Sashe 158
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Karfe 10:00am na safe aka Sada Inteesar da kayattacen dan madaidaicin Gidanta Dake Alu Venue anan cikin garin kano,Ta samu Rakiyan Mama da Maman Nasara da Anty Uwani sai su Inna Maimunatu da su Inna Bintalo da Sauran Tawagan Matan su Basheer da na Anty Safiya da ita kanta suka Sada Inteesar har saman Kayattacen Dakin Barcinta Kan gadonta na Royal bed mai kyau da yarari wanda yaji Shimfidun alfarma sai wanda ya gani bayan sun Umarceta da Tun kafin ta shiga Gidan ta Dafa Ginin Gidan ta karanto addu"an kariya da Zaman Lafiya Acikinsa da Dukkan alherai na Har Abada. Kafin a wuce da ita Abba yayi mata Nasiha sosai da kuma Fatan Zama Lafiya Tsakaninta da Imran ya kuma Horeta da sai tayi Hakuri Sosai sanin Halin wanda Zata Zauna dashi An kaita da Wuri ne saboda Za"ayi Walima,Atashi karfe Biyu na Rana akwai Wadanda zasu koma Gida yau Saboda ayyukansu kamar su Khalil da su Sa"id yau zasu koma Gida. Duk wanda yaga irin Uban Dukiyan da aka Narka a wannan gidan sai kaji yana Sakama Baffa Kabiru albarka ana Fatan Allah ya bar wannan Zumuncin Har gaban Abada,Kowa sai Santin gidan yake Kitchen kuwa shima ya kawatu matuka Umma ce ta Roki alfarman a bar mata Kitchen din Ta gyara a Mtsayinta na Uwa sai aka Barmata Lalle ta Aurar da Autarta Sai wanda ya gani Kayan abinci cike da Store wannan aikin Duka na Daddy ne Ba abincin da Babu aciki Fridge kuwa Cike da kayan Cefene wannan kuma aikin Yusuf ne yasan Waye kaninsa Careless ne sosai kan Abunda ya Shafi Cin Abinci Shiyasa ya gama da Wannan Barayin ya Tabbata Cefanen zai matukar basa Wahala. Irin su Anty Aneesa da su Fareesatu sai Daukan Hoton Gidan suke su Munari kuwa sai Faaman Daukan Hotuna suke yi ko gajiya basa yi Kowa yana Nuna Murnansa a Fili banda yan Bakinciki irin su Inna Bintalo Har Video gidan sai da ta Dauka ta Turama Mami Asma"u Tana nuna mata Irin Kudin da Baffa Kabiru ya bar nartar kan wanda ya Saki yarsa da Inteesar din da aka yi mishi auran Tura Haushi da ita. Mami Asma"u Tun Jiya Take kwance bata da lafiya ta gama Sarewa da al"amarin Baffa Kabiru ta gama yarda ya Juyamata baya kuma bai da Niyyar Dawowa gareta,Daada da yan"uwansa sun yi musu Farraku lokacin Dataga Hoton Imran da Inteesar Awajen Dinner sai da kwalla ta kawo mata A zahirin gaskiya Imran bai da makusa ko D'anta Khamis Wlh bazai jera kafada Dashi ba Cikin Maza Dubu Sai an Tona za"a samu kamarsa anya anya ba Gaskiya bane Tana da Sonkai.?ta so kanta da yawa yasa bata Fahimci Babban goron da Allah ya Kashe yabama yarta ba sai Rudin Duniya da hujjarta mara Tushe Ballatana makama ta Ruguza komai ta Bata komai Karshenta itace tayi Biyu babu An Saki yarta Sajida Tana chan Tana Ramewa Saboda Damuwa itama Gatanan Gotai Gotai Da ita Miji ya Saketa ta dawo Gida Zawarci Itafa bata yarda ma ta Fara Kirga kwanakin Iddarta ba gani take kamar Wasa Kabiru yake zai zo ya Dauketa su koma Gida bai Saketa ba. Da Bintalo ta Turo mata Video gidan Tagani Batace mata komai ba ta Fara Jin Haushinta Taya zata Rika Turo Mata Abunda zai Dagamata Hankali Ita kuma ba wani mganin Matsalarta Zatayi mata ba Shiyasa ta Kashe Wayarta bata son ta