← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 181 OF 190

Sashe 181

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Tafiya ya Fito Daga Bankin kenan yaji Kiran Abba ya Dauka sukayi mgana Abba yana Fadamai Halin da ake Ciki yace Yanzu Baffa ya Kirashi shima Abujan zai tafi yanzu Abba yace yaje ya Dauko Inteesar gabadayansu Zasu Tafi da haka suka Rabu. Gida ya koma Inteesar na Kwance da Matashin Cikinta yace ta tashi ta sa Hijabi su tafi shi ya Zata gidan Abba zata zauna kafin su dawo jin Tafiyace ta Mike da Murna ta saka Hijabi suka Tafi koda sukaje sun iske har Ya yusuf shima dashi Za"a tafin bai je aiki ba Khalil ma yace dashi Za"aje Kowa yace sai yaje harda Munari Anty Safiya ce kadai aka bari agida Tana jego Saboda Yadda Labarin ya same su sun matukar Tsausayamata da Halin Datake ciki,ganin haka yasa Itama Inteesar tace sai taje itama Imran bai da yadda zai yi ya Hanata zuwa ammh bai so bayaso gudan Jininsa ya Wahala sosai ammh baida yarda zai yi. Ashe Labari Tuni ya Zaga Dangi suna Shirin Tafiya sai ga Wayar Sadam shima zai je basheer ya Kirasa ya Fadamasa yace ya Kira sa"id shima ya Tabbatarmai da yana Hanya Duk wanda yaji Halin da Sajida Take Ciki Sai ya Tsausayamata. Sadam suka Tsaya jira ba Dadewa sai gashi Shi kadai ne Aneesa na Gida da Yara Imran ya Kira Sagir yace ya Shirya su tafi Daman jiya su ukun suna Tare sun Hade shi da Khalil suna ta Caccakasan yayi musu banza. Imran a Motarsa ya Dauki Khalil da Sagir Ya Hada matan chan Motar Yusuf,Abba dagashi sai Direbansa hakama Ya Sadam suka Dauki Hanyar Abuja,suka bar Anty Safiya Dayake Tasleem na Tare da ita ga kuma Mama Achan kaduna ma Daddy Da Umma sai Ya Basheer Dake Tukasu suma din duka Hankalinsu ya tashi goggo Bintali da goggo Maimunatu suma sun ji labari Daddy ya Kirasu ya Fadamusu,Daada ce kadai basu Fadamawa ba Gudun Tashin Hankalinta,Dukkansu sun kamo Hanya basu zauna ba Domin Haka suna da kara iin wani abu ya Faru da nasu kwansu da kwakwartansu. Daddy su suka fara isa Abuja waya kadai yayi ma Baffa Kabiru ya basu kwatancen Inda suke,Daman yasan asibitin nan take sai gasu sun iso Lokacin an kai Sajida ma Daki na Musamman kebabbantacce. Koda suka iso an mata Alluran barci Ta samu barci ganinta Tana ta kuka da Sambatun Kiran sunan Imran Umma ta kara jin jikinta yayi Sanyi ganin yadda Mami Asma"u ta koma Kunya Ya hanata ta iya Daga ido ta kalli kowa Kukan ma ya Daina zuwar mata sai ajiyar zuciya kawai ta Jeme kamar ba ita ba Shi kanshi Daddy sai da ya Jinjina. Gudu sosai sukayi a Hanya kafin su iso,wajen azahar suma Direct asibitin suka iso,Mami Asma"u ta kasa Iya Hada ido da su Abba ballatana Imran Kusan Lokaci Daya suka iso da Inna Maimunatu da Mijinta ,Inna Bintalo ma ta iso Daddy da Abba Dan"uwansu suka Rumgume cikin Damuwa da ganin yadda shima Duk ya Jeme Saboda Damuwa su Sadam suka isa ga Khamis shima abun Tsausayi Umaima ta Rumgume Munari Tana ta kuka,ba Dadewa sai ga Sa"id ya iso Shi da Fareesatu da Hafsah da yara Inteesar dai na makale da Umma itama Duk jikinta yayi Sanyi,Khamis kuwa Sau Daya ya kalli Inteesar bai kara ba haka itama Imran na Tare da abokansa Sagir da Khalil,Sai dai Kuma karo na Farko da yaji Taausayin Mami ya Darsun mai ganinta a rakube Duk ta Fige ta Rame kamar ba ita ba Rayuwa kenan Dayake Justice da Hajiya Turai sun Koma Gida Dazu bada Dadewa ba Kamar Sajidan ta sani suna isowa ta Farka ta Fara Kiran sunan Imran,gabadayansu suka Nausa Cikin Dakin Baffa Kabiru ya bangaje Mami yana Hararanta wacce ta isa ga Sajidan Tana Riko hannunta Mami kanta na kasa ta kasa dagowa ma ta kalli kowa sai Hawaye dake bin Kumatunta Kowa adakin sai da ta bashi Tsausayi Umma ce ta Rikota zuwa gefenta ganin Tana neman Faduwa. Baffa Kabiru ya isa ga Sajida ya Riko Hannunta yana Fadin"Sajida ga Imran nan yana jinki..Gashi nan kin gansa..? Yafada yana Nuna mata Imran wanda Abba ya jawosa Gefen da Baffa Kabiru ke Zaune daga ido Tayi tana kallonsa Shima kallonta yake yi cikin Kallon Kuduran ubangiji ganin yadda Sajidan ta koma Lokaci Daya.. Idanuwanta na Zubar kwallah ta Kira Sunansa..!
Chapter 181 · 0% Book details