← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 190

Sashe 19

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Inteesar da Wuri Tayi barcin Tana idar da Sallar Isha"i Ta ci Danbun namanta da Umma Tayi mata,Ta hada da Lemo har mamana mganar bazai taso mata da Daddare ba..?Umma tace"Wannan ki kyaleta inda kika barta Shan zaki da kayan Kwadayi nan tafi auki babu abunda yake mata..!
Mama tana Dariya tace muna da lafiya ne,Inta dai Intee Kayan Barcinta ta saka ta Bi Lafiyan gado sai barci,ta bar Umma da Inna Amina suna ta Hira Sama sama take jin suna waya da Inni da Mallam Babba,Sai kuma taji Ya Bashir ya kira ta wayarta Data Manta da ita saboda gajiya Umma ta Dauka sukayi mgana har tabama Inna Amina suka gaisa.
Kusan Raba Dare sukayi suna Hira kafin su kwanta Umma kusa da Inteesar ta kwanta,Ita kuma Mama ta yada katifa ta kwanta.
Da asuban Fari suka tashi..Mama ta Fita waje ta saka musu Ruwan wanka kana tazo tayi sallah Bayan ta idar suka gaiggaisa ta kara Fita Bayan Fitantane,Umma ta karayima Inteesar fada tana Nuna mata ta Rika Taimakon Mama da wasu ayyukan Inteesar tace Insha Allahu.
Mama tayi musu abun karyawa bayan ta juyo musu Ruwan wanka Umma ta Farayi kana Inteesar,suna gama Shirya suka iske kayan Karyawansu tea da Buredi da Soyayyah kwai sai Umma datace Kosai take so da koko suka zauna suka karya atare,Suna Hira cikin Sha'awa Inteesar bata wani ci Abun kirki ba Bata iya cika Cikinta in Zata Fita wani waje ta Dade,Umma ta matsa mata sai da ta saka wata Sabuwar amtafa da Ummanta Ta Dinkamata Doguwar riga Chiganvi mai kalan green ssi tayi amfani da green din mayafi da Takalmi da Jaka.
Sagir ma yayi wanka yana Dakinsa yana karyawa sanda Daddy ya karisowa shi ya Fita yayi mai Jagora zuwa Cikin gidan suka gaisa da Mama Da Umma lokacin sun gama suka Tashi suka Fara Shirin Tafiya.
Daddy ya duka har kasa yana Damka Amanar Inteesar wajen Mama tace ta karba Tayi alkawarin Zata kula da ita kamar yadda Zata kula da Sagir.
Yaji Dadin haka ya Dire mata kudi 30k tace bazata karba ba ya Fice bai Dauka ba.
Umma ta Dauka ta bata bayan ta Hada mata da 10k tace ta Rike ahannunta Mama nata Godiya Inteesar kuma sai Hawaye kamar sallaman kenan bata Dauka haka abun yake ba da bata Zabi Karatu a Kano ba.
Har waje Mama ta rakasu tana Godiya Tana Daga musu Hannu.Umma ta shiga Gaba Inteesar da Sagir abaya wacce ke ta Sharan kwallah Daddy na gaba yana Tuki hankalinsa na kanta kamar shima ya saki kukan.
Daganan basu Dire ko"ina ba sai Cikin Jami"ar Bayero,Sagir bai Rabu dasu ba sai da komai na Inteesar ya kamallah Zata Fara Daukan karatu Daddy har bakin Hall din inda yan Department din su ke karatu suka Rakota Wato Itama Zata karanta Fanni Tsumi da Tanadi wato Economics.
Inteesar Tayi kuka kamar Ranta zai Fita ta makalkale Daddy taki sakinsa Harta Umma sai da ta sakata kwallah,dalibai suna ta wucewa suna ganin abun mamaki kuka a jami"a..? Kamar wata yar sakandiri.
Dakyar ta saki Daddy,bayan ya Share mata Hawaye,Ya lallasheta kana ta juya ta shiga Hall din Tana Daga musu hannu.