Dameta da Tseguminta wanda ta Saba kuma ya Zame mata jiki gwara ita Tana Gidan Mijinta kuma ya"yanta ba wacce aka Taba Saka ta zama karamar bazawara irin y'arta Sajida,kuma duk fa aje a dawo Daada uwa take ga Bintalo kuma kabiru da su Mustapaha Shakikan yan"uwa ne gareta Duk inda akaje ita ce ke cikin Bala"i ba Bintalo ba Shiyasa ta Kashe Wayarta abunda Taji ya Isheta bata Kaunar kuma ta kara jin wani abunda zai yi barazar Tafiya da Numfashinta. Karfe 12:00pm aka Fara Walima Malama Juwairiya Anty Safiya ta gayyato an saka Kanofi a Haraban Gidan Duk da bai da Girma sosai an Fito da Amarya Saboda Wa"azin Walimar Aure,Masha Allah Malama ta yi Wa"azi sosai kan Hakkokin mata ga Mijinta da Hakkin miji kan mata da yadda Mu mata zamu gyara Jikinmu Tare da Shawarwari ga Amarya an Raba Snks da Key Holder da Kofuna da Memo karamin Choter,Hanky da Riguna da Jaka Duka Dauke da Tambarin IMSAR FOREVERâ¤ï¸ðŸ¤© Duk wannan aikin su Munari ne Snks din kuma aikin Umma ne,naga Tarin Mutane sosai a wajen Har da gayyar GMB2BAND GROUP suma sun Hallaci Wannan Walimar Domin Tabbatar da su Team din Imsar Forever ne. Sai Karfe 2pm aka tashi Walimar sai aka Fara shirin gyara gidan da kuma Haraman Tafiya abar Amarya a Muhallinta. Dr Isa Ali argungu sun zo shi da Matarsa Hajiya Barira yima Abba Allah sanya alheri aure da kuma aikin Daya samu yau zasu bi Jirgin Karfe 4pm zuwa Lagos tare da D'ansu Khalil Daga Fagge Suke daman Tunda suka iso suna chan gidan Dan"uwanta Taje Dake nan Zoo Raod ta iske Duka Gidan basa nan yayan nata kadai ta gani suka gaisa duk sun Tafi Biki. Koda suka zo Gidan Abba ma ba Kowa sai su Imran da shi kanshi Abba Duka suna Chan gidan Amarya. Bayan sun gaisa da Abba tayimai Allah sanya Alheri tace akaita Ta Leka Gidan Amarya kafin ta wuce Yusuf ya Dauketa Amota zuwa Gidan Tana zuwa suka Hade da Anty Safiya sai suka Tsaya suna kallon juna Baki Sake Anty Safiya Tace"Goggo Barira..! Hjiya Mero ma ta Kira sunanta itama Cikin mamaki tace"Hajiya Mero..Ikon Allah yanzu nan Da muka Fito Daga Fagge gidanku muka Fara zuwa bakwa nan sai Alhassan kadai muka iske shine muka kariso chan Gidan Dr.Malami ai makotan mu ne,abokin aikin Dr.Ne tare sukayi koyarwa nan Jami"ar Lagos kuma mun zauna ga gida ga gida a Lagos..! Sai kallo ya koma Sama Hajiya Mero Cikin Fara"a tace"Ikon Allah..Ai Safiya Yusuf take aure..! Hajiya Barira ta rike baki Tana Fadin"Ikon Allah..Wato auran da Goggo Tace yayima yarsa a Wulakance batare daya Fadama kowa ba ashe ma D'an Gida ta aura Yusuf Duk Tare da ya"yanmu suka tashi. Iyalan Dr.Malami nasu Nagarta ne ni nan munyi Zaman Amana da Mahaifiyarsu Marigayiya zuwaira Allah ya jikanta Khalil kuma Hala baku Hadu bane ai abokin Imran ne yana nan Tun Ranar jumma"a Hajiya Mero tace"Hajiya yaushe zasu Shaidasa ko ni nan ai na Dade ban gansa ba ko yazo iyakarsa Fagge baya karisowa kece dai in kika zo sai kin kariso..! Nan fa Hira ta Sarke Hajiya Barira Tace"Ai Dayake ga Karatu ga yanayin aikinsa Banki ne ba Lokacin sun gama Sayarma gwannati..! Nan fa Aka Tsinke da Hira Anty Safiya sai Nuna Hajiya Barira take kanwar Alhaji Alhassan ce Da goggo da Wacce ta Haifeta Inna Furare Uwarsu Daya Ubansu