← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 190

Sashe 75

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari Monday tun Karfe 7:40am Munari ta biyo ma Inteesar suka Shiga makaranta basu jira Ya yusuf ba Tunda shi sai 8am zai fita BUK old Site suka nufa anan suke lectures dinsu a wannan Zangon karatun na Biyu,Zangon karatunsu na farko Gabadaya sun yishi ne a New site,sai jifa Jifa suna shiga Old site din yin wani lectures din. Sai 5pm na yammah suka Dawo gida Daga bakin Titi mai adaidaita ya ijiyesu suka Tako da Kafarsu zuwa Cikin anguwa Inteesar ce ta Roki Munari ta shigo Ta diban mata Dambun nama da kayan Snaks din Data zo dashi Munari bata da yadda zatayi Dole ta bita suka Shiga gidan Tare ta gaida Mama kafin su Shiga Ciki,Bata wani Dade ba Saboda mangariba ta kawo jiki Abinci sukaci Tuwon Shinkafa Miyar Zogale Mama tayi Sai Inteesar ta Diban mata Dambun naman da yawa dasu Samosan da Cincin da Springrool,da Donot Tace ita dasu Abba Munari ta rasa bakin godiya Domin alkharin Inteesar gareta mai fadi ne haka Jiya Data nuna ma Abba kaya yana ta Saka albarka,Basu baro gidan ba sai da Inteesar ta kira ma Munari Umma suka gaisa Tayi mata godiya. Da inteesar taje raka Munari ta mtsamata sai da ta shiga suka gaisa da Abba da Anty Safiya Ta nuna musu Abunda ta kara bata Abba nata Saka mata albarka Har taji kunya,Itama bata Zauna ba tayi musu Sallama Zata tafi ta Fito Falon kenan Munari ta Rakota taga Imran zaune gefen Abba Yana mai mgana ya kauda kai yana kallon wani gefe Daga alamun dai Fada Abba kemai Shiyasa Fuskarnan ba Annuri.. Lokacin Dayaji Muryanta sai da gabansa ya amsa haka Itama Tana ganinsa taji wani Sanyi ya Shigeta acikin Jikinta Lokaci Daya Duk yadda yaso kada ya Dago ya Kalleta ya kasa sai da Zuciyarsa ta Rinjayi gangar Jikinsa ya Dago yana kallonta Daidai Lokacin itama Shi take kallo,Yanzu adakin Munari ta gama Tambayansa Munari tace ita duk yau bata gansa ba yana Dakinsa sai gashi sun hadu. Lokacin da suka Hada ido sai yaji kamar Zuciyarsa tayi Tsalle waje Daya ta Daina aiki Da Sauri ya kauda kai ya Hade rai Yana wani Dakuna Fuska ganin shi yasa Munari ta fasa Rakon da Zatayi ma Inteesar zuwa Haraban Gidan. Ita kuma Inteesar sai ta kallesa kafin tace"Ina yini Ya Imran..! Haka muryanta a bazata cikin Sanyinta akoda yaushe yi yayi kamar bai jita ba,Sai da Abba yace mai bai ji ana gaisheshi bane kana ya amsa yana wani Tattare giransa Waje Daya..ita dai bata bi ta kansa ba Tayi ma Abba Sallama Daganan suka Rabu da Munari duk da daman ta san Munari ta na matukar Tsorom Imran kamar Ranta bazatayi wani kwakwaran Motsi agabansa ba.. Duk da yana Fushi da ita kan taki cika alkwarin datayi mai bai Fasa ganin ta Rame ba,Kuma Zuciyarsa bata Fasa jin Dadin ganinta ba,muryanta kuwa Dayaji kamar wani Waraka ne Daga Garesa haka yake jin kansa ya rasa gane Meke Damunsa Ballatana ya Dora hakan kan wani Mizani. Cikin Satin kaf su Inteesar basu samu Zama ba Saboda Karatu kullum in suka Shiga makaranta sai yammah Suke dawowa,Saboda sun Fara Karatu ne Gadan gadan ba zama Ga kuma assigment da suketayi akwai wadanda aka bada lokacin basu Dawo ba Shiyasa basu da Lokacin kansu sam. Ranar jumma"a Karfe 7:30am suke da Lecture tun 7:20am Inteesar