Sashe 86
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
yace"A"a Maimunatu kada ma ki fara Dare yayi..Ki bari insha Allahu gobe bazan kara kwana agarin nan ba sai a dukku gaban Daadarmu sai mu hadu achan.! Inna Maimunatu na sharan kwallah Tace"Shikenan Ya malami daman Sa"id yace min ya kira Kawunshi kabiru na Abuja yafadamai shima yace zai kamo Hanya in ya Samu jirgi shikenan in kuma bai samu ba zai yi Tafiyar Mota..! Abba na Dauke Hawayensa bai so su kara zuba yace"Barrister..Yaya kabiru ashe baya Fushi dani..! Da Abba ya Fadi haka kamar Imran ya Mutu haka yake ji,baima san sadda Abba ya gama Wayar ba sai da ya tsinci Muryan Inteesar tana mgana da Daddynta. Alhaji Mustpha shigowarsa Gida kenan Shida Basheer Inteesar ta Kirashi Kokari ma yake ya shiga gida yayi alwala ya samu Sallar mangariba Domin yaji ana ta Kira Basheer kuma ya Biyosa gida ne saboda akwai Lissafin da zasu yi yaji kiran Inteesar. Suma shiga Falon ya Daga Kiran irin yadda yaji yanayinta cikin Murna yasa yace"Inteen Daddynta me ya Faru ne najiki cikin Annshuwa..? Inteesar na kallon Abba tace"Daddy Albishirinka..! Yana zama kan Daya daga cikin kujerun falon yana Fadin"komai Intee na take so shine goron albishir dinta..! Yafada Daidai Lokacin da Umma ta iso Falon dauke da Ruwa da Kofuna Basheer na gefe zaune yana Latsa waya a Hannunsa.. Inteesar tace"Daddy gani ga..Baffa Malami gani kusa dashi..! Daddy yaji mganar asama adaidai Lokacin kuma Ana ta Kiransa a waya Call Waiting,. Cikin Dan daburcewa yace"Wane kikace Intee Daddy..!? Da sauri ta kara Fadin"Baffa malami Daddy gashi ma kuyi mgana..! Tafada tana mikama Abba wanda ya karbi Wayar yasa a kunni lokaci Daya yana Fadin"Mustapha Baban Basheer Mijin Salaha..! Kamar a mafarki haka yaji muryansa da Sauri ya mike jikinsa ba inda baya rawa,har yana Ture Umma Dake duke gabansa Tana Tsiyayamai ruwa. Suka Mike atare suna binsa da kallon mamaki. Cikin In ina yace"Yaya Abbakar..? Kai ne da gaske..! Abba na Mirmishin jin dadi yace"Nine Mustapha..Abun kunya Inteesar na tare damu na tsawon Lokaci ban gane yata bace..! ? Yafada abun na karamai ciwo Daddy daya yi mutuwar Tsaye yace cikin son Tabbatarwa "kai..kai ne Baban Munari kawarta..!? Abba yace"Ni baban Mai sunan Daada ne..sai dai in kaine Baban Mai sunan Autan Daada..! Sai ga Daddy na Hawayen Farinciki cikin murna yake kallonsu Umma yana Fadin"Wlh shine Salaha Basheer..Babanka ne ya Malami ne fa muke mgana dashi..Ya malami fa Alhamdulillah Alhamdullilah..! Su Abba suna ji daga alamu ma ya manta yana waya ne ya Gama Rudewa Inteesar ta karbi wayarta ta kashe nan take ta Kira Mama tace ita da Sagir suzo gidansu Munari hankalin Mama ya tashi ta Zata wani abu ya samu Abba Sagir na Kofar gida Yana kokarin Daura alwala ya shiga Sallah Tunda an kira Mama ta Fito da Hijabi a Rude tana Fadamai Halin da ake ciki Sallar da bai shiga ba kenan ya Rufa mata baya zuwa gidansu Imran. Su Umma mamaki ya cikasu da Daddy ke maida Zencen ya kasa Zama Umma