Sashe 160
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
gabadaya yana Fadin"Insha Allahu zan taimaka muku.! Mai adaidaita ne ya gaji da jira yayi hon kana suka kara Sallama Sagir ya shiga Imram na Dagamai hannu suka Wuce kowa na Dauke kwallarsa. Jiki ba Laka Imran ya Taka ya dawo Gidan sa yana Kallo da nazarin anguwan da kansa ya Rufe get din Kana ya taka zuwa Cikin gidan ya Kulle Kofar Falom a aransa yana Fadib"Lalle na yarda nabar gida..Imran na kulle gida..? Sai da ya Murmusa Har zai shiga Dakinsa ya fasa ya Tunkari Dakin Da Inteesar take ya Tura a Hankali sai ta Bude bai Shiga ba kansa ya Leka ya Hangota Tsakiyar gado Cikin mayafi ta Dungule Tana Ta kuka sai ta Bashi Tsausayi sai ya Bude Kofar gabadaya ya Shigo Kafafunsa suna Taka Italian Cafet din Daya malale Bedroom din Bataji Takun sa ba ballatana Bude Kofarsa,Tadaiji mganar su Shida Sagir a Falo da Farko har Tsorata ma tayi kafin ta gane sune kawai taji Muryansa a saman kanta. "Kinsan bana son yaawan kuka ko..!? Haka ya fada yana Tsaye Gaban gadon hannayensa Zube Cikin Aljihun Wandon Kayan Dake jikinsa ya Zuba Mata Idanuwansa yana kallonta da Duk Zuciyarsa. Dagowa tayi ahankali jajayen Idanuwanta da suka tasa saboda kuka suka Shiga Cikin nasa gabadayansu sai da Zuciyarsu ta amsa Shi yayi Saurin kauda kai yana Fadin"Subahanallah Maryam kuka haka..? Mamakin yadda ya Kira sunanta taji yasa Hawayenta suka karo ta Runtse ido kafin ta Bude akansa Karisowa yayi gabanta yana Fadin"Look nifa kinga ban iya Lallashi ba..Kuma kowa yace na Kula Dake ban iya da wannan Shagwabar taki Intee kiyima Girman Allah ki Daina kukan nan kin ji ko..? Kallonsa Take yi Cikin so da kaunarsa Mganarsa tana kara sakata Dariya Sai dai bata Daran ba Idanuwansa ta kallah Taga sun sauya shima kamar yayi kuka yasa tace"Kai ma kayi kuka ne..? Tafada Tana lamgwabe mai kai Cikin Dabi"arta Daya zame mata jiki Saurin Kauda kai yayi yana Fadin"Kuka..! Ni ban yi kuka ba..! Yafada Lokaci Daya yana Dakuna Fuska Mirmishi Tayi tana Hawaye tace"Nasani..Kayi kukan Rabuwa da Abba da ya yusuf da Munari ko..? Nafada tana kallonsa Shima kallonta yake da Dukkan Zuciyarsa Kai ya girgizamata yana Fadin"Anni..Anni na Tuna..! Inteesar taji kaunarsa ya kara kamata da Tsausayinsa Bataasan Sadda tace"Allah ya jikanta da gafara..da Sauran duka musulmai nima ina jin Zafin Dakake ji Ya Imran..! Nima ina ta kuka da zan Rabu da Umma da Daddy na da Ya basheer..Ina ta kuka..,! Ta fada Lokaci Daya Tana Fashewa da kuka Imran ya Dafe kai yarasa Mafita ganin Tana ta kuka yasa ya Zauna gefenta batare da Tunanin komai ba ya jata Jikinsa ya Rumgumeta kamkam yana Fadin"Intee plz..Ki bar wannan kukan ni ban iya Lallashi ba..Bansan ta ina zan fara ba..! Ya Fada Muryansa na karyewa kamar Zai yi kuka shi ya karama Inteesar Rauni Ta kamkamesa shima suka Hade Waje Daya suna Jin Bugun Zyciyar Juna Imran yana Shakan kamshinta yana jinsa kamar yana Wata Duniya kanta yake ta Shafawa alamun Lallashi. Yana Fadin"kiyi Shuru..! Dole tayi Shuru Dolenta ta karbi Wannan Lallashin da Imran ya Tattaro Duka Karfin Halinsa yanayi mata Sai daga yaga Tayi shuru kana ya Rabata da Jikinsa yana kallon Fuskarta yace"Kin yi sallah..? Kai ta girgizamai kafin tace"La"asar kadai nayi..Ban yi mangariba da isha"i ba..! Tafada Tana kallonsa Shima kallomta yake yi kafin yace"Ni kuma nayi mangariba Tare da su Abba Isha"i ne ban yi ba..bari najr nayi wannka In Dauro alwala kema ki tashi kiyi wanka kiyi alwala kiyi mangariba sai nazo mu yi jam"i muyi Sallar Isha"i Tare ko baki so..? Inteesar tace"Ina so mana..Ai bamu da kowa anan sai mu kadai ko.? Mirmishi yayi yana Lakuce mata Hanci bai ce komai ba ya Mike ya Fice ta Bisa da kallon Kauna yana Fita ta Mike Daman Less din Jikinta ya Dameta Tiolet ta Fada daman Tun kafin Fitan su Anty Safiya sukace tayi wanka Kukan data Fara ne ya mantar da ita komai. Tayo wanka tazo ta Shafa lotion da Turare,kayan barcin ta acikin na Gida ta saka wata riga doguwa mai Taushi Saboda kayan suna cikin akwati kuma bazata iya Bude su ba Allah yasa Munari Duk ta Hado mata kayanta Taji Dadin ganin Harda Littafan Karatunta gobe karfe 8:00am na Safe suke da Jarabawa ga Gajiyan Biki Da Zirga Zirga bata gama Sakinta ba