← Book details Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 190

Sashe 131

Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Basu isa da wuri ba,Sai wajen 12pm na rana duk da sun fito da wuri,Sagir dai nashi dan bi ne domin baima san da Tafiyar ba,ana gobe Tafiyar ya kirasa a waya yace mai ya shirya gobe Zasu tafi Dukku ya zata ma amotarsa Zasu tafi Imran din yace A"a saboda bai wani san hanya ba Yusuf ne yasan Hanyar sosai,infact ma bai yi niyyar zuwa da Motar tasa ba. Sagir kallon Imran kawai yake Ko da bai gayamai komai irin Mirmishin Dayake ta saki na kasan Lebe yasan na mugunta ne irin Mirmishin Imran naci Nasara shifa Bai taba ganin mutum mai sa"a kamar Imran ba Komai ya sama gaba sai yaga bayansa komai yace zai yi to tabbas Zai yi ne yana da kyawawan Halayya da ba kowa ke sanin haka ba sai kana Tare dashi,Mashin dinsa Halak malak ya mallakamai Sagir din Saboda ai ya Chanchanta shi Sagir din ma yaki amsa Daga Farko Imran din ya wurgeshi da key din yace in bayaso to ya Bada ita yadai san In Imran ya Fadi mgana baya sauya mgana Mashin dai ta Zama nashi sai dai shi yayi abunda yaga Dama da ita. Koda suka isa Tuni bakin Abuja sun iso,Hatta Khamis ya iso,Daman jiya da Daddare ya sauka a Abuja da Safe suka kamo Hanya Harda Sajida Umaima Tana gida Saboda makaranta. Imran bai yi wata Shiga ba kamar yadda ya saba haka yayi sanye yake da Riga da wando,Rigar mai ruwan kasa ce Mai Hasken wandon kuma Shima mai ruwan kasa ne sai dai yana Duhu sosai,Wando daga kasa ya Tsuke kadan Ya kamasa. Sun shigo Har falon Daada inda su Umma ke Zaune ita da Mami Asma"u da su Sajida dasu Sa"id da Basheer,Su Abba suna Dakin Daada tun da suka Shigo Sajida idanuwanta suka Kafe akanshi shi Wlh bai ma ganta ba yaga dai Uwarta wacce ko kallo bata isheshi ba Umma kadai ya gaisar Kadahan kadahan,Sai ya karisa wajen su Ya Yusuf suka gaisawa ta Hanyar yin Musabaha,Abun mamaki Da kansa yau ya mikama Khamis hannu suka Gaisa suna kallon Juna ido Cikin ido. Imran kallon kayi kadan yake yi ma Imran irin na Riga na gama Dakai shi kuma Khamis Kallon Au ka Tuba ne..?Irin dai dole dai ka dawo Hanya yaro. Daganan Dakin Daada ya Shiga ya gaida su Abba,Da Daddy sai Inna Maimunatu,Yana kallon Goggo Bintalo da Baffa Kabiru yaki gaishesu da Abba yayi mgana sai yayi Shuru ciki Ciki ya gaishesu kamar bai ganesu ba,Abun yayi ma Inna Bintalo Ciwo sai dai bata mgantu ba Kada yaron ya Zageta tasan Tsab zai iya Tunda bai da kunya,Baffa Kabiru kam bai Damu ba Domin yasan Daman yaron baya Darajasa kuma bai Dauke sa a Uba ba. Dakin da suka sauka wanchan karon nan suka kara sauka shi da Sagir wanka Imu yayi ya sauya kaya saboda yana jin Zafi,yazo da karamar Laptop dinsa saboda aiki akwai aikin da Wani Ma"ikacin su zai turo mai Daga gyagyadi branch yau din so yana Bukatar ya Duba shiyasa yazo dashi Wayarsa ya Dauko domin yaji karan Shigowar sako Kamar yadda Ya zata Intee ce. Tana Tambayansa ko sun issa Lafiya ya Tura mata da cewa eh suna Dukku,Daga haka ya maida wayarsa aljihu,agogon Tsitsiyan hannunsa ya Duba yaga lokacin Sallah ya kusa Daman ya Dauro alwala cema Sagir yayi alwala su tafi masallaci ba