Sashe 90
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mara kunya..! Imran ya Dakuna Fuska yana kallonta ido cikin ido Tabarsa ya zuka Hayakim ya sakesa ta Hancinsa harta Kunni cikin kallon sama da kasa yace"Ni kin ji sanda nace Daada tazo nan..? Ai ni ina girmama Daada..Ko bakomai Daada ta nuna Rauninta kan abunda ya same mu,nifa da ku nake bada Daada ba, kada kuma ki kara Kirana Mara kunya bake kika Haifeni ba mganar kwaya kuma in ma na sha ai ba da kudin Lauyoyi na siya ba ko..? Kowa ido ya zaro da jin kalamansa Yusuf ya Dafe kansa cikin Takaichi Mami Asma"u taji ta Muzanta ta kalli Baffa Kabiru wanda yake bin Imran da kallo yana Tunanin Tsegerancin yaron zai saka ma ya iya Zaginsu kila ma Har malamin ya gagaresa Tunda gashi ya kasa mgana. Yana neman hanata mgana ta Kwace hannunta ta fara taku zuwan gaban Imran tana nuna kanta Lokaci Daya Tana Fadin"Ni kake fadama wannan mganar..? Kasan wacece ni..? Irin kallon sama da kasa na Rainin nan yayi mata Irin to ke din wacece cikin Gadaransa yace"To ke din Wacece..? Ai b..! Bai karisa ba ya yaji tsawar Abba ta karade Falon cikin bacin rai yace "Kai IMRAN...! yafada yana Huci Huci mai zafi Tun dazu ya kasa cewa komai saboda Yasan tankwasa Imran ba abu bane mai Sauki Daman yasan tabbas sai haka ta Faru,sai dai an kawo gabar da Dole yayi mgana yana da Tabbacin da bai Tare Imran ba cemata zai yi kedin ai ba uwata bace..Zai iya Zaginta Duk mganarta yana da amsarta shi ya Haifi Imran yafi kowa sanin baya da Shayi ko Tsoro ba Asma"u ba ko Baffa Kabiru zai iya kallah yace mai ai ba Ubansa bane shi ballatana ita. Imran ya wani kalli Abba a karkace kafin yace"Abba daka koma ka Zauna..Na dade ina sauraran mganarka ammh yau kam bazan saurareka ba..! Yana Fadar haka ya juya wajen Mami Asma"u Lokaci daya ya saka Hannunsa ya Murje Sauran Taban Hannunsa Data rage da Wutar da komai ya saki Sauranta a kasa Hannunsa duka Biyu ya maida cikin Aljuhun wandonsa yana Fadin"Arm kika ce ma me..? Yauwa na tuna bansan ko wacece ke ba ko..? To ni ina ruwana da saninki Tunda ke ba Uw....! Abba ya kara Dakamai Tsawa yana Fadin"Wlh in ka kara cewa Tak anan Wajen sai naci Mutumcinka imran kaji ma na Fadamaka..! Yafada cikin kakkausan Murya yana nuna shi da yatsa. Imran ya dago yana kallon Abba Lokaci Daya yana wani Dakuna Fuska. Mami Asma"u tayi wiki wiki kamar mara Gaskiya Dariya kowa ke kunshewa aciki ganin yadda tayi,Basheer da Sadam suka kalli juna suna Mirmishi Inteesar kuwa sai da ta Dara Tana Rufe bakinta aranta tana godema Ya Imu yau taga mai mganin iskancin Mami Asma"u saura Diyarta Tsagera mara kunya,Hatta Umma abun yayi mata dadi kanta na kasa tana Dariya kasa kasa wato mganin Mami Asma"u sai tsageru irin su Imran Daddy na gefe bai ce tak aransa yana fadin in bata kama girmanta ba ai yaron zamani zai tayata kamawa. Abba ya karisa wajen su Baffa Kabiru yana Fadin"Ya kabiru don Allah kuyi hakuri ku dawo..Bai kamata ka Dauki wannan abun da zafi ba..wajena kuka zo ba Wajen Imran ba kuma Imran bai isa ya hanani Abunda nayi Niyya ba..Kuma bai isa ya Raba jinin dake Tsakaninmu ba Ya kabiru..! Baffa Kabiru ya kada