← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 190

Sashe 48

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wannan Tozarcin gaban wannan Mara Mutumcin yarinyar nan za"a Tasashi ana mai Fada Lalle me ya Zama Dole yaci Ubanta Ko Zata gane Shi din ba"asanta bane,Duk da Abba ya riga yagama Sakawa yarinyar ta kara Rainasa Yana mata Fada agabanta. Mikewa yayi a Fusace kamar wani Damisa Daidai Lokacin da Inteesar ta Fara Tafiya Zuwa Dakin Munari yace"Ke..! Cikin Kakkausan Muryansa Cikin Tsawa da Bacin Rai Cak ta Tsaya Lokaci Daya ta Juyo Tana Kallonsa ai Ransa bai kara baci ba sai Da yaga yadda Take kara Toshe Hancinta da Mayafinta Sai yaji kamar yayi Tsalle ya gansa a gabanta yana Kwallo Da ita Har sai ya Rakata Waje da Duka. Abba da Yusuf suka Saki baki suna Kallon Ikon Allah Safiya bata Wajen Tana Kitchen sai dai har chan Taji Tsawan Shiyasa ta Fito da Sauri. Cikim Takunsa na Takama da Sassarfa ya Fara Taku zuwa gabanta yana Fadin"Ni sa"an wasan ki ne..? Ni Tsaran wasan ki ne kina kallona kina Toshemin Hanci..? Ya Karishe Fada yana Nuna kansa Cikin Dakuna Fuska Inteesar kuma jada baya take yi acikin Ranta kuma Tana ayyana Lalle ne ma wannan Mutumin bai da Mutumci Dukanta Zai yi ko menene Nufinsa..!? Fadi take Munari batayi Sa"an Yaya bane..Mara Mutumci Tsageri Kuma Dan iska Saboda Tsabar Tacewa Shi a gaban Abba ma Shaye Shayensa yake Baya ko Shakkar Boye Mummunan Laifinsa kamar yadda Sauran masu aikata Laifi irin nashi suke yi. Yusuf ne ya Mike yana Fadin"Kai Imu Lafiyan ka kuwa..? Abba kuma yana Zaune ne kawai yana Kallon Ikon Allah. Inteesar Tana da Tsoro ammh kuma Bata bari a Takata ko Yayane Juya Manyan Idanuwanta tayi Lokaci Daya Tana Tura bakinta ta Cikin Mayafin Hannunta tace"To nifa bana son Warinta..Amai take sakani..! Tafada Lokaci Daya tana kallon karan Sigari da Har Lokacin Take Rike Tsakanin yatsunsa manya Guda Biyu na hannunsa Cikin kwarewa Inteesar tace acikin Ranta"Jar uba..Lalle wannan ya kware a Harkan ji wani Rike Sigari..! Bata gama Mganar Zucinta ba Taji yace"Ashe kuwa yau Zaki Aman kayan Hanjin ki..Maza ki Cire Abunda kika Sama Hancin ki..Zan gani yau ko Zaki mutu ne...! Yafada Lokaci Daya kawai Ransa na kara kuna ganin yadda yarinya kamar Wannan da bai Wuce ya saka Hannu ya Damketa ya Murjeta ba itace Zata Tsaya yana Fada Tana Fada..? Kai bata isa ba Dole ya koyamata Hankali ayadda yake ji kamar yayi ta Dukanta Har ta suma Ta Daina Numfashi. Kallon Anya kana da Hankali Inteesar Tayi mai kafin ta Nuna kanta Tana Fadin"Wai ni...!!? Kai Imran yaji kamar Wuta ne acikim Zuciyarsa Saboda yadda ta Fara Tafasa Tuni Jiyoyinsa sun Tashi na Saman kansa Radau Tuni ya Fara Fitar da wani Huci Kirjinsa na Sama yana kasa. Kamar kiftawar Wani abu sai gashi a gabanta so yayi ya saka kafa ya Tadiyeta ta Fadi sai ya fasa ya Daga Hannu zai kai mata wani Dukan da Kila sai tayi Sati acikin Coma bata Farfado ba,Inteesar Da Tsoro ya kamata ganin yanayinsa ta Falfala da Gudu Zuwa Bayan Safiya Cikin Alamun kukan Shagwabanta Tace"Wayyo Allah na..Abba ka gansa ko..? Tafada Tana kara Boyewa Bayan Safiya Jikinta na Rawa ganin yadda ya Rikide ya Sauya Lokaci Daya Ganin haka yasa Abba yace"Yusufa Rikomin shi kada ya Illata yar Mutane..! Da Sauri Yusuf ya Mike ya Rikosa sai ya Fizge,Kallon Inteesar kawai yake da Rinannun