Sashe 154
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ranar talata da yammah suka Dira a Kaduna sun iske gida acike da yan"uwa da abokan arziki,Inna Maimunatu da ya"yanta Tun Ranar Monday suka iso,Inna Bintalo ne bata Riga ta iso ba ammh Dangin Umma sun Cika gida ana ta Hidima Nasara Daman already sun yi mgana ta waya tasan da zuwansu,Dayake gabadaya Dinkunansu na ankon da suka Fitar Kudin suka Turama Anty Hauwa gabadaya ta siya musu Nasara tazo ta karba ta kaimusu Dinki Gabadayansu Harda Umaima da Daddy ya siyamata itama Munarin da Hafsah Daddy ya siya musu Tasleem kuma Ya yusuf ya Tura nata kudin Duka ankon,Kayan Lefen Inteesar kuma Umma ta Diba ta Bama Nasara ta Hada da kayan su takai Dinkin Shagon Telan da suke kai Dinkunansu ita da Inteesar tun Tana Kaduna kafin ta tafi kano Karatu. Washagari Laraba Hafsah da Tasleem Suka Dira a kaduna,Hafsah jiya Da Daddare suka iso kano ita da Anty Fareesatu da yara gidan Abba suka kwana nan ita zata Tsaya tayi Bikinta Ita da Anty Aneesa a kano ita kuma Hafsah Damansun yi mgana da Tasleem In tazo zasu wuce Tare haka kuwa akayi,Tare da Tasleem suka Dira Kaduna Alhaji Alhassan bai da tacewa Saboda duk abunda ya Hada da iyalan Gidan su Imran bai da Karfin Gwiwan yin wani Motsi mai karfi Gabadaya ma Sha"anin Biki,Hajiya Mero da Danginta ne suke ta kaida kawo da gayya ma Hajiya Mero ke basa Labarin Wasu abubuwan Saboda ya Shaka. Umaima bata samu zuwa ba sai Ranar Alhamis Ranar da zasu yi Bridal Shower dinsu,Ta jirgin kasa ta zo Baffa Kabiru yayi yayi Ta bari yasa Direba ya kawota tace ya siyamata Tiket na Jirgin kasa Zata iya kai kanta Har Kaduna Bazata gane gidan ba Zata Kira Munari a waya haka kuwa akayi Tana isowa kafin ma ta Kira Munari Baffa Kabiru ya Kira Basheer ya Fadamai yaje ya Daukota in ta Sauka. Daman Tana da Lambar Ya Basheer din ta Kirasa ta Fadamai ta Sauka Daman yana Kusa shi yazo ya kawota Har Gidansa Inda su Inteesar din suke nan fa suka Hade suka Rungume juna Cikin Farincikin ganin Juna Umaima Babu Ruwanta Tana da kyakyawan Zuciya bata taba Duban Inteesar da Duba Ta auri mijin yar"uwanta ba,Tasani komai ya Faru Daga Allah ne SannanTa sani Mami bata san auran Shiyasa ita bata ga abun nuna Wata Damuwa ba ta shigo Cikin yan"uwanta wanda daman Tare suke Shirya komai.. Agidan Ya Basheer suka Shirya kayattacen Bridal Shower dinsu,Nasara ta gayyato Kawayen Inteesar sosai da suka yi makaranta Tare,sun kira mai Decoration yazo ya kawata Haraban gidan komai dai sun yishi Cikin Tsari da Wayewa Khalil da Sagir sun yi kokari Su suka basu 100k bayan Dinner da zasu Shirya Sagir fa gabadaya albarkar Dinki ya Fito Dashi Ana ta Hidima Indai akan Imran ne ko nawa ya Kashe bai Fadi ba. Sun Kira mai Makeup Tazo ta Tsantsarama Amarya Kwalliya mai kyau ita da Zaratan yan"uwan nata Munari da Umaima da Hafsah da Nasara suna Zagaye da ita Kawayen su sunzo sun mata kara sosai Sun Kira Dj yazo sun Chase iya Chasewa Anty Hauwa da yan"uwanta duk sun zo Da kannenta dasu akayi komai Ga Cikinta ya Fito sai Fama Take yi ita da Anty Safiya ga Hidima suna Fama da Ciki agabansu Tiri tiri,Sun sha Hotuna sosai Inteesar tayi kyau matuka Sanye Cikin Red din Yadi Daman kusan Ja kalanta ne sai akayi mata Head da Bakin wani yadi mai kyau yana Daukan Ido Fitted ce Rigar ta kamata Daga kasa an Saki baza Rigar da wani Bakin Tazaran wani yadi mai Raga Raga,An Salaga mata Wani Yadin Fari mai Dauke da Rubutun BRIDE..! Su Munari suma Haka akayi musu Dinkin Sai dai nasu ba"a Sake sa Daga kasa ba ammh su nasu Kalan Lemon Green ne sai akayi musu Kwalliya da Jan Flower suka Sirka suma sun sha Kyau Masha Allah,barin ma Amarya kamar ka saceta ka gudu Saboda yadda Inteesar tayi kyau sosai Sai dai ta Rame kadan Saboda Stress din Maakaranta da Zirga zirga da kuma Fargaban wannan Tarewar. Sai 7pm na Dare suka tashi Daga Shagalin Tuni Hotuna suka Fara yawo a Social media barin ma Group din Marigayi Hamisu Dukku nan suka Turasu Kala Kala yan"uwana saiDauka suke suna sakawa a Status Intergram,Da sauransu suna Tayasu Murna sai dai Ba Ango ba wanda ma yaga Kyallinsa sai dai Sagir sai da ya Nuna mai Hotunan,yafa ga yadda Inteesar tayi kyau matuka sai dai ya kauda kansa bai nuna ma Kwalliyar nata sun Dakesa Har yaji yana son kallonta bai ko son Kiftawa. Basu yi waya ba Tunda suka je Kaduna sun dai yi mgana Lokacin Tana Dukku Har tabama Daada sukayi mgana Inteesar din bama ta san ina Isalin Wayarta take ba Tana Hannun Munari Shi kuma Imran aiki yayi mai yawa ga Gida ya Fara cika da Jama"a Jiya ma Dakin Sagir ya kwana saboda baya son Hayaniya Mama ta na chan Gidan itama suna ta Hidima ya Kirata Sau Daya Munari ta Dauka yana jin Muryanta ya Kashe bai kara Kira ba ita kuma bata Nemesa ba sai da yaga Hotunan nan ya gane ga Shanshancin da suka Tsaya yi kenan Inteesar ta manta Dashi,Harda Videon da sukayi Rawa suka saka Inteesar a Tsakiya suna ta Rawa su Munari ita dai batayi Rawa ba Tana Tsakiya Tana Mirmishi Hade rai yayi yana mamakin yara kanana sun iya Iskanci haka..? Shiyasa yace baya son Bidia a Bikinsa bazai Dauki wannan Shanshancin ba. Washegari kuma Jumma"a A Kaduna aka tashi da Yinin Biki,yinin Bikin Gabadaya a Gidan Daddy zasu gudanar Harda Lonching din wanda Za"a Fara da karfe Biyu na Rana a tashi Shida na yammah kuma a Haraban Gidan zasuGudanar da komai. Imran bai so yazo kaduna ba Daman yayi niyyar ba zo ba din Sagir yace saiyaje Ya Yusuf ma Haka Sadam da Sa"id ma sun iso sukayi mai Chaa suma Kadunanan zasu su Dagachan ne Gobe zasu Dauko Amarya da Tawaganta Imran yaso ya Zille sai dai bai isa ba Abba ya saka baki kuma Daga Wajen aikinsa Mr.Sulaiman ya bashi Hutu na Ranar yace yaje bakomai ya kuma Hada damai Fatan Alheri bai yi mamakin a ina yaji ba Tunda yana Tare da Katon Ameobe Sagir kenan. Ai bai gama mamaki ba sai da Khalil ya Kirasa yace mai yanzu zai Hawo Jirgi ammh ta kaduna zai Sauka su Hade ta chan Tun jiya yaso tahowa bai Samu Dama ba Dr.Ali isa Argungu ne suka Taho jiya Hajiya Barira tazo Duba Innarta Dake Fagge bata jin Dadi Daganan zasu zo suyima Abba Allah sanya alheri kafin su koma. Imran ya kasa mgana Lokacin da Sagir ya Fitomai da Sabuwar Bugaggiyar Shadda Gezner wanda taji Dinkin Hannu na Zamani Dinkin Riga Sharashara da Babbar Riga,Aikin jikin Shaddan Baki ne Haka ma Hula kansa baka ya sanya da Bakin Takalmi Rufaffe na Matar Damisa Agogon Hannunsa ma Baki ne shima na Fata ne mai kyau da yarari duka aikin Sagir ne shima Irinta ya saka sai dai Tashi ba Babban Riga Imran yayi kyau Har gaji da kyau kamar Wani Wata Dan Daran Goma sha Biyu yadda yake Walwalin Daga Kallon Farko zaka Fahimci Yana cikin farinciki duk da Fuskarsa bata wani Saki ba sosai. Lokacin da sukaje yima Abba Sallama sai da yaja Dogon Tasbihi ga Allah Domin yadda Imran ya zama kamar Wata acikin Taurari ya Dafasa ya yi mai addu"aTare da sakamai albarka Daga Karshe ya Bisu da Allah ya kaisu Lafiya Sagir da Imran Motar Yusuf suka Shiga Sa"id da Sadam suka tafi a Motocinsu tunda suna tare da abokansu ne suma,Karfe, 1pm suna cikin Garin kaduna a masallacin Sultan bello sukayi Sallar Jumma"a kana suka karisa gidan Daddy wanda dashi da Ya Basheer din duk sun gansu nan a Masallacin Tare sukayi Salla bayan sun idar suka Dumguma gabadaya Koda suka isa an kawata Haraban Gidan da ado mai kyau an saka Kanofi da kujeru duka aharaban Gidan Masha Allah ga masu abinci nan kala kala Daga mabambamta Gidan abinci ga Moticin Ababen sha nan sai Wanda ka Zaba Falon Bakin Dake kofar Waje Daddy ya shigar da ya"yan nashi kana ya Kira Umma ya Fadama ta gasu Imran sun iso,Lokacin su Inteesar basa nan suna Shagon Sallon in da za"ayi musu wankin Kafa da Kwalliya Kunshi sunyi jiya da Safe,achan zasu Shirya ga kawayensu nata zuwa basu Dawo ba.. Sagir Hafsah ya Kira ya Fadamata sun iso tace basa gida ammh gasu nan Zuwa su an gama musu Amaryace kadai ta Rage ana karisa Shiryata,Anty Hauwa ce da kannenta suka yi ta Hidima da su Imran ta Bangaran Abinci da ababen sha,Sai Wurga ido yake yaga ta inda zai Hango Inteesar bai ganta ba Sagir ne ya Fadamai basa Gida ga Inda suke Dakuna Fuska yayi yana Fadin Shirme. To bama su Dawo ba Khalil ya Kira Waya yace ya Sauka,Sagir yayi yayi ya Tsaya azo a Daukesa yace su bashi address zai hawo Mota haka kuwa akayi Ya Basherr ya bashi Kwatancen Cikin Lokaci sai gashi nan suka Rumgume juna da Imran da Sagir da suka Riga suka Saba ta waya nan da nan Sagir ya gabatar mai da Nasa kayan ya Kwabe Shaddar Jikinsa shima ya Chakare Masha Allah abokan ango suma sun Fito Ras dasu Masha Allah. Su Inteesar sai wajen uku saura suka Dawo Gidan,Anata jiransu Lokaci ya Tafi suna shigowa Cikin Gida Goggo Maimunatu ta Dauki Gudan ga Amarya nan saboda kyan da Inteeear tayi,Sanye Cikin Wani Ubansu Less cikin na Lefenta ne mai kalan Blue da Golden Dinkin Riga da Zani Ciki da alaku anyi mata Nadin Golden din Head a saman kanta kafarta Cikin Wani Takalmi mai igiya mai Tsini shima Golden haka Karamar pos din Dake hannunta,Tasha Kwalliya Tayi kyau Har tagaji da kyau su Munari kuma suna Sanye da Atamfar yinin Biki ne suma sunyi kyau har sun gaji da kyau. Maman Nasara ta ta ja Hannun Inteesar din zuwa Dakin Umma,su kuma suka Nufi Falon Baki inda su Sagir suke suna Shigowa Kallo ya Dawo kansu Khalil na gefe ne yana kyalla ido yaga Munari ya Rude baki Bude yace Wow...Shima Sagir Hafsah kadai yake Kallo Domin ta gama Tafiya da Imaninsa. Imran