi Dayake Biye mata. Wankan ta Shiga Daman Shi take da So,Mama da kanta ta Juyo mata Ruwan Zafin Data saka afulas,ta kai mata Har Tiolet kuma ta kwashi wayarta da Jakarta da Takardunta ta kaimata Ciki kan gadonta Sabo 6by7 na karfe wanda Sagir din yayi mata tare da kujerun Dakin nata,Sai katifa Lamba goma Sha Biyar sabuwa Dake jingine gefe sai karamin wardrope dinta mai Kofa Biyu,sai Ledan daki Sabuwa malale ga kayan Inteesar nan jere agefen gadon da akwatuna da wasu ledoji kayan abincin kuma Suna Falon Mama,Tunda Umma tace nata ne Tana ta Godiya Kamar bakinta zai Cire Umma na Fadin bakomai. Bayan Shigar inteesar wanka ne Umma da Mama suka zama Bayan sun gaisa Mama tace"Ya wajen su Inno..? Dazu da safe Muda ya kirani munyi waya da Mallam Babba nace musu kina Tafe sukace ai jiya Inteesar din tazo tayi musu sallama..! Umma tace"Eh Taje..Tare naso muje ammh
Chapter 17 · 0% Book details