Idanuwansa yana Tunanin Ko Kasheta ma zai yi ya Huta da Yadda yaji Zuciyarsa na Fitar da Wani Zafi. Abba ne ganin haka ya Mike da kansa ya isa ga Imran ya Rikosa Da yaso ya Bangaje Yusuf din sai ga Abba sai ya Dakata yana Sakin Huci. Sigarin Hannunsa Abba ya amsa ya Mikama Yusuf yana Fadin"Fita da ita..! Amsa yayi ya Nufi Hanyar Fita da ita Shi kuma Abba ya Riko Hannunsa ya Zaunar dashi kan kujera yana Fadin"Imran wannan bakar Zuciyar taka ina Rokom maka Allah ya Rabaka da ita..Tun Zuwaira nada rai Tasha maka kukan wannan bakar Zuciyar taka..Tasha Fadamim Tayaya kana irin wannan abubuwan Za'a Dauki mace abaka..? Wanda bai iya Kula da Rayuwarasa bane zai kula da na wata..? Ko Dago kansa bai yi ba kansa na kasa Shi Abba wai baisan kara ma wutar Abun yake ba yana Mai fada gaban wannan Mara mutumcin yarinyar bane,Shiyasa kawai ya Mike saboda in yacigaba da Zama komai zai iya Faruwa ba Cikin Sassarfarsa ya Wuce Dakinsa ya Shige Lokaci Daya yana Bango kofa Bumm! Abba ya Bisa da kallo Kafin ya Kada kai yana Fadin Allah ya Shirya. Inteesar ya kallata Da Tayi Tsuru Tsuru Yace"Inteesar kiyi Hakuri kin ji ko..? Yi tafiyarki Wajen Munari haka yayan naku yake sai Hakuri..! Kamta ta Sadda kafin tace"Bakomai Abba.." Ta juya zuwa Dakin Munari sai ma ta ganta akofar Dakinta Ashe Tun Tsawan Farko ta Fito ganin Abunda ke Faruwa ya bata Tsoro yasa ko Fitowa ta kasayi kada ganin Wajenta tazo itama ahada da ita. Hararanta Inteesar taja Tana Fadim"Ashe kina Tsaye kina ganin wannan Mahaukacin yayan naki Zai Dake ni..? Munari batayi mata mgana ba Tayi Saurin jan Hannunta suka fada Dakinta ta maida Kofa ta Rufe Tana Waigre Waige,sai abun ya bama Inteesar Dariya ta Zauna Bakin gado Tana Fadin"Dillah bsshi fa anan Dakin..Naga kina ta Waige Waige ne..! Munari ta Zauna kusa da ita Tana Sauke Numfashi tace"Baki san wanene ya Imu ba..Da baki Fara yana mgana kina maidamai ba Besty..! Inteesar ta Saki karamin Tsaki Tana Fadin"Munari Daman wannan Dan iskan ne yayan ki..? Tabdijam gaskiya baida Mutumci Wlh...! Kallon da Munari tayi mata ne yasa ta Fahimci barnan Datayi da Sauri ta Wayance Tana Fadin"Yi hakuri ba Haka nake nufi ba..Ammh kawai sai ya Dakeni..? Kuma fa Shaye Shaye yake har acikin gida agaban Abba..? Ranar da na Fara ganinshi Tare da Sagir yana Shan Taba sai da nayi amai yanzu ma haka Zuciyata tashi Take yi Wlh..! Ta karishe Fada tana wani Dakuna Fuska. Munari ta karkace kai gefe tace"Ya Imu baya Shaye Shaye Besty..! Inteesar ta Kalleta tace"Ita Sigarin kin Cireta a Ciki ne..!? Munari Tace"Kefa wani Lokacin kina jin kanki kamar Wata bagwariya..Sigari ai ba Bugarwa kuma Bata saka maye bata Cikin kayan Shaye Shaye..! Inteesar ta Bugamata Harara Tana Fadin"Kare mai Tunda Yayanki Ne besty..Ammh ni kam kiyi hakuri bazan fasa Fadin gaskiya ba Itama Sigarin ai Duk Mayen ne miye maraban Dambe da Fada..? Nifa Tun ina karamata Na daukan mai Shan Sigari nake Dan iska..! Munari Tayi Mirmishi Tana Fadin"Ko Daya..Ba ina karema Ya imu bane sai Don yana Dan"uwana ba A"a Sai dan Gaskiya nake Fadamiki baya Shan kowani kayan maye banda Sigari..Ita kam Ta Zama addict atare tsshi Dashi..Zai iya Shanta Daga Safe Har Dare bai Nemi wani abinci ba ko Ruwa ba..! Inteesar ta Zaro ido Tana Fadin"Kuma Lafiyarsa Kalau..? Munari tace"Ba gashi kingani ba..Ai da kim Tsaya daya Nuna