Sashe 180
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dora yakini akansa Tir da Rayuwar Daya Zabama kansa Tundaga Ranar ya Tattara komai ya Watsar Tare da alkawarin Har Abada bazai kara ko Busa Sigari ba ballatana Har ya Daga wata kwalba ya Rufe babin mata da komai na Harkan Shanshanci Har Abada ya Fara Shirin Tahowa gida Domin ya Nemi Gafaran Daad ya yafemai Laifin Daya aikata. Aranar da Baffa Kabiru sukayi mgana da su Abba da asuba Khamis ya Sauka a Filin Jirgin Abuja Taxi ya samu zuwa Gida sai dai Baffa Kabiru da Umaima suka gansa Kwatsam Allah Sarki Rayuwa Khamis yayi kuka sosai Dayaga yadda ya tafi ya bar Baya da Kura Mami Ta Dade bata gida sun Rabu da Daad Sajida Tana makaranta Cikin Halin Ciwo shi kuma yana chan yana Shanshanci Kai consa,Abakin Umaima yake jin komai Domin Sanda ya iso Dad na cikin Dakinsa sai da ya Fito ya gansa.. Haka Khamis ya Duka ya Rike Kafafun Baffa Kabiru yana kuka yana Rokonsa Gafara Tare da alkawarin ya Daina Duka Abunda yake yi Har Abada bazai koma ga aikin Daya baro ba Me ya kamata Baffa Kabiru yayi banda ya Tallafi D"ansa da Allah ya Dubesa ya Karkatomai da Hankalinsa kan Hanya Madaidaiciya ya Rumgumesa yana Godiya ga Allah Hawaye na Ziraromai bai bari Khamis din ya gani ba yayi Saurin Dauke hawayen.. Nan da nan Baffa Kabiru ya Kira Daddy ya Fadamai ya Dakata da Tafiya Anambara ga Khamis ya Dawo gida da kansa jin haka yasa yayi Hamdala Daddy ya Kira Abba ya Fadamai Khamis ya Dawo gida Abba ma Nata Hamdala sun isa Barka. Aranar ma Baffa Kabiru bai Fita ba yana Tare da ya"yansa Khamis da Umaima Domin ya Dauki Daraman Gyaran Duk inda ya Kuskure Domin Dawo da walwalan ya"yansa sun yanke Shawaran gobe da safe dashi da Khamis zasu je makarantan su Sajida su Taho da ita sai dai Misalin karfe Daya na Dare Sai ga wayar Mami Asma"u ta Kira Baffa Kabiru karo na Farko Bayan Lalacewar abubuwan Daya ga Kiran bai Dauka ba Tunda Idonsa Biyu Har Lokacin bai yi barci ba Mugun Haushinta yake ji Gani yake Munfuncine ba Tuban Allah da Annabi bane gani tayi ba Sarki sai Allah ta kuma Rasa komai Shiyasa ta Dawo Tana Rabe Rabe Macijiya. Sai da yaga Kiran yaki ya kare kana ya Daga afusace ya auna mata ashariya ko Ta kyalesa sai da jinta Cikin kuka Tana Fadamai gasu a asibitin Specialist Hospital inda aka kawo Sajida bata da Lafiya Tana ta Tari da Jini Jin haka yasa Hankalin Baffa Kabiru ya kara tashi Cikin Tsananin Tashin Hankali ya Zura Jallabiya ya Fice Dakin Khamis ya shiga ya tasosa hankali Tashe yake Fadamai Halin da ake Ciki,Shima Hankalinsa ya Tashi Umaima ma Muryansu ya tasheta Daga Barcin Daya kwasheta itama jin Abunda ya Faru da yar"uwanta sai kuka Gabadayansu suka Dunguma suka Tafi. Koda suka je sun Iske Mami Asma"u da Hajiya Turai da Justice Tafida yarkace yarkace sai kuka Take TanaTuma kamar Mahaukaciya Idanuwanta sun Kole saboda kuka Ita jenefer ta Kira saboda itace Lambar Karshe da Sajidan Tayi mgana da ita suna Kwance adaki Sanda Tarin ya Sarke Sajidan da Zafi Har ta Fita Daga Hankalinta Jenefer ita taje ta Fadama Maman Hostel dinsu ita kuma ta Sanar da kuma Hukumar makaranta aka Kwaso su zuwa asibiti bayan an Shiga Da Sajida Emergency ne Ta samu Wayar Sajidan ta Kira