ta gama Shiryawa ta Fito kofar gida Tana Jiran Munari sun yi mgana tace mata gatanan Fitowa Tana Sanye cikin Doguwar riga atamfa Gold,mai kalan Brown sai da ta saka Karamin mayafinta Sikiws,sai bakar jaka da Bakin Takalminta mai dan Dudu sai wasu littafai a hannunta. Sakamakon Lokacin yayi Safe ne da yawa ba Mutane sosai sai Daidai ku ne ke Wucewa sai yara masu Haraman zuwa makaranta. Tana nan Zaune Tana kallon Shashen da Munari Zata bullo Lokaci Daya Tana Kuma Duba agogon Fatan Dake Hannunta na kamfanin gucci. Sai dai me..? Maimaikon Taga Munari sai taga yayan Munari yana Tahowa Cikin Kayan jugging Riga da karamin Wando duka Farare,sai Takalmin Kafarsa Booth shima Fari ne Tafe yake yana Jogging a Hankali ko'ina na Jikinsa na amsawa gabadaya Muscles dinsa sun bayyana alamun Karfi da Mazantaka. Inteesar tunda ga Nesa ta Kuramai ido bata san ta Shagala da kallonsa ba,bata son haka yake da kyau da Zati ba Shan taba bai dace da Kamili mai Daraja irinsa ba,bakinta ta Saki da Hanci Tana kallonsa batare Datasan me take yi ba Shi kuma Tundaga nesa Daman ya Hangeta sai yayi kamar bai ganta ba sai dai Kallonta Datake Binsa Dashi ne yasa ya kasa Wuceta sai kuma Karamin gyalen Dake jikinta Haka kurum yaji Haushin yadda Zata Tafi makaranta Cikin Duban maza da wannan mayafin da bai Rufe mata jiki ba,,Har ya Tsaya sai wata Zuciya tace menene naka..? Sai kawai ya Kada kai ya wuce Kuma sai ya kasa Zuciyarsa sai ta Fara Zafi da kuna wanda yasa ya Juyo zuwa gareta batare da wani Tunani ba.... Shagalan Datayi da kallonsa yasa bata san ma yazo gabanta ba,Sai dai kawai taji Hucin Numfashinsa agabanta Da Sauri taja baya Tana Rarraba ido Binta yake da kallo Daga Sama Har kasa Bakinta ma yayi Nauyi ta kasa mai mgana sai kallon Zufar Goshiinsa Take wanda ke gangarowa zuwa saman Fuskarsa. Sai da ya Kalleta ido Cikin ido kafin yace"Koma ki Cire wannan Mayafin ki Sako Hijabi..! Yafada kai tsaye cikin bata Umarni a karkashin Zuciyarsa kuma yana Fadin ko bakomai kamar kanwa take gareni Tunda Kanwar Sagir ne,Zai kula da ita kamar yadda zai kula da Tarbiyan Munari duk da ta batamai rai ta yi mai alkawari kuma ta Sabamai. Ita kuwa mamakin kalamansa Taji,sai dai kuma Kaifin Idanuwansa yasa bazata iyamai Musu ba Sai ta Rausayar dakai tana fadin"Ban fa da kalan Hijabin nan..! Tafada Tana nuna mai Kalan Brown din Dake jikin Atamfan,Dan Hade rai yayi kafin yadan Mtsa baya yana fadin"bai zama Dole in an bani Umarni nabi..Ammh ya Zama Dole in na bada Umarni ni abi..! Yafada kai tsaye Cikin Dakewarsa Bata isa ta kara cewa wani abu ba,Ganin yadda Girman Jikinsa duk ya Babbage ko"ina sai kawai ta Juya ta koma Cikin Gida yana Bin kowani Takunta da kallo Zuciyarsa na amsawa. Sai dai Mama ta ganta ta Dawo Data Tambayeta sai tace Zata Sauya Mayafi ne,Wani Farin Hijabinta ta Dauko ta Sakamai hannu wanda iyakarsa Gwiwanta,Ta sagala Hannun ta Dauko Jakarta da Littafanta ta sake yi ma Mama Sallama ta Fice. Yana nan Tsaye inda ta barsa Tana Fitowa Kaifin Idanuwansa yasa ta Fara Jin kamar Zata Harde Jikinta Duk sai ya Fara sanyi bata iya Jure Kallon nan nashi,Kanta na kasa ta Kariso gabansa Kafin tace"Kagani..! Na chanzo..! Tafada Cikin Shagwababbiyar Murya,bai ce mata komai ba ganin Munari Tana Tahowa kawai sai ya Kada kai yayi gaba abinsa Inteesar ta Bita da kallo har ya bace ma ganinta afili ta Furta"Komai nashi na Dabam ne..! Daidai Lokacin Munari ta iso Wajen Cikin mamaki take kallon Inda Imran ya bi ya wuce ta Kalli Inteesar Tana Fadin"Kamar Ya Imran na gani..? Inteesar ta Kalli Munari kafin ta Waske mganar tana Fadin"A ina..? Munari tace"Tsaye anan wajen kuna mgana ko bashi bane..? Da Sauri Inteesar tace"Anya..? Baki lura badai..Wani dai ya wuce ta nan wajen ammh ba shi bane..! Munari tayi Shuru tana Tunanin itafa Taga wani kamar Ya Imran,sai dai kuma Inteesar tace bashi bane,Ganin kamar Ta shiga Nazari ne yasa Inteeasr ta Duba agogon Hannunta Tana Fadin"Muje kin Sakamu makara..In kuma zaki zauna Dogon Nazarin ki ne shikenan..! Munari ta Sauke Numfashi kafin tace"Shikenan Muje..! Daga haka Suka bar mganar suka Fara Takawa zuwa Bakin titi Domin su Samu adaidaita sun kai Titin kenan suna Jiran abun hawa sai ga Ya Yusuf yazo da mota zai tafi Wajen aiki ya Daukesu zuwa Makaranta sai da ya ijiyesu har cikin makaranta kana yayi Kwana ya Dauki Hanyar ma'aikatan su. Basu samu zama ba sai da weekend ta Zagayo,Ranar asabar suna gida Inteesar sunyi mgana da Ya Sadam kan in ta Shirya tamai mgana zai zo ya Dauketa saboda tafi Saurin gane gidan to tayi ma Munari Mgana Kan Zata Rakata ayau din Har Abba ta Tambaya ya barsu sai kuma Bayan ta Shirya Tana jiran Munari Ya Sadam din ya Kirata yace wani Emergency ya taso mai zai shiga cikin asibitin ko Zata Bari sai gobe ne ko kuma da yammah in ya gama abunda yake yi acikin asibitin sai yazo ya Dauketa sai ta kwana agidan sa Gobe sai ya Dawo da ita. Ganin bata Shirya kwana ba kuma bata Gayama Mama ba,sai tace mai kawai ya bari sai gobe sai yazo ya Dauketa Da haka suka Rabu ganin haka yasa tace Ma mama bari ta je gidan su Munari tunda sun fasa Tafiyar sai gobe Mama tace sai ta Dawo Tana Fita suka Hade da Sagir ya Dawo Daga kasuwa ya siyo kayan Dinki Zai shiga tamai sannu da zuwa ya amsa yana Tambayanta ina Zata tace Gidansu Munari yace ta gaida su. Daganan suka Rabu shi ya Shiga gida ita kuma ta kama Hanyar Gidansu Munari. Yana Zaune Saman Motan Yusuf ya Dauko karan Sigari acikin Aljihun wandonsa ya sakata abaki ya Dauko Lether ya kunnata kenan Yana Shirin Maida Lether, Aljihun wandonsa yaji an Dauke Taban Dake Bakinsa Da Sauri ya ware idanuwansa akanta Cikin Mamakin ganinta Domin bai ga Shigowarta ba kuma yana dan jima awajen,Ya fito ya Busa Hayakinsa ne Saboda Abba ya Hanashi shan Taba,Shi kuma bazai iya bari ba sannan baya so ya zama Sillar Sabama Abba Shiyasa ya koyi shanta aboye. Duk da ya Rage shanta ba kamar baya ba Daya maida ita cinsa da shansa ba Batare da yayi mata mgana ba ya mika mata Hannun alamun ta bashi Noke Hannunta Tayi Da kafadarta Lokaci Daya.! Waro mata ido yayi Lokaci Daya Yana Mamakin Karfin Halinta Dakyar ya Bude baki yace mata"Bani..! Kawai ya iya Fada Cikin Dakewa.. Kara Nokemai kafada Tayi alamun A"a Dan Dakuna Fuska yayi acikin Ransa yana Fadin yarinyar nan akwai Shagwaba. Saukowa yayi Daga kan Motan wanda yasa Inteesar tayi baya Da Sauri Tana Fadin"Plz kada ka Dakeni..ga abunka..! Ta fada tana Mikamai Cikin Tsoro wanda ya bayyana acikin Idanuwanta. Sai
Chapter 75 · 0% Book details