Musu ya tashi yaje yayi alwala suka Fita Tare koda suka fita duka mazan suna Waje suna alwala har da su Abba ya Hadu da Mami Asma"u a Falo bai ko kalli barayinta ba,Dariya yake cikin Ransa Domin har yana Hango irin yadda Zatayi in taji Hukunci da ya yanke akanta da ita da yarta. Gabadayansu suka Dumguma zuwa masallaci sai da suka Tsaya aka Tada sallar tunda sunje da wuri bayan sun idar suka nufo gida. Imran da shi da Sagir suna Baya sai Daga baya suka Shigo gidan Tun Daga Nesa ya Hango Sajida Tana Tsaye ko da bai sani ba yana da Tabbaci shi take jira zatayi mgana dashi Sanye take da wani material mai Santsi Dingin Doguwar riga ta yane kanta da karamin Bakim Vail kafarta Cikin takalmi baki sawu ciki a Fuskarta ta Rame sosai Idanuwanta duk sun Sauya Launi Sagir na ganinta ya Zunguri Imran yana Fadin"Ga Amaryan ka nan..! Ko kallonsa Imran bai yi ba sai ma kara Tamke Fuska da yayi kamar bai Taba Dariya ba Har suka kariso kusa da ita Sagir na Shirin Dakatawa Imran ya wuce Kamar ma bai ganta ba ganin haka yasa Sajidan da gabanta ke Fadi Saboda yadda Imran din yayi mata Kwarjini tace"ina yini..! Imran yajita ammh yayi kamar bai jita ba ya cigaba da Tafiyarsa Sagir Daya ga haka ya Daga Murya yana Fadin"Imu tana gaisheka fa..Don Allah ka Tssya..! Da kamar bazai Tsaya sai Wata Zuciyar tace ka Tsaya ai ba wani Sauran Rina Dake Tsakaninku. Cak ya Tsaya Lokaci Daya yana juyowa Hannuwansa ya Haarde Saman Kirjinsa yana kallon Sagir irin gashi na Tsaya sai yaya..? Sagir ne ganin haka yasa ya Kalli Sajida da kanta ke kasa jikinta ma ya fara rawa tana ta wasa da Kwalliyar Jikin Rigarta. Ya sanyaya Murya yarinyar ta bashi Tsausayi saboda yasan wacce Zata iya gaba da gaba da Imu ba karamar Jaruma bace Yace"Ki je ki sameshi in ba haka ba zai Tafi abunsa..! Daga haka ya wuceta da sauri kusa da Imran ya karisa daidai kunnensa yayi mai Rada"Plz ka saki Ranka She is ur Wife..! Sanda Sagir ya fadi haka sai yaji kamar ya Mangaresa da mari,sai kuma yayi Fuska kawai ya kara Hade rai ko kadan ba annuri ballatana Samun sukuni agame dashi Sagir dai Ciki ya shige yana Fatan kada Allah yasa Imran ya zabgama yarinyar nan Rashin Mutumcinsa. Gajiya yayi da tsayuwa ganin Ta na nan Tsaye bata ma tako ba,juyawa yayi niyyar tafiya sai gata ta kariso Salau Salau kamar mara kuzari aransa yace ji ta kamar wata ta Allah. Kanta na kasa bata son Hada ido dashi Tace"Ina yini..! Tafada Lokaci Daya gabanta na Faduwa,Saboda bata son kallonsa kwayan idonsa yana bata tsoro matuka yana saka taji duk wani Comfident dinta ya tafi indai tana gabansa gabanta sai Fadi yake in da Zai lura har rawan jiki dana Baki take yi alokaci Daya. Kallonta yake Daga sama Har kasa so yayi ya sakin mata Tsaki sai kuma ya fasa cikin Dauke kai da Dakuna Fuska yace"Lafiya..! Yafada yana kallon Fuskarta acikin Ransa yace irin Fuskar uwarta ya"yan nagada ba na haya ba. Gajiya yayi da tsayuwa yasa yace"Ammh kinsan dai ba wasa tsakanina Dake da zaki Tsaidani ki tasani agaba kuma kiki mgana ko..? Yafada cikin Kaushinsa kamar ko yaushe. Jim haka yasa ta kara Sadda kanta Tana Fadin"Dama..Dama! Wani Haushi ya kamashi yace"Dama What..?ke