← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 190

Sashe 126

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Daga Yusuf har Abba basu matsa da sai sun ji Ina zai je ba Tunda suka ga bai Fada musu ba bayanzu yake son su sani ba Har ya fice suna binsa da Allah ya kiyaye da Fatan Nasara da Sa"a,yana Fita Daga Haraban gidan Wayar Khalil ta shigomai Dakatawa yayi Daga Hawa mashin din nasa ya amsa kiran mgana dai sukayi kan aikinsu Inda Imran din ya Fadamai yanzu ya fito zai isa Bankin sun Rabu kan Duk abunda ke nan Imran din zai Kirasa ya Fadamai haka ya Hau mashin dinsa ya fice Daga Haraban Gida acikin Ransa yana jin ya Zama Dole ya sauya ko saboda Mutanen da suka Damu da ganin Cigabarsa irin su Khalil da Sagir.
Karfe 8:00am tayi ma Imran a office din Manager Turanci ne kadai ke tashi acikin wajen su biyu ne kadai Sai karan iskan AC,Manager din Bahaushe ne Sulaiman Ishaq Dawanau,Sai Imran Dake zaune kan wata Kujera Dake kallonsa gabansu wani katon Tebur ne baki mai Sheke sai ruwa da lemo,Dake gaban Kowanensu.
Tattauna sukayi sosai Duk ba Interview bane sai dai Sulaiman Ishaq ya Karu da abubuwa sosai da D'an karamin Tattaunar da sukayi da Imran ta Tsawon awa Daya,ya Fahimci Abubuwa Dadama,ciki harda Sanin Tarin Ilimin Imran da baiwarsa da Sanin Abunda ya karanta din ba Shakka Lokacin da yayi aiki an samu Zakaran ma"aikaci ya Duba Duka bayanansa da Mr Tunde ya Turo musu ta Email dinsu mganace Daga Sama ba wani bata Lokaci Bayan sun gama Tattaunawa Sulaiman ya Mike yana bama Imran hamnu sukayi musabaha bayan ya Zana sunansa a Mtsayin assistan Manager na Branch din Gt bank din Dayake ciki Suna maraba dashi da ko a gobe ne zai iya Fara aiki Office dinsa yana Ready.
Imran Dayaji haka cikin karfin gwiwa ya basa Hannu suka jinjina bakinsa nata Fadin"Thank u sir..Thank Very Much..!
Sulaiman na Mirmishi yace"U are Most Wlcm Mr Imran..!
Imran bai Tsaya bata ma kansa Lokaci ba yace ko yau zai iya Fara aikinsa Sulaiman Ishaq yaji Dadin haka yayi mai Jagora zuwa Cikin bankin yana nunamai ko"ina bayan ya sanar da Taron meeting lokacin da aka tashi break na Lunsh da masu yin Sallah yana so ya gabatar da Imran a Mtsayin mataimakinsa a wannan wajen mai kula da duka Shashen Dake Cikin Bankin.
Kayattacen Office din Imran na Hawa na Uku ne Tunda Buliding din bankin Babba ne sosai,Office ne babba mai Dauke da glass Daya Zagaye wajen,ana ganin na ciki na ciki ma yana ganin na Waje sai Tebur baki daya kusa Cika Office din,sai kujerarsa Baka mai mukami sai wasu Dake Fuskarta guda biyu wannan na karban baki ne akwai Laptop na aiki Sabuwa awajen komai ma sabo ne Tunda assitan din Dake Wajen karin girma ya samu zuwa Manager na Brarch din su Dake Abuja Shiyasa aka Daukesa adaidai Lokacin kuma sai ga Imran shiyasa Faduwa taxo Daidai da Zama,harda karamin Frige akwai da kuma Tibin bango karami sai AC masu sanyaya Waje guda uku Daga gaban Teburin an Dora wani karamin Katako mai kyalli Wato IMRAN ABUBAKAR MALAMI(assitance Manager) da sunansa makale ajiki kamar yadda suka sanya komai an Riga an Tsara kuma an gamashi.
Nan Sulaiman ya barsa bayan sun kara shan Hannu da juna Cike da Farimcikin da Imran ya Dade bai jisa a Ciki ba ya tsinci kansa Lokacin Daya ambaci sunan Allah ya Zauna saman kujerarsa Idanuwansa suka cika da kwallah aikin Banki Burinsa ne kuma Muradinsa Shiyasa wani Rauni ya bayyanamai da kewa mai Tsananin Dayaji kamar ya Fitar da kwallah.
Bai Fara komai ba sai da ya Fito da Wayarsa Abba ya fara Turama Sako..