kai yana Fadin"Ammh kana ji yana neman Zaginmu ni da iyalina..! Baka iya dakatar dashi ba..? Abba yace"Ai na Dakatar dashi Baban Sajida..kuyi hakuri..! Kafin ma Baffa ya samu bakin mgana ta tareshi da cewa"Ka tareshi lokacin Daya gama Tozarta mu ba? Wannan gabar Daddy ne yayi magana yana fadin"Yaya ya kamata ka Dakatar da Asma"u kan saka baki cikin mganar nan ba Huruminta bane..nan wajen fa akwai mutane kuma bataji kowa ya tanka ba..Mganace Tsakanimu iya mu nan manya bai kamata matarka tana Sako baki ba..! Su Sa"id dake gefe suka kada kai alamun gaskiya ne. Mami Asma"u tabi Daddy da Harara Tana Fadin"Sai nayi shuru ana cin Zarafin Mijina ko..? Ni Asma"u nasan Ciwon kaina kan Mijina da ya"yana zan iya yin komai domin sune iyalaina anan duniya..! Daddy yace"Musan wannan kowa anan ai Ya"yan nasa da matarsa sune iyalansa kuma don su ma muke fita nema ammh bai kamata kina Tsallake in da ba Huruminki ba..! Ta bude baki zatayi mgana Baffa ya Rike mata Hannu ammh duk da haka sai da ta Furta cikin bacin rai tace"Ammh shi Tsagerun yaron naku daya Tsoma baki sako cikin mganar kukayi..? Daddy zai yi mgama Abba ya Hanashi ta Hanyar tareshi yana Fadin"Mustapha ba girman kabane..Kyaleta don Allah Yaya kabiru Asma"u don Allah kuyi hakuri ku dawo ku zauna ba domin kowa ba saboda girman Allah da kuma Girman zumunci..! Yafada yana Hada Hannayensa alaman Roko Imran Dake Tsaye yaji Haushi ya kamashi Karamin tsaki yaja kawai bai ce komai ba. Jin haka yasa Baffa Kabiru ya kalli Mami Asma"u yana Fadin"Muje mu zauna..! Zatayi mgana ya hanata bayan ya Girgizamata kai dole ta Bishi ya koma in da ya tashi ya zauna itama Haka sai Harare harere take yi tana waige waige,kowa yayi kamar bai ganta ba. Suna Zama Abba ya koma ya Zauna Kafin yayi mgana Baffa Kabiru ya Rigasa da cewa"Malami Imran Shaye Shaye yake yi..? Yafada yana kallon Abban Imran Dake gefe kamar yace"Eh ko zaka iya Daukan mataki ne..? Sai dai ba Halin mgana saboda Abba ya hanasa ammh Kallon kafa fara cikani yake ma Baffa kasa kasa Yusuf na gefensa bayaso ya bar Wajen domin Imran bazai damu da ya Zubar da Halin nashi ba. Abba ya dan Murmusa Kafin yace"Imran baya Shaye Shaye Yaya..Taba kadai nasan yana sha..! Baffa Kabiru yace"Taba..? Kaidai ita kagani ammh daga ganin yanayinsa bazai rasa shan kayan maye ba Allah ma ya kyauta bayashan giya..! Yafada yana kallon Imran din daya ji kamar ya Durama Baffan Ashariya. Abba yace"Eh bazan yi shaidansa ba..Sai dai nafi kowa sanin Imran duk cikin Ya"yana shi kadai ne bayamin karya..Yana fadin gaskiya komai Dacinta Inda yana shan wani kayan Maye bilahil azim kaji Rantsuwan musulaimai sai na fara sani..! Baffa Kabiru ya jinjina kai bai kara mgana ba Abba ya gyara zama yana Fadin"Yanzu dai ya mganar zuwan mu Dukku gobe..Ina so naje naga Daada na roketa gafara..! Yafada cikin wani yanayi Baffa Kabiru ya dan zakuda kafada kafin yace"Aini na gama mganata..Gobe nace daga nan mu isa Dukku bana so kowa ya Fadama Daada sai dai ta ganka kawai ammh naji Yaron ka yace bazaka je ba kila ita Daadan kake so tazo ta sameka..! Abba ya girgiza kai yana fadin"Ban isa nace haka ba Yaya..! Baffa