Sashe 106
Gidanmu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Hajiya Mero ce da Alhaji Ahasaan da Tasleem zaune kan Dining din Dake Falon gidan,Suna Breakfast kowa na cin Abincinsa bakajin karar komai sai Cokali da bugawar Filet da Kofuna.
Hajiya Mero bata wani ci da yawa ba ta Share bakinta da Tissue tana kallon Tasleem tace"Tasleem tashi ki Daukomin wayata acikin Bedroom dina..!
Alhaji Alhassan dake Zaune yana Tura Dankali soyayye Cikin bakinsa,Cikin muryan Abu na Cikin bakin mutum yace"Haba Mero kina gani fa Breakfast take yi ai kya bari ta gama ko kuma ke tunda kin gama ki tashi ki Dauko Da kanki..!
Wani kallo tamai batace komai ba Tasleem ta mike tana fadin"Bakomai Abbu bari na Dauko mata..!
Shima bai yi mgana ba ya cigaba da Tusa dankalinsa yana Hadawa da Kurban Ruwan tea a wani karamin mug mai kyau da yarari.
Ba jimawa sai ga Tasleem ta Dawo da Wayar Hajiya Mero a hannunta sai da ta Zauna ta mikamata Tana fadin"Gashi Mommy..!
Karba Tayi tana Yar dariya da sai da suka Kalleta gabadayansu Lambar Safiya ta Lalubo ta doka mata Kira ta saka Wayar a Speaker ta ijiyeta nan kusa da Hajiya Alhassan saman Tebir din.
Kira Daya biyu uku Safiya Daga Chan bangaran da suke Kitchen suna aikin Abincin da su Abba sukace ayi mai yawa Saboda bayan Salar azahar in in aka gama Daura auran za"a Fito da Abincin arabama Mutane.
Gefe ta koma kafin ta Dauki Wayar Tunda gabadayansu suke Kitchen din Har da Inna Maimunatu dasu Zainab dasu Aneesa da su Munari Inteesar na Cikin Daki bata Fito ba tace kanta na Sara mata.
Sallama ta Ragada kafin tace"Mommy ina kwana..!
Momny ta amsa Tana Fadin"Lafiya lau Daugher ya kuke..? Ya Dukkun..?
Tafada tana kallon Alhaji Alhassan Daya ijiye cin abinsa yana Sauraransu Da mamakin jin ta ambaci Dukku.
Safiya Dagachan bangaran tace"Lafiya lau Mommy gamu cikin sha"anin biki kin ji Hayaniya ko..?
Mommy tace"Eh fa bikin waye..?
Safiya tace"Mommy Imran za"a Daura ma aure yau da yar"uwansa Diyar wanda Abba kebi Baffa Kabiru Barrister Dake Zaune A Abuja..,!
Mommy ta Rike baki tana Fadin"Ikon Allah kice Tuwon a maina Za"ayi..Ammh abu cikin gaggawa haka..?
Safiya tace"Daurin auran kadai za"ayi Mommy Tarewa inaga sai daga Baya..Daada ta hada abun saboda kara Hada kansu Waje Daya..Mommy kinga Danginsu gabadayansu kowa yazo da ya"yansu gidansu Babban Gida ne Mommy a Dukku su din Dangin Manyan Mutane ne Duk garin Dukku ba wanda baisan Iyalan Gidan Marigayi Alkali Hamisu Dukku ba..!
Mommy Dake sakin Dariya Tana kallon Alhaji Alhassan ta gfen ido kafin tace"Masha Allah..Naji Dadi sosai Safiya..Allah bai barin Zalunci Daman Nagodema Allah yadda wani yaso ki tozarta Allah bai bari haka ya Faru ba gaki yanzu cikin Ahalin mijinki Cikin nasaba da Karamcin da Tushe da asali in arzikin ne suma sun Taka Allah ma godemaka da kika Tsallaken Siradin Tozarci sai dai Mutum ya Tozarta..!