Daya Zumunci sosai kowa da yaji yayi mamaki matuka Har Bedroom din Inteesar Mommy ta kaita ta saka Amarya albarka Sauri Take yasa Datace Zata koma Mommy tace su tafi Gabadaya suma Daman yanzusuke Shirin Tafiya yusuf na Haraban Gidan yana Jiranta sai gasu sun Fito nan yake jin Sabon Labari yana ta mamaki haka ma su Abba sukaji Wannan mamakin da suka koma Hajiya Mero kam sai jin Dadi take irin wannan Ranar take jiyema Alhaji Alhassan Ranar da zai ji kunya,Hajiya Barira da Dr.Isa Ali argugu suna bada Labarin karamccin da Mutunci irin na Abba da Duka Iyalansa suna Fadin har suka Zauna dasu na Tsawon Shekaru basu Taba Samun Mtsala ba Shiyasa ko yanzu Megadin Dake Tsaron Gidan nasu da Iyalansa DR.Isa Ali argungu ke Biyansa Duk Wata yace ma Yusuf kada ya Damu shi ya Dauke wannan,Tsakaninsa da Abba sai Godiya anyi Zaman Amana da Mutumci Hajiya Barira da kanta ta Kira Alhaji Alhassan tana Fadamai,Dayake Daganan Filin Jirgi zasu wuce kunya da Nadama suka kara Lullube Alhaji Alhassan ya Godema Allah baya Wajen da wani idozai kalli Yusuf da Abba..?ballatana Imran Daya gama Sanin Duka Sirrinsa. Yaji kunya sanda Hajiya Barira ke Fadamasa Marigayiya Hajiya Zuwaira Kawartace sosai har Allah ya Dauki Ranta Daga Karshe ta Sanar dashi AhalinDaya bada yarsa kyakyawan Ahali ne mai Cike da Nagarta Alhaji Alhassan dai ba baki Zufa kadai ke Ketomai har suka gama mgana yana Tunanin Allah na son shi Dayake ta Nuna mai Ishara kala kala alamace Ta ya Tubarma Allah kafin Lokaci ya Kuremai in ba Haka ba ya Gujema Ranar da Duniya zata san Halinsa na Boye sai ga Alhaji Alhassan na kuka da Idanuwansa kukan Nadama da danasani Ba shakka Imran ya Cika Mutumin Kirki mai kyaakyawan Zuciya a yadda yake kallonsa bai taba Zata Har yanzu bazai iya Tona mummmunan aikinsa ba sai gashi ko alama yaron ya nuna masa yasan Abunda yake yi alokacin Alhaji Alhassan yaji komai ya Fita kansa Nadama ta Shigesa yadaukan ma kansa Alkawarin ya Daina neman mata Har Abada yana me yin Nadama ga abunda ya aikata a baya. Khalil kuwa baisan Wainar da ake Toyawa ba sai da ya Dawo Shima Kiransa Babansa ke tayi Lokaci ya Kusa kada su Rasa Jirgi suna chan Gidan Amarya Shi da Sagir kowa yaja Wacce ta shiga Ransa yana Fadamata Sirrin Zuciyarsa Saboda Dama Daya Take zuwa a Rayuwa. Sagir ya gama gabatar da kansa Wajen Hafsah kuma ya samu shiga kwarai da Gaske sun karbi Lambar juna khalil ma ya gama Sace zuciyar Munari Tuni itama tayi Na"am da mganar na Khalil saboda ai ya gama Haduwa Shima,Tuni suka karbi Lambar juna Duk da kowa nadashi Imran nachan sai Kiran su yake su Hajiya Barira na Jiransa Ya Yusuf zai kai su Filin Jirgi sai da suka gama Kafa Zuciyarsu sai gasu sun Dawo sai Alokacin Hajiya Barira ke nuna mai Hajiya Mero da Anty Safiya,Tasleem ma ashe kanwarsa ce Shiyasa yaga kamar ya santa Tunda shi yama Dade Rabonsa da kano yafi Shekara Bakwai. Imran sai Hararansu yake yi Shi da Sagir saboda wani Hade kai da yaga sunayi Da yayi mgana Sai su yi mai Chaaa,A gurguje akayi sallama gabadaya acikin masu Rakiyan Har da Imran da Sagir suka shiga Motar Imran din suka Rakasu Filin Jirgi basu Baro ba sai da Jirgin su ya tashi suka Dawo a Mota Imran ya wani Hade