kinga ni ina da abunyi yanzuma Da kika ga na Tsaya Wlh ba wai domin darajanki bane ke har kin Isa..? Ba macen data isa ta sani ni Imran nayi abunda ban yi niyya ba Darajan Abokina kikaci..So in baki da Fada on my..! Bata bari ya karisa ba,Tunda taji mganarsa Cikin Kaushinsa kafin tace"Dama ina ta Kiranka a waya ne baka Dauka ba Daga baya kuma sai na Daina Samun ka..! Karamin Tsaki yaja kai Tsaye yace"Nayi Blooking dinki ne..! Batasan Sadda ta Dago rinannun Idanuwanta Tana kallonsa ba Cikin mamakin kalamansa Duk da tasan dai Ya kulleta ne ammh bata Zata zai iya gayamata haka ido Cikin ido ba. Ganin irin kallon Datake yimai ne yasa ya Daga mata gira guda Daya yana Fadin"Yes..Saboda bana son Wata mu"amala ta shiga Tsakanina Dake Infact ma bamu da wata alaqa..! Bai bata Zarafin mgana ba ya cigaba da Fadin"Nasan zuciyarki na Fada miki ba an Daura mana aure ba..? Auran Dan iska dan Shaye shaye bai Dace da Sajida Kabir Dukku ba Diyar Lauyoyi jikar Lauyoyi Diyar na gada ba na Haya ba..To u better wake up..kinga kuwa ni ban Dace dake ba..Ke ba Matata bace bamu da wata akala! Gabadaya kalamansa sun rikitata Bata san Sadda ta dago kanta Tana kallonsa ba sanda yace ita ba Matarsa bace Kara Dakuna Fuska yayi kafin yace"Eh nace bamu da akala ko muna Dashi ne? Nasan zaki ce to ko ba aure ai ni yar"uwarka ce u ara mad in kikayi Tunanin haka akaina ni Imran Wlh wanda keyi dani sai ma naga Dama Zanyi Dashi acikin Dangi ballatana Wanda basan da wanzuwarsu ba So plz and plz ki Rabu dani kada ki kara Kirana am not ur mate kada ki kara Kirana In baka ba Haka zaki san Oder Side dina! Tsaki yaja mai karfi yana Fadin"Rubbiish kawai..! Daga haka ya juya ya shige cikin Gida,da kallo ta Bisa Hawayen da suka cika mata ido suka zubo mata masu Zafi da Tsananin kaunar Imran Kuka Take so ta fashe dashi ammh Zuciyarta ta Chuse waje Daya Meyasa yace ita ba Matarsa bace ko ya saketa ne? Saurin dafe kanta Tayi jin ya sara mata da wannan Karamin Tunanin a Fili ta Furta"A"a bazai taba sakina ba..Bazai sakeni ba bazai sabama mganar Baffa data Daada ba..Wlh ina sonsa inajin kamar in na Rasashi Zam iya Mutuwa..! Take Fada tana Sharan Hawayenta kamar Wata Tattabiya soyyaya Ta sakata Zatayi hauka kafin ta Dibi Sauri Zuwa Cikin Gida. Tana shiga Taga ana ta cin Abinci Mami Asma"u dake Faman nemanta ta Tsareta da ido Cikin Tuhuma Tana fadin"Ina kika shiga Tun dazu..!? Cikin kame kame tace"Na fita amsa waya ne Mami..! Tafada Tana kallon Imran Dake kusa da Yusuf suna cin Alalan da Baba asabe Tayi a Filet Daya,Ko barayin Datake bai kallah ba kansa na kasa ya bada natsuwasan kan abun ke gabansa. Hararanta Mami Asma"u tayi Tana Fadin"Waya ko..? Ita kuma wannan ta waye..? Tafada Tana Daga mata wayarta da ta barta gefen Mami Asma"u din bata sani ba. Kanta ta Sadda kasa batace komai ba Hankalin kowa baya kansu Ba wanda ma yabi ta kansu su Abba suna Dakin Daada achan suke cin nasu abincin. Mami Asma"u kure Sajida da ido take yi,Tana Nazarin wani abu acikin Ranta Taga shigowar Imran kuma ba Dadewa Taga Sajida ta shigo Allah yasa ba ajinta ta Zubar taje tayi mai mgana ba in ko hakane
Chapter 131 · 0% Book details