← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 190

Sashe 129

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Marigayi Hamisu Dukku har ya rasu alkalin alkalai ne na Kotun musulunci to shi Waye..? Alhassan ne fa wanda ubansa ba kowan kowa ba almajiranci yazo yi garin Kano Allah ya taimake sa Da Taimakon Mallam yayi karatu da kuma alfarmansa ne har yau yake kan wannam mtsayin shi ko Rabin Dr bai kai a iliminsa ba,Karamin alhaki ne in kazo matakin rayuwa a kan Abba da Zuru"arsa. Yusuf ya Fita Haraban gidan yayi waya sai ga su Baba Manu da Matarsa Kaltume da Mama da Sagir sun kawosa daman Tuni yaji Labarin komai a bakin Mama Shiyasa Dayaji wannan abun Faricikin yace ta kawosa yayi musu murna da Yusuf suka Fara jin karo yaji Dadin ganin Baba Manu saboda bazai manta dashi ba,Yayi musu jagora zuwa Falon gidan su inda su Abba ke zaune bayan sun gaisa Daga Waje Abba ya mike Cikin girmamawa Sanda Yusuf ya sanar dashi Baba Manu ne baban Sagir wanda ya karbomai Auran Safiya Alhaji Alhassan dake Zaune yana ganin Manu aransa yace Shikenan na Mutu Daman yana zaune ne yana Allah Allah kada tsagerin yaron nan ya Shigo Kada ya yagemai Sauran Rigan Mutumcinsa Dayeta ita a wajen Abba. Sun gaggaisa Cikin Aminci da Farinciki Abba yayi ta ba Baba Manu Hakuri Da baisamu zuwa yayi mai Godiya ba Baba Manu yace Haba ba komai Shi kanshi yasan Wani kaya fa sai Amale Yusuf sun wuce Raini da Wulakanci Tunda yaji ance Yaya yake Wajen mijin Salaha kanwar Amina yasan Babban goro sai magogin karfe. Sai da aka Natsu yama Lura da Alhaji Alhassan nan take ya Kira sunansa ya basa Hannu yana Dukar da kai da Kifta ido ya amsa mai shi bai ma Lura dashi ba sai acikin Ransa yaji Dadin Da Alhaji Alhasan din ya gane cewa Safiya batayi ma kanta Zaben Tumin Dare ba ta shiga Ahali irin Ahalin da kowa Ke Burin nashi ya kasance. Munari da Inteesar keta Hidiman kawo ma baki abun sha da kayan Motsa baki Sagir dai Dakin Imran ya shiga ya samesa zaune kan Tsakiyar gadonsa yana ta aiki Bisa karamar Laptop dinsa nan ya Zauna suna gaisawa jin cewa da Baba Manu suke Imu ya mike ya Zira Jallabiya ko bakomai yana ganin kimar Baban Sagur din ba Dan"uwa bane ba kowa ba ammh yayi musu Ranar da wani nasu bai musu ba. Ai yana Fitowa Falon Alhaji Alhassan yaji kamar kasa ta Tsage ya Fice ga Sanyin AC ga komai ammh Sai zufa yake yi,Imran bai ma gansa ba da Baba Manu suka gaisa sai su Mama da suka Fito Daga Shashen Anty Safiya Zasu tafi ne ma,Kawai yaji Alhaji Alhasan na gaisheshi kowa awajen sai da yayi mamaki sai alokacin Imu ya gansa yako hade rai ya amsa lokaci Daya yana Bashi Hannu sukayi Musabaha yana jin Sadda Hannunsa ya Jike da Zufa sai rawa jikinsa yake yi Dariya ta kamasa aransa yace kowa ya Tuba don Wuya ba lada Saboda Safiya bazai so asirin Mahafinta ya Tonu a Bainar nasi ba sai dai zai so ace ya Tuba kuma Allah ya Shiryesa ya Dawo uba nagari kamar kowaa yasan dai shi Imran bai jin mgana ammh Wlh bazai iya Fallasa asirin da wani ya Rufe ba har ga Allah yana mai Fatan Shiriya. Su Baba Manu suka Fara Tafiya sai gashi Har da Ya Imu a yan Rakiya,sun Tafi kenan Ba Dadewa suma su Alhaji Alhassan suka wuce bayan yayi ta Dokama Mommy kira ta fito su tafi kunya yakeji gani yake kamar Kowa yasan abunda yake aikatawa Abba Har Bakin Mota ya rakasu Mutum mai Saukin kai inji Mommy Anty Saratu tace Dagani ya Gado Dattako da Mutumci shidai yana jinsu Tak bai ce kunyar duk ta gama kamasa sai da suka isa gida ya iya Ssuke Numfashi Anty Saratu nan zata kwana sai Gobe Zata koma Gidanta nan suka baje afalo suna labarin Karamcin Gidansu Yusuf anan me yake jin Labarin Safiya nada Ciki sai yaji Dadi ko bakomai zai yi Farinciki in ya Hada zuru"a da Abba Shi kanshi ya sani Babban Goro ai sai magogin karfe.
Chapter 129 · 0% Book details