*Alhamdullillah Imran is back..Am now a Assitance Manager GTB branch Kano..*

Bayan Abba haka yayi Copying ya Turama Sagir da khalil sune ma Masoyansa ne kafin ya kashe Wayar gabadaya yasan zasu kirasa shi kuma ayau Dayake jin kansa wani iri so yake yayi aikin Daya Dade yana kewa ko Hakan zai Ragemai jin Dadin Dayake Ciki,Har ya kashe wayar sai ya Tuna da Mr Tunde da Sauri ya kunna kamar yana Jira sai ga Kiransa yana Dagaawa ya faramai Congratulation,
Yana Tayashi Murna ya amsa mai Cikin Sakin Fuska lokaci Daya yana mai Godiya,basu wani jima suna mgana ba suka yanke kiran suna gama Wayar ya kara kashe wayar ya maida ita aljihu yajawo Computer gabansa ya kunnata komai da komai da Duk wasu bayanai da zai Bukata yana Ciki Tuni ya fara aiki ba kama Hannun yaro yanayi wani Annuri yana Fita daga Cikin Ransa Har zuwa Saman kyakyawan Fuskarsa.
Abba ne ya fara ganin Sakon na Imran Lokacin yana Falo Inteesar da Munari sun fito suna shirin Tafiya makaranta yau bada Safe suke da Lectures ba.
Abba daya ga sakon Sai da ya Daidai Gabansa ya Duka yayi Sujjada ya yi ma Allah godiya da Kirari sai da ya Dago Farinciki yasa sai da yayi kwalla nan yake Fadama su Inteesar abunda ya Faru Munari ta Daka Tsalle da Ihu Lokaci Daya ta Rumgume Abba ihun ne ya Fito da Anty Safiya Inteesar baki har kunne,zuciyarta Dake Cikin Damuwa tayi Fal da Farincikin jin Imran dinta ya Zama kamar yadda Kowa ke Bukata Allah Sarki
Munari ta Rumgume Inteesar da Anty Safiya Tana Murna ita kanta Safiyar tayi murna kwarai Tana ta saka albarka Lalle Imran wato shi dai na Dabam ne Komai sai dai aji kawai,Yusuf ne ya kira Abba ya Dauka yana Murnan gayamai Sakon da Imran ya Turomai Abba yace mai shima ya Turomai Farincikin su yaki Boyuwa Abba nata Fadin Allah nagode maka Allah ka kara Shiryamin wannan yaron ka kara Mishi Natsuwa Allah ka yayemai wannan Zuciyar dayake Fama da ita.
Haka chan ma Khalil da Sagir suke Cikin wannan Farincikin sannan dukkansu sun kirashi wayarsa tana Kashe aiki gamai kareka kenan
Sagir haka ya kira Mama yana Fadamata itama tana ta saka albarka Inteesar suna Hanyar zuwa makaranta ta Kira Daddy ta Fadamai yace yanzu suka gama waya da Abba ya Fadamai sun dan jima suna mgana inda yake Fadamata shima Abba Saura Kadan a kirashi Domin Manya Daga sama a gwannati suna Duba lamarin.
Bayan nan ta Kira wayar Imran a kashe sai ta Turamai Sako.

*You had the passion, and you had an ambition. You truly deserved every bit of the success you have achieved. Congratulations Ya Imu..*

Ta turamai Tana Mirmishi ita kadai Munari na Lura da ita sai Mirmishi take yi bata dai ce mata komai ba Tana jiran Wata rana ranar da mganar Zata shigo ko kuma ita Inteesar din ta tareta da mganar Zata Fito ta gayamata cewa Son ya imu take yi bata sani ba.
Chapter 126 · 0% Book details