← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 168 OF 190

Sashe 168

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Fadin"Kiyi maneji ba kudi a Hannuna..! Daga haka ya Fice ya Turo mata Kofar sai da Ta Tabbatar da ya bar Gidan kana ta Mike Zaune ta jawo Ledan Tana Dubawa ai data Gwada sai da ta Rike baki Tana Fadin"Tabdijam..Ni ce Zan saka wannan kamar wata Malama..! Tafada Tana kallonta ta Madubi,Wata Zuciyar tace"Kuma ki ki sawa..Abu ya Zama Bala"i..Kila ma wannan karon Har da duka! Tuna Haka yasa ta bata rai Hijabin kala Goma ne kala kala gashi an yi musu Dinkin Zamani. Bata bar gidan ba sai ta Soya kwai tasha Da Tea da Buredi wanda sai da ma suna Hanyar dawowa Gida Ranar tagani tace su Tsaya su siya kana ya Tsaya ya siyan musu shi ba ci yake yi ba ballatana Yayi Tunanin siyowa. Dakyar ta samu Daya daga Cikin Hijaban ta saka Kalan pick Zanen Material din Jikinta Har kasa ya kaimata ya Rufemata Diga digi ya ta iya Matar Imu take in batajin mgana Mganinta Zai yi a Dake ka kuma a hanaka kuka kuma aki Lallashinka sai dai ka gaji kabama kanka Hakuri..! Lokacin da Munari taganta a makaranta Sai da ta Kusa Kaiwa kasa Saboda Dariya Inteesar sai kwal kwal kuka Cikin Shagwaba tace"Duk ban yi kyau ba ko..? Ba yaya Imran bane ya kawomin wai kada ya kara ganina da mayafi..! Munari na Dariya tace"Tab..Mrs Imran Abubakar Malami..! Take Fada Tana Dariya wayarta ta Fito da ita Tana Fadin"Bari nayi miki Hoto naji Dadin Bama su Nasara Labari..! Daman Kiris take jira sai ta sakamata kuka ganin haka yasa Munari ta Daina Dariyan afili Sai da Taga Inteesar din Idanuwanta duk sun kumbura alamun tasha kukabata Tambayeta ba sai da suka Fito Paper Course mate din su suna ta Murna Final Suka samu Waje suka Zauna Munari ta kalli Inteesar Dake Fama da Hajibi Tana Fadin"wai ya imun dukan ki yayi ne naga Idanuwanki sun Sauya..?in dai kuwa ya Dakeki Wlh Tashi muje office din Abba ki Fadamai kan me..?aure ai ya wuce wasa..! Inteesar ta Dago tana kallonta kafin Tace"Wlh bai Taba Dukana ba..! Munari tace"To me ya yi miki..?daga ganinki kin sha kuka wannan i don naki..! Inteesar ta kauda kai batayi mgana ba Munari tace"Shikenan Tunda baki san Gayamin ammh Zan Fada miki gaskiya in baki Mike Tsaye ba Wlh Ya Imu Wahala Zai ta baki kafin ki gano kansa Kingama Jigata..! Inteesar ta Juyo tana kallonta Kafin tace"Uhm..Naga alama..Ranar da naje gidan nan..!., Nan ta shiga bama Munari Labarin abunda ya Faru ta Karishe da Fadin"Haka ya dinga min tsawa da Fada ina kuka bai Lallasheni ba yace ma in na kara Damunsa yazo nan sai yayi kwallo Dani..Ni ba ance Miji na Lallashin matarsa ba ni Wlh Ya Imu bai Taba Lallashina ba Munari in ma Fushi zan yi baisan inayi ba sai don in nagaji na Hakura dakaina anya Yana Sona..? Munari ta gyara Zama anzo Wajen Data ke son zuwa Cikin Hikima tace"Wlh yana sonki..So mai Tsanani ma Daya kai ku wannan Mtsayin in da baya Sonki ko sama da kasa Zasu Hade bazai Aure ki har ya Zauna dake ba Baki ga Sajida da baya sonta ba ya Saketa.ba..?haka Ya Imu yake Dan kafiya Dan Ra"ayi bamai Turasasa yayu abu Dole sai Abba ammh ko shi baya yarda yasakashi ya Zauna da abunda baya Ra"ayi..! Inteesar ta jinjina kai alamun gamsuwa kafin tace"Ai bai taba Cemin yana sona ba..! Munari tace"Ai bazai fada ba..Ke ce Zaki Sakashi ya Fada ma bai sani ba..! Inteesar tace"Ta yaya..? Munari tace"Baki gane ba..?tsaya ma wai Kun Fara amarcin ne ko kuwa Dai kina nan kina Jiransa..! Inteesar ta Rausayar da ido Tana Fadin"Bama mu taba fa kwana Daki Daya ba Tunda muka yi aure..! Munari ta Zare ido Tana Fadin"No Wonder shiyasa bai yi Laushi ba Har yanzu..ke kuma kika yarda..?baki cemai kina jin tsoro ba..! Imteesar tace"To ya zanyi..?dakinsa yake Shigewa fa sai na Bishi..!? Munari tace"Sosai ma.irinsu ya Imu sai da Tarko..Ki bisa ki Danamai Tarkon da zai kawo kansa da kansa yana Magiya..! Inteesar tace"Ta yaya hakan zai Faru..?kamar fa baya son abun ne ni ko irin Romance din nan bamu taba ba..! Tafada Abun na fitowa Daga Karkashin Ranta Munari tama kasa mgana Inteesar ta Cigaba da Fadin"Ina Fadamiki sirrina ne saboda Ke Kawatace kuma yar"uwata wacce banda kamarki..ki bani Shawaran ya Zanyi..? Munari tace"Insha Allahu Inteesar Zan baki Shawara kamar yadda Zan bama kaina..! Nan Munari ta Zauna Tana ta karanta mata Yadda Zatayi da Dubarin mata Inteesar tayi Kasake tana ji kafin tace"Kina ganin...kin fa san Ya Imu..! Munari tace"Ai shima Mutum ne kamar Kowa kuma Namiji mai Lafiya Wlh karyansa ya Ture Kiran wannan Majalisar Dinkin Duniyan in kuma ya Fara Dandanarta To zai so kullum ya Dinga Ninkaya aciii ina nan Zaune Zamu gani Ya Imu yayi Laushi sai yadda kikayi Dashi..! Inteesar tace"Allah yar"uwata..! Munari tace kina wasa ne Dariya sukayi lokaci daya suna Tafawa Inteesar na Fadin"Khalil ya Shiga uku..,! Munari na Fadib"Ai yama shiga Goma ne..!. Dariya suka saka gabadayansu sun dan jima acikin makaranta bayan sun gama Sallama da Course mate dinsu suka Tafi Office din Abba suka gaisheshi bayan sun gama shan A.c da Lemo suka Mai Sallama suka Tafi Daga Bakin Get suka Rabu kowacce ta hau adaidaitan da zai kaita inda zata suka Rabu Da Inteesar kan Zata gwada Shawarwarinta.
Chapter 168 · 0% Book details