Bayan ta Shige ne Sagir sukayi sallama yace shima zai Shiga karatu ne,Daddy ya kara Damka Amanar inteesar a hannunsa yace bakomai yanzu hakama Umma ta bashi Lambarta zai jirata su gama karatu su koma Gida Tare kafin ta saba Daddy yaji Dadin haka 10k ya bama Sagir ya karba yana ta Godiya Daganan sukayi sallama suka Shiga Mota suka kama Hanyar kaduna shi kuma ya wuce Department dinsu yana ta Sauri Tunda yasan an Shiga Tun Dazu!
Wayarsa ya Fito da ita yana Dubawa yana tafiya,karamin tsaki yaja ganin har yanzu bai ga kiran Imran ba alhalin tun safe yake kiransa bai Daga wayarsa ba Jiya kwata kwata basu hadu ba yadai kirasa yace ya Turamai lambar Baba Manu ya tabbata ya kai mai kudin Da sukayi mgana ne,Yasan waye Imran in yace zai yi abu baya saba alkawari zai yi din ne yana so yaji yau su Baba Manun zasu je neman auran..? Ammh bai Daga kiransa ba Shiyasa har ya karisa cikin ajin yana ta sskin tsaki.!
Abunda Sagir bai sani ba jiyan Banki Imran yaje ya Ciro kudi a Bankinsa wanda baya amfani DashivSai Lokaci bayan Lokaci,Sai kuma yaje Banki ya Cike Form yake iya Fidda kudi Gabadaya kudin bankin nashi Dubu Dari uki suka Rage bai yi mamaki ba yau da gobe bai bar komai ba yana Cire kudi Lokaci Bayan Lokaci yayi Hidimansa kanar siyan takalma,Kaya da Sauran abubuwan da baza"a rasa ba!
Sauran dawaniyar Yusuf ke gudanarsu da albashinsa in ya gagara sai ya taba kudin Dake Bankin Abba ko na Marigayi Yayansu Nura saboda Dawaniyar Abba da Likitan Dake zuwa Gida Dubashi da kuma Dawaniyar mganguna,Ammh shi baya karba ko Naira Biyar wajen Yusuf da kudinsa Daya tara lokacin Daya fara aiki a inda suka zauna yake amfani.
Bashi da Zabi Dubu dari Biyu 200k,ya ciro ya Dawo Gida a kuma Lokacin ya kira wayar Yusuf yace ya sanar ma Safiya ta Fadama Babanta mgabatansa suna tafe gobe,ya kashe nan take kuma ya kira Sagir yace ya bashi Lambar Baba Manu yana Turomai ya kirashi yafadamai sunansa yace ga kudin nan zai kawomai shi kuma yace ya bari zuwa anjuma yanzu yana gareji ne.
Haka kuwa bayan Isha"i Imran yaje yakai ma Baba Manu kudin yau ko Rakiyar Sagir bai nema ba.
Yusuf kuwa bai yi mamaki ba Sanin Halin kaninsa Duk Abunda yace zai aikata baya Runtsawa sai ya Tabbatar dashi..Safiya ya kira ya Fadamawa,Sai taji abun kamar wasa Cikin Tsoro Ta sanar ma da Mahaifiyarsu Hajiya Mero ita kuma ta sanar ma da Alhaji Alhassan bayan ya Dawo ya Cije a lebe a Fili ya Furta."Allah ya kawo su lafiya..!
Domin ya gama Shirya abunda zai yi goben da Zarar sun zo..Shi da kimarsa da mutumcinsa agari bazai bari saboda Dalilin Safiya wannan Shegen yaron Mara kunya ya Zubarmai da Daraja ba.!

*Ba na fara saka Lokacin Posting bane kamar yadda wasu ke Tunani ba,Ni bana Ware wasu ranakun Lokacin Posting,Ina yi duk rana alokacin da na samu dama da Lokaci sai dai in Rashin Lafiya ko ciwo ko wani Uzuri,Domin daman kana naka ne Allah yana nashi na Allah kuma shine Daidai Jiyan nan na wayi gari bani da Lafiya shiya kawo Tsaikun Rashin posting dina ajiyan..Ina ganin Comments dinku ina matukar godiya Yan Wattpaddian Voting dinku yayi kasa fa ya kamata ku kara kaimu nayi muku alkawarin Bazan baku kunya ba Insha Allahu*

*Shakira..*
3/22/22, 23:03 - Ummi Tandama😇: *GIDAN MU..!*
_(Our House)_
*Book 1*

*Wattpad:Jamilaumar351*
*Mallakar:Janafty❤️*

*DEDICATED TO:*
*Aisha alto(Sisinah)*
*Chubado muhammad(Uwar dakina)*
*Yahanasu Soupnass(Qawalli1)*
*Kausar salis(My jika)*
*Rahma Ladingo(Dota)*

*🅿�08*
Chapter 19 · 0% Book details