Mamin Ta Fadamata wanda Kurruwanta ya Fito da Justice da Hajiya Turai jin Abunda ke Faruwa yasa suka Rankayo Gabadayansu Cikin Tashin Hankali. Ita uwa uwace ko ya ta Zama Haka Umaima da Khamis suka isa ga Mami Asma"u suka Dagota suka Rumgumeta suna Lallashinta Data kyalla ido Taga Khamis sai Rauninta ya bayyana ta Fada Jikinsa Tana Fadin"kaima ka Gujeni Khamis..Dad dinku ya sakeni Sajida Zata Mutu ta barmu Aman jini fa take..an shiga da ita Likotoci basu Fito ba Har yanzu na shiga ukuna na Lalace..! Haka take fada Cikin kuka tana Rike Jikin Khamis da shima yake jin kamar ya Fashe da kuka Idanuwansa sun yi Jajir kukan Mami kuka ne da zai Kassara Duk zuciyar mai Sauraranta Ammh banda ta Baffa Kabiru bayan gaisawa da Justice Tafida da Hajiya Turai bai kara mgana ba sai gaisuwan abokiyar Karatun Sajida Jenefer Daya amsa ko Barayin Mamin bai kallah ba Ballatana ta saka Ran wani Rahma Daga bangaransa. Gabadaya Hankula basa kwance Fin Mintina arba"in kafin Likitocin da suka Rufu kan Sajida su Fito basu tsaya amsa ma su Baffa Kabiru Tambayansu ba sukace jictice Tafida ya Biyosu Office shi da Baffa Kabiru Matan su Tsaya a waje. Baffa Kabiru ya Razana Dayaji bayanin Likita kan Abunda ke Damun Sajida ta Hadu da Heart problem Ciwon Zuciya Wanda har ta Fara Tabuwa saboda matsanancin Halin Datake Ciki Ta fara ganin jini in tana Tari bata zo asibiti ba har abun yayi yawa,Ammh dai yanzu ta Fita Daga Cikin Hatsarin Datake ciki sai dai Duk Abunda akasan Tana son gani ko Tana so a kawo matashi gabanta da Zarar ta Farfado in ba Haka ba zata samu Heart Attack arasa ta gabadaya. Baffa Kabiru Haka yake sharan kwallah Da Gaske Sajida take Tana son Imran Asma"u ta rabata dashi Gashi Soyayyarsa zai Zama ajalinta Shi kanshi Justice yaji Mganar sosai Jikinsa yayi sanyi shine ya iya Fita yayi ma su Khamis Bayanin da Likita yayi musu ai sai Wajen ya kara Rikicewa Mamin Har wani Suu Tayi Zata Fadi Hajiya Turai da Khamis suka Tarota kasa takai hannunta Saman kanta ta manta asibiti suke ta Kwarara Ihu Tana Fadin"Na shiga Uku..Na Shiga uku Ni Asma"u na lalace..! Baffa Kabiru da Ransa ya baci Tana Neman Tara musu jama"a Allah yasa ma Dare da sanin su manyan Mutane ai da ba haka ba wata Gigitattaciyar kara ya Daka mata Cikin Kaushin Murya ya fara fadin"Dillah kima Mutane Shuru..Kukan Uban me kuma Zaki mana..?kukan karya da munafunci..?ko na nadaman Dole..?duk abunda ya Faru da Sajida kece Sila...ke kika Rabata da abunda take so kika yi Sanadiyar Shigarta wannan Halin sannan kizo ki Damemu da kukanki na Banza Baki bani kin Lalace ba Asma"u Sai Y'ata ta Rasa Ranta ta Dalilinki na Rantse da wanda Raina ke Hannunsa sai nayi Shari"a dake sai kin Biyani Diyar kashemin yata da kikay Muguwa kawai azzalumuma mai Zuciyar Zalunci wacce batasan komai ba sai kanta.! Ya karishe Fada Cikin Sakarmata Jajayen Idanuwansa da suka Rine Saboda kuka Ba wanda iya mgana sanin ai gaskiya ya Fada Mami Asma"u jikinta na rawa da bakinta ta kasa mgana Jikin Khamis ta koma ta Lafe Umaima ta Kwantomata Tana kuka ai ita kukan natama ya Tsaya ta shiga wani yanayin da bawa bai isa ya Fassara ba. Hajiya Turai ne cikin Damuwa tace"Haba Kabiru don Allah ka Ragama yarinyar