miki Lafiyarsa kalau..! Inteesar tace"Tabdijam wa ni..? Na Tsaya ya Karyani..? Naga yadda yake Huci kamar Zakin Daya Kwana Biyu bai Samu Nama ba..tsoro ya kamani badomin su Abba ba yau da na gama Yawo wannan Mara mutumcin yayan naki! Kallon ta kawai munari tayi batayi mgana da Sauri tace"au na manta Sorry..! Munari ta kada kai kafin Tace"ke mai Sa'a ce Besty..! Inteesar ta Kalleta Tana Fadin"Sa"ar me..? Munari tace"Banta ba ganin ya Imu ya Tsaya yana mgana da mace Haka kamar yadda kukayi ba..ko mu da muke kanmensa baya mgana Damu Mu maida masa martani Daga kusa kusa..Baya som ka Rainashi ko alama Yana Daga Cikin Abunda ya Tsana Kazo wucewa ko kazo gabansa yana Shan Sigari ka Toshe Hanci..! Wlh ni nan ya Taba kamani na Toshe Hancina Domin Nima bana son Warinta Wlh Tallahi Daya Kama Bakina ya Damke Ya Rika Fesamin Hayakin Sigarin acikim Hancina sai da kara Daya ta kare Hayaki na Shiga Cikina da ace ina da Asthma na Tabbata da sai na Mutu Har Lahira aranar..! Inteesar ta Kwalalo ido Cikin mamaki da Tsorata tace"Kai Besty..Kuma kika Tsaya..? Meyasa baki gudu ba..! Munari ta saka Dariya Tana Fadin"Dana Gudu da kila Har da Duka Zai Hadamin..Ai shi bakayi mai Laifi Ya Kiraka ka Gudu..Zai ga ka Rainashi Saboda Zuciyarsa In ya kama Dukan Mutum sai ya Sumar dashi..! Zuwa Lokacin Inteesar ta gama Tsorata Cikin Kwalkwal da ido Tace"Na Shiga uku Besty..Ya Zanyi na koma Gidan Mama yau..!Me munari Zatayi in ba Dariya ba Harda Dukawa Inteesar ta Daka mata Duka abaya Tana Fadin"Shegiya Daman Ciwon karya kike yi ko..?Domin ni ban ga alamun patient anan ba..! Munari ta Dago Tana Lamgwabe Wuya Tana Fadin"Wlh bani Lahiya Zazzabi yau na Tashi Dashi..Taba Jkina ma kiji..!ta fada Tana Daukan Hannun Inteesar ta Dora Saman Wuyanta. Inteesar taji da Dumi tace"Eh gaskiya kina Fever to kin sha mgani..? Kai ta gyada mata Tana Fadim"Tashin na kenan tunda nssha Mgani..Sai naga Kiranki a waya ina Shirin kiran ki naji Tsawan ya Imu Shine na Leka sai na ganki Kina ta Zare ido nace yau Besty ta Fada inda bai Dace ba..! Inteesar tace"Umh bari kawai..Ai Insha Allahu bazamu kara Haduwa ba.Na tsorata da Labarin da kikabani im na Auna yadda naga Lokaci Daya ya koma..Ammh dai ke bai taba Dukkan ki ba ko..? Munari tace"ya taba Kamar sau Biyu ko...Inaganin. shima mari ne da Tokari.Ni ai ina Kiyayemai Anty Asma"u ce Tasha Wahalan sa sosai Har Sumar da ita ya taba yi Dayake ita ke Binsa..! Inteesar taji Gabanta ya Fadi ta Dafe Kirji tace"Innalillahi Anya bai da Aljanu..! Munari tace"ke Lafiyansa kalau fa..! Ta karishe Fada Tana Dariya Inteesar Tace"Ai naji abun nasa ne bana Hankali bane..Allah Sarki Yanzu ina ina Anty Asma"u? Hala tayi aure ne..naji baki taba bani Labarinta ba..! Munari Tayi Shuru batace komai ba Inteesar ta Kalleta kafin Tace"Ko Ta Rasu ne..? Munari ta Kalleta da Sauri tace"Ya akayi kika sani..?Inteesar Cikin jimami Tace"Yadda naga kin yi ne Besty..Am sorry bansani bane da Ban Tambaya ba Allah ya jikansu da Rahma Kice Bayan Rashin Anni Harda ta Asma"u ma kunyi..So Sad..! Dayake inteesar din ta Taba Tambayanta Ina Mahaifiyarsu tace mata ta Rasu. Cikin Wani yanayi Munari ta amsa da Ameen. Daganan suka bar mganar suka Shiga Wata,Suna ta Hira makaranta suna Dariya,Sai ga Anty Safiya ta Shigo Itama ta Shige Cikinsu suna ta Hira,Sai
Chapter 48 · 0% Book details