Ta Karishe Fada da karfi kuma da gayyah ba Alhaji Alhassan ba Hatta Tasleem da Safiya susan da wanda suke.
Safiya tace"Plz Mommy..!
Tafada Cikin shagwaba Hajiya Mero Tace"Ki gaidamin da Yusuf sai kun dawo zamu zo da Saratu da Tasleem Insha Allahu..!
Safiya tace"Tom Mommy ki gaida Abu da Tasleem sai na Kiraki..!
Daga haka ta katse kiran Mommy ta Mike Dauke da wayar tana yar waka Lokaci Daya tana Fadin"Allah ba azzalumin bawa bane..Allah kana gani..!
Haka take fada Cikin Salon waka ta wuce zuwa Falon tana Hararan Alhaji Alhassan Ta gefen ido samin baida gaskiya ko Dagowa ma bai yi ba kansa na kasa gabadaya Jikinsa ya gamayin Sanyi Tsoro ya Shigesa yana Tsoron kada Hakkin Safiya ya kamasa a sirinsa ya Tonu,Domin bai fa Daina Dabi"arsa ba sai dai kalaman Hajiya Mero sun bashi Tsoro,Ashe yaron nan Yusuf dan asali ne,Lalle ne kada ka shiga Hurumin Ubangiji gabadaya ya kasa Tashi ma Har Tasleem ta gama tabi bayan Hajiya Mero zuwa Falo kunya ya hanasa wani Motsi.
****
Imran cika kawai yake yana batsewa kamar yayi Bindiga sai kunkuni yake Fuskar nan ba Fara"a ya Hade ran nan kamar bai taba Dariya ba.
Zaune yake gefen gadon dakin da suka sauka,Sagir da Yusuf na Tsaye kansa,Wasu Fararan kayane Riga da wando na Wata Shadda mai kyau da yarari,kayan Yusuf ne Abba yace ya bama Imran ya saka saboda Daurin aure,Da farko so yayi ma ya Gudu ya bar anguwa sai Abba ya Ritsashi yace mai in yasake ya Fita sai ya sabamai baida yarda zai yi Dole ya koma yayi lakwas,Sha biyu ta wuce sun fara Haraman Daurin auran tunda Har sun Daddy ya baama su Basheer kudi sun siyo goro da Minti Umarnin Daada ne Gida kuma ana ta Girki Kayattace,Mami Asma"u na Cikin Daki ta kasa Zama sai kiran Baffa Kabiru take tana so su kebe bai bata Dama ba Saboda baisan me zai ce mata bai isa yabi mgnarta ba yabar Umarnin Daada ba
Shiyasa yaki yarda su Hadu hankalinta ya shi sosai,Khamis ma ta kirasa tana Fadamai yaje ya gayama Baffa Kabiru kada ya yarda a Daura wannan auran bata amince ba Da ya fita bai Dawo ba bayason Mami Tana irin wannan sai abu yazo ya Lalace Daga baya.
Sajida kuwa Daada ta saka Inna Maimunatu da Da Inna Bintalo suka Daukota nan Dakinta Mami Asma"u tana ji tana gani bata da tacewa,Ta Kira Chan gidansu ta Fadama Tsohon Alkalin Alkalai Justice Tafida tana kuka bai biye mata ba yace Baffa Kabiru nada Hurumi da iko kan yarsa ganin ba Sa"a yasa ta Kira Hajiyarsu Hajiya Turai itacre ta Dauki ZAfi ta Kira Baffa Kabiru,bayan sun yi mgana ya nuna mata Umarnin Daada ne shi kuma bai isa ya kauce ma Umarninta ba Dole tayi Shuru ta kira Mami tana bata Hakuri Mami Asma"u ta Cika kamar ta Fashe ga ya"yanta basa Goyon bayanta Umaima ta shige cikin Danginta Ita da khamis suna ta Shirin Daurin auran