nan mana..Tafuskanci abubuwa da yawa ko baka Ragamata ba Saboda Zaman tare ba ai ka Ragamata saboda Daranjanmu iyayenta Dake Tsaye da su kansu Yayanku gasu nan da kuma Wacce ke kwance cikin nan Cikin Kokawaa da Numfashinta..! Ai in ma ya Bude baki yace wani abu Allah Zagin Hajiya Turai zai yi shiyasa yayi Shuru ya Dauke kansa yana ajiyar Zuciya Sai Wurin yayi Tsit sai Jan majinan Umaima ake ji Mamin kamar ai Wutarta ta Dauke justice kala bai ce Daman ba kuma zai ce ba Wanda bai ji bari ba bazai ji Hoho ba Dukkansu Zaman jiran Farfadowam Sajida suke Gabadayansu suna asibitin aka Kira sallar asuba kana Mazan suka tafi masallaci cikin Asibitin Harda matan sukayi Sallah Kowa Zuciyarsa ba Natsuwa Jenefer sai alokacin Tayi musu sallama ta koma Cikin makaranta su kuma tunda suka Dawo Sallah ba wanda ya Mtsa suna Fatan Sajida ta Farfado Cikin Hankalinta. Saboda Tashin Hankali yasa Baffa Kabiru ya mamta da Kiran kowa Sai da Sajida ta Farfado Daman Tana Emagency din har alokacin Likitoci sun Rufu kanta ammh ba sunan Datake Kira sai sunan Imran kuma Rashin Ganinsa Cikin Lokaci Mtsala ne haka Likita ke sanar dasu Baffa Kabiru Hankulansu ya kara tashi an basu Izimin Shiga su ganta Mami ce kan gaba Kamar Zata Kifa Tana Shiga Tafada jikin Sajida dake kwance Rai kwakwa Duk ta Rame tana mai Fashewa da kuka Tana Fadin"Ki yafemin Sajida..Dom Allah ki yafemin..! Sajida Tana kuka Tana Rike Saitin Zuciyarta Tana Fadin"Mami Ku kiramin Imran in ban gansa ba Mutuwa Zan yi..! Take Fada Tana kuka Gabadayansu Sun Zagayeta masu Saurin kuka irin su Hajiya Turai da Umaima suna ta Faman Sharbawa Justice Tafida ne ke Fadan Mami Ta Daga Sajida bata ga bata da Lafiya bane kuma ta Danneta Tana kuka Khamis kuwa Gefen Gadon ya Durkushe yana kokuwa da Numfashinsa. Baffa Kabiru waje ya Fita yana Dauke kwallarsa bazai iya Juran ganin Sajida ahaka ba ba ita ya kamata ta Fuskanci wannan ba Asma"u ita ya kamata ta karbi wannan Hukunci. Kai Tsaye Abba ya Kira da Daddy ya Sanar dasu abunda ke Faruwa Hankalinsu ya tashi Kwarai Tare da Tsausayin Dan"uwansu dukkansu sun Tabbatar mai gasunan zuwa yanzu zasu kamo Hanya. Daga su sai Imran Baffa Kabiru ya Kirasa Lokacin ya bar Gida zuwa Wajen aiki ne Jiya gidan Abba suka kusa Raba Dare Khalil ne jiya ya zo Daga Lagos wajen Munari mgana har Taje kunnensu Abba Tunda Dr.Ali argungun ya Kira Abba sun yi mgana,Wajensa ya Tsaya suna Hira da kuma Rigiman Inteesar na da sai ya barta ta Kwanan anan ya Tubure mata ya dawo Mata a Imran dinsa da baya Daukan Raini ballatana Wargi Dole ta biyosa suka Dawo Ko yau da Safe ya Fita ya barta Tana ta Fushi ya Fita Batunta daya dawo ya Fara Lallashinsa Zata mamta komai ta bada kai Bori ya hau. Lokacin da Baffa Kabiru ke Fadamai Halin da ake ciki jikinsa yayi Sanyi sai bai kara yin sanyi ba sai da yaji Baffa Kabiru na Rokonsa Allah da Annabi kan yazo yaga Sajida kafin ta bar Gidan Duniya yana mgana Daga jinsa kuka yakeyi Imran bai taba Jin Tsausayin Baffa Kabiru ba irin na Wannan Ranar ba har baisan Sanda ya Tabbatarmai da Insha Allahu yana Tafe yanzu da yardan Allah.. Jikinsa a sanyaye ya Tattara kayansa ya Biya Office din Manaja ya Fadamai Uxurin Rashin Lafiya ne yamai Izinin