Kabiru yace"D"an ka ya yanke maka Hukunci kuma baka iya cewa komai ba..! Imran da ransa ya gama baci ya Budi baki yace"Ba Hukunci bame haka ce zata Faru ba inda zamu je..! Abba ya Mike ransa yana Fadin"Imran..Imran me na gayamaka..? Cikin Dakuna fuska yayi yana Fadin"Kace kada na sake mgana..! Abba yace"Shine kuma saboda ka Rainani ka sake yin din ko..? Imran yace"Ammh Abb..! Rufemin baki kafin Raina ya baci na tsinke ka da mari..! Abba ya katseshi cikin Fusata kafin ya Cigaba da fadin"Ina Ruwanka da mganarmu.?kana sako baki cikin mganar manya yaya fa Yayana ne Uba yake gareka ya isa dani Ubanka bama kai ba..! Imran ma kunkuni acikin ransa yana fadin Tab ni dai ba Ubana bane wlh. Kowa yaga Motsin bakinsa Hatta Abba sai dai bai bi takai kada ya Matsa ya fada da karfi kowa yaji ya kuma san ba abu bane mai kyau ya fada ba. Cikin Kaushin Murya Abba ya Nunashi da yatsa yana Fadin"To kul na sake jin kayi mgana anan wajen..Mganar Tafiya Dukku kuma da yardan Allah Gobe zamu tafi dukkanmu dani da kai da Yusuf da Munari da Matarsa In kaga dama kabiyomu in kaga dama kada kaje..! Yafada cikin Fushi Imran yabudi baki yace"Fine..ni tunda bakace Dole naje ba Allah ya kiyaye hanya..! Yana fadar haka ya juya zai koma Dakinsa Abba ya rike baki cikin mamaki kafin yace"To na fasa..Wlh sai kaje! Imran ya Juyo cikin mamaki yana fadin"Abba..! Yace"Eh sai ka je Umarni ne Daga ni Mahaifinka in kuma ka Sauya wani Uban ne zan gani..! Yana gama Fadar haka ya koma Wajen Zamansa Ransa na baci. Imran kamar zai yi mgana Ya dago ido keman suka Hada Ido Hudu da Inteesar kai ta girgizamai tana Lamgwabe kai alamun kada yace komai batajin dadin Fadan da Abba kemai yana sata jin wani iri. Shi kuma Saboda ita bazai iya cewa komai ba Idanuwanta suna da kaifi a gareshi yasa ya juya kawai ya Shige Dakinsa ya bango kofa. Abba ya jinjina kai kawai bai ce komai ba ya juya yana kallon Baffa Kabiru da Daddy yana Fadin"Kuyi hakuri dashi..Haka yake sai fatan Allah ya shirya..! Ameen kawai sukce ba wanda ya kara mgana Abba ne ya mike yace su Daddy su tashi su shiga Dakinsa sa tattauna achan sauran matan kuma Safiya ta kwashi gayya zuwa Shashenta Inteesar da Munari da Hafsah suka tafi Dakinta Yusuf kuma yayi ma su Basheer jagora zuwa Dakinsa na baya. Shi kuma sai ya yanke Shawaran kwana Dakin Imran tunda yana da Tabbacin ko giyan wake yasha bazai Tura wani Dakin Imran ba. Shashensa ya koma ya iske Safiya ta bama Kowa wajen kwanciya Bedroom dinta ta sauke su Aneesa. Dayan kuma ta Sauke Umma da Mami Asma"u wacce ke ta wani shan kamshi Umma dai sai dariya acikin ranta to shan kamshi me ke da yaro ya gama Tsage miki gaskiyarsa. Imran na Kwance yana fama da Nauyin Umranin Abba bashi kuma da yarda zai yi ya Tsalleke mganar sai Mami Asma"u dayake Tunanin sai yayi mata kyakyawan zuwan da zata gane Waye shi zata kiyayesa dauka take ita wata ce..? Shi ko Baffan mijin nata ba ganinsa yake da wata kima ba ballatana ita karan kada Miya. Yaja tsaki yafi sau ba adadi shi kadai kafin yaji Shigowar,Yusuf dago kai yaga waye zai shogomai daki sai yaga Yusuf da kayan barcinsa da Blanket da Safiya ta kawomai