tana ta maimaita Allah gagara Misali Daman Munari yar"uwan Inteesar ce..? Koda tace ramar data fara ganin Hotonsu tare sai da taga kamarsu Data fada kuma ba wanda yabi ta kanta. Suna cikin haka Baffa Kabiru ya kira Daddy ashe shi yake ta Kiransa yana waya da Inteesar yana Dagawa Cikin Farinciki ya gayamai labari mai Dadi sai yaji yana Fadamai Cikin Farinciki Daddy yace"Wlh nima har mgana ma munyi da ya malami Barrister...Inteesar ta Hadani dashi Allah sarki Rayuwa..! Baffa Kabiru Daga chan bangaran yace"Yanzu haka ina hanyane ban sanu jirgi ba Tafiyar mota ce ni da Ma"u ce,kaima kayi kokari ka Tashi yau din bana so mu kuskure ya sake bace mana kuma ka da ka kira Daada so nake mu bata mamaki har Bintalo na gayamawa yanzu muka gama mgana da ita..chan zamu kwana Gobe in Allah ya kaimu sai mu hadu da kowa da kowa a Dukku..! Daddy yace"Yanzu kuwa zamu kamo Hanya..! Daga haka suka yanke kiran Daddy na Kallon Umma yana Fadin"Salaha Shirya..Ko kuma ke Salaha ki bari gobe Direba ya taho daku keda Hauwa da yara mu a hadu a dukku..Kai Bashir kira matarka ka Fadamata bari na shiga ciki na fito yanzu zamu dauki Hanyat kano ba sai gobe ba..! Baima Tsaya Sauraransu ba ya Shige ciki kamar zai kifa saboda Sauri. Umma ta Kalli Basheer tana Fadin"Kai duk tare zamu tafi..Nima bazan iya Zama sai gobe ba kira matarka mu biya mu daukesu ayi tafiyar gabadaya..! Basheer yace"Umma anya Zata iya..? Kunsan yanayinta ko zamu Kyaleta kawai mu muje..! Umma ta kada kai tana Fadin"Kuma fa hakame..Shikenan kirata ka Fadamata sai muje din..! Daga haka ta bi bayan Daddy shi kuma ya Dauko wayarsa Domin ya Kira Hauwa ya fadamata Halin da ake ciki. Mami Asma"u ta kalli Baffa Kabiru bayan ya gama mgana da Daddy Tana Fadin"Yanzu daman duk wannan uban Wahalan neman da kuke ma wannan bawan Allah yana kano zaune abunshi bbu abunda ya Dameshi..!. Take fada Lokaci Daya tana kara gyara zaman gilashin dake idonta suna Kishingide a bayan Motarsu Kirar prado Direba na gaba yana jansu. Cikin wani yanayi ya kalleta yana Fadin"Bari kawai. Ni kaina naji abun haka..Ace yana nan kusa ammh ya kasa neman kowa..? Kuma daga alamu he is Fine now..! Mami Asma"u ta tabe baki Tana Fadin"This is Selfish yana chan yana Jin dadinsa ya manta da ku..Alhalin kuna nan baku huta ba wajen nemansa..! Baffa Kabiru yace"Saboda Daada nake komai kuma kinga all the blemming akaina Daada ta maidashi so yanzu zan yi amfani da wannan damar na Daukesa na maida mata..! Da sauri tace"Shikenan kuwa..Ammh sam bai kyauta muku ba..! Shidai bai kara ce mata ba sai Dannan Wayarsa yake yi Khamis ya Tura ma Sako ya kira Wayarsa bai Dauka ba.. Umaima da Sajida suna gida suka barsu Umaima ce ma taso zuwa Uwar ta Hana Sajida kuma bata manuna Concern dinta ba she is telling cewa Test zasu fara karatu take bata da Lokaci. Mami Asma"u ita da kanta tayi Ra"ayin zuwa saboda tana so taje taga komai kuma Komai za"ayi so take ayi shi agabanta bayan ikonta da izzanta na akwaita da